27

277 10 1
                                    

💫 SANYI DA ZAFI 💫

         ✍🏻M SHAKUR

EPISODE 2️⃣7️⃣
Dawani irin full confidence Bilal yazo wajen ta yau but ganin wani lafiyayyen guy me kirarran jiki tareda ita and from the way he's doing kaman saurayinta ne yasa yaji zuciyanshi na kumfa, daman Rashy nada saurayi ne? Who is he? Waye atare da ita? Waye dan wulakancin nan? Well yasan koma waye da wuya idan yakaishi kudi he will wait she will come begging for the money yana gama tunanin yajuya azuciye yayi motanshi ya shiga yabar hospital din.
Tare suka shigo ward din daidai lokacin shima Baba Liman na zuwa da ladanin masallaci su biyu, gaisawa suka tsaya yi da Riyad ita kuma Rashida ta wuce, shiga cikin ICU Nurse din da Mrs Bugaje ta turo tayi akasa Mama akan wani wheelchair aka gungurota har zuwa office din Mrs Bugaje Rashida na biyeda ita saikuma su Riyad da Baba liman da Ladanin is duk suka shiga ciki.

Already Mrs Bugaje tasa an saka kujeru duk aka zazzauna gawasu sababbin syringe agabanta guda biyu, anatse tace "welcome to my office" sannan tace "before muyi proceeding muyi asalin abinda yakawomu nan office din, as a medical Doctor i want do something for both Riyad and Rashida" ta taso dagakan kujeranta da kanta tazo gaban desk ta kalli Riyad ahankali tace "bani hannunka" bata hannunshi yayi ta kulle igiyan tajajininsa tasa a specimen box tarubuta suna sannan tama Rashida ma haka, sannan tabama wani Nurse dake wajen data kira musamman tace "Abbakar take it to the Lab I need Asap results on this two sample kan genotype blood group HIV, hepatitis da sauransu important blood test na aure" gyadamata kai yayi yace "Yes Ma" yawuce yafita takoma tazauna takalli Riyad tace "inaso kasan wakake aure ba kokanto ba zargi a zuciyanka ko na yan uwanka dake nan wajen" Baba Liman yace "kwarai" Rashida dai na wajen Mama kanta akasa takasa kallon kowa na dakin, almost 20min akayi aka kawo result din Mrs Bugaje ta karba tarike na Riyad a hannunta tamikama Riyad na Rashida tace "take open it" karba yayi ya warware takardan ahankali, Mrs Bugaje tace "read it kowa yaji" dan shiru Riyad yayi chan yace  "genotyp AA, blood group O+, HIV negative, HEP B Negative, HEP C Negative komima negative" yayi maganan ahankali,  Mrs Bugaje ta bude na Riyad tana saka glass na idanunta like a professional tace "Genoyype na Riyad is AS Rashida is AA so you guys are compactable zaku iya aure, Blood group O+ shima, HIV, HepB and HepC da sauran komi negative, Masha Allah" tai maganan tana bama Baba Liman wanda kaman shine zai tsayama Rashida as uba, sannan tace "Alhamdulillah nayi part dina sai daura aure yanzu" faduwa gaban Rashida ya shigayi sosai, cikeda hikima na manya Buba yace "Alhamdulillah Masha Allah, muna addu'a muna kuma rokon Allah daya bawa mahaifiyarki lafiya Rashida Ameen Ameen, Mahaifin jikana ya rasu nine zan tsaya mishi a matsayin uba, sannan sunna ne atambayi yarinya nawa takeso amatsayin sadakinta, dan haka Riyad tambayi your wife to be nawa takeso a matsayin sadaki".   Dan murmushi Mama dake cikin ciwo tayi ahankali Riyad yakalli Rashida da kanta ke kasa ki fuskanta baka iya gani da kyau sabida yanda kan nata ke kasa cikin murya mai taushi yace "nawa kikeso na biyaki sadaki?" Kasa magana tayi kai ko motsi bata iyayi itama Mama batace komiba, Mrs Bugaje tai murmushi itama tai shiru, Baba Liman yace "tunda nine zan tsaya amatsayin waliyin Amarya bari na ari bakinsu" yakalli Rashida yana murmushi yace "yarmu me kyau ce! Ga ilimi boko da islamiyya ga hazaka gakuma son iyaye dan haka bazanmuma Riyad karamin kudi ba ko Zainabu"? Duk ciwon Mama saida tai murmushi sosai hakan ba karamin dadi yama kowa na dakin ba, Baba Liman yasake murmushi yace "dubu dari biyu mukeso akudin sadaki" harga Allah yafadi haka sabida yasan basuda kudi kuma dole amata Kayan daki dazaran Mama taji sauki an sallameta saisa yasa kudi haka, hannu Buba yasa acikin babban rigan dake jikinsa yaciro wrapper na 1k guda biyu yasa akan jikin Riyad yace "tashi kaje kabata sadakinta" kallon Buba yayi cikeda so sannan yatashi ahankali har zuwa inda Rashida ke zaune yamika mata kudin cikin wani kalan murya mai taushi yace "ga sadakin ki" hannu dasauri takai ta kulle fuskanta tana rike kukan datakeji gawani irin kunya Mrs Bugaje tace "ayiriri Amarya na kunya ijiye akan cinyanta" ijiyewa Riyad yayi yajuya yakoma ya zauna sannan aka fara daura aure agaban Buba da Aminin sa, Liman da Ladani, Munir da Riyad, Dr Bugaje da Dr Usama, Mama dakuma Rashida, agaban su aka daura aure tsakanin Riyad Baba Ali da Rashida Almustapha akan sadaki naira dubu dari biyu!.

Mama na ganin an shafe Fatihan daura aure sai kawai tajawo Rashida ta rungumeta tana wani irin emotional kuka bata taba sanin Allah zai nuna mata auren yarta Rashida haka ba, itama Rashida kuka take she can't believe ita aka daurama aure just now, wai yanzu tazama matar Riyad? Dreaming takeyi ne, tasowa Buba yayi yazo wajen su yace "kidena kuka shi ciwo na Allah ne, hakama waraka ta Allah ce, komi yayi zafi maganinsa Allah, Allah zai baki lpy kinji" gyadamai kai tayi ahankali Mama tana sakin Rashida tace "Riyad" zuwa wajen yayi yadan saci kallon yanda Rashida ke sharce hawaye Mama tace "nagode Riyad!" lumshe idanu yayi, Buba ya juyo ya kalli Rashida dake kuka sosai sai kawai yaduka agabanta hannunshi yakai yakama kuncinta hakan yasa Rashida takalleshi da jajayen idanunta, cikeda wani irin tausayin yarinyar da kaunarta dayaji Allah yasamai hakanan yace "dena kuka Allah zai bawa Mahaifiyarki lafiya kinji" gyadamai kai tayi ahankali cikeda kunya ganin tsoho dashi ya duka agabanta,  murmushi yayi mata yasa yadauki byro daya gani akan table na Dr Bugaje yace "dan tsammini takarda Docta" paper Dr Bugaje tabashi rubuta number shi yayi yabama Rashida yace "duk randa Riyad yamiki wani laifi, koya bata miki rai, call me zanzo har gidanku na sabamishi, saina ciwa mijin naki mutunci" akunyace ta sunnar dakai Mama tai murmushi sosai Buba yace "karba" ahankali Rashida tasa hannu ta amsa sannan yatashi yakalli Munir yace "muje ka maidamu gida" dasauri Riyad yace "zan maidaku Buba" kallonshi Buba yayi yace "stay da iyalanka kabar Munir ya kaini" wani iri Rashida taji jin ance iyalanka shikuma Riyad saiya gyadamai kai suka wuce suka fita nurses sukazo suka wuce da Mama aka fita da ita, ganin Riyad har lokacin tsaye a office din itakuma Rashida takasa mikewa sai hawaye take gogewa yasa Dr Bugaje ta tashi itama tace "bari na bisu" gyadamata kai yayi tawuce tafice ganin haka yasa itama Rashida ta tashi da sauri tazo zata fice kawai taji yakama hannunta, mugun faduwa gabanta yayi da saida ya lura dasauri ta kalleshi hada idanu sukayi yamata wani irin kallo kaman baimasan yarike hannunta ba gently yace "who is that guy"? Yanda yamata maganan yana kallon kwayan idanunta dasuke ajike yasa takasa jure kallonshi takasa magana, dan jawota yayi sabida yanda take so light this days kawai ta taho dab dashi gabanta nafaduwa sosai mehaka yake mata, cikin whispering voice yace "me tsakaninku"? Heart dinta na racing sosai tace "bakomi classmate dina ne" "mesa yakawo miki kudi?" Dan kallonshi tayi yanda yau yake kallonta saitaga kaman ya banbanta da yanda yasaba kallonta ada, sake sauke kanta kasa tayi tace "nayi seeking help a group namu for Mama" hannunshi dake free ya mikamata yace "your phone" dan kallonshi tayi saikuma ba musu tasamai wayanta a hannunshi ya karba a aljihu taga yasaka wayan nata ahankali yace "the next time he approaches you tell him someone owns you now! And that person is Me!" dago kanta Rashida tayi da sauri ta kalleshi yanda yake maganan kaman yaci wani competition saikuma ta gyadamai kai yace "zanje and get you food and clothes you need to shower and change" sake gyadamai kai tayi takosa yasaki hannunta dataji yana mata kaman shock, ahankali yasaki hannun yace "let's go" tare suka fito har zuwa ICU Mama da Mrs Bugaje dake tare duk suka kallesu murmushi Mama tayi Dr Bugaje tace "congratulations Mama, Allah ya sanya albarka, Mama yanzu saiki kwantar da hankalinki ayanda nake ganin yaron nan Riyad he will protect Rashida no matter what so dan Allah kiji sauki BP ki ya sauko" gyadamata kai Mama tayi tanajin wani karfi da lafiya na shiganta.

SANYI DA ZAFIWhere stories live. Discover now