8

438 15 0
                                    

💫 SANYI DA ZAFI 💫

          ✍🏻M SHAKUR

EPISODE 8️⃣

BAYAN 1YR!!

Cikeda natsuwa wasu manya manyan fadawa ke bude wani hamshakin kofa da girmanshi zaiyi girman wani karamin gate daidai karfe sha daya na safe, sannan dukansu suka fadi suka zube suna daga hannu irin yanda dai fadawa ke gaisuwa suka fara zuba kirari.
"Lafiya jakadan Baba Ali dan Baba Ali! Lafiya mai kiran gabas da yamma! Lafiya jinjirin wata sha kallo! Lafiya kwankwason jimina mai wuyar shafawa! Lafiya Garkami Wandon Karfe! Lafiya jijigen addini! Lafiya toya matsafa! Lafiya baya goya Marayu! Lafiya toron giwa! Lafiya tufaniyar gabas! Lafiya jinjirin wata shakallo! Taaaakawanka lafiya sarkin mu sarkin Riyad zakaran gwajin dafi mai hasken zuciya da hasken aura!, lafiya dan lellen Mai Babban daki....."
Tunda suka fara kirarin nan kusan good 10min sai yanzu wani dogon mutum yafito yana sanye da wata milk kokuwar alkyabba dahar walkiya takeyi tsabagen kyanta ga rawani dawani white yadi mai kyau dake walkiya akamai, inda farare tarrr na idanunshi kake iya gani, hannunshi yarike wata sanda mai kyau, rabon da mutanen gari da yan fada suga fuskanshi shekara daya kenan, tun kafin yakaraso inda suke turarenshi yagama gauraye wajen da kamshin dadi dake dauke da yalwataccen ni'ima, ahankali yake tafiya kaman baiso yataka kasa, wani irin kwarjini shiganshi ke dauke dashi da bamaka iya kallonsa, har ya iso inda suke ya tsaya chak na kaman 5secs ya kallesu one by one to check idan kowa is healthy fine and present wanda hakan yana daga cikin abinda yasa jama'a ke sonshi, kaman baiso ya furta magana yace "kun tashi lpy"? Kaman jira suke. "Lapiyanmu kalau Sarkin mu mai adalaci, sannu sannu toron giwa tsintsiya madaurinki daya!" yanda jikinsu har rawa rawa yake sunamai kirari suna yabashi ya kalla sannan kawai yawuce duk suka biyoshi abaya, direct fada suka shige inda mutane suke cike makil wajen zama yayi ya zauna, batare daya hada ido da kowa ba this is mostly method dayayi adopting dayake samai natsuwa cus dazaran ya shigo fada he sees love hatred envy a idanun mutane da dama barinma yayanshi Kabeer, but koda wasa baitaba disrespecting yan uwanshi ba, and so far so good Kabeer din has been supportive bai bashi wani matsala ba haka ma yayyin babbanshi da Waziri ana koyamai komi everything is going smooth Alhamdulillah.

Munir sai kallonshi yake bayan yazauna, yadade baiga sarkin da mabiya keso kaman Riyad ba, anason Baban su but son da akema Riyad daban ne, har lakabi akamai da Sarki me farin jini, dudda akwai yan adawa but wlh ana sonshi barin yan cikin gari, cus kafin ma yazama sarki yana taimako sosai yasaka yara a school da dama, yanzu kawai dan he's not happy about zama sarkin sai the whole abu yasa he hardly talks, yakara miskilanci da wulakanci fiye da da, he's so angry sabida he's feeling kawai responsibility akasamai akai da baya so, responsibility daya tsaya and funny enough he's doing so good da leadership din saisa har yanzu an kasa fadin wani negative abu akanshi ko kokafadi babu wanda zai yarda ma though yasan alot of people na jiransa to just make a mistake ne and he pray dan uwanshi will not make that mistake dasukeso suke kuma jira yayi.

Almost 2hr yayi afadan sannan aka tashi yakoma side nashi, bayan an bude katon kofan nan kaman gate still akwai tafiya kafin asalin babban gininshi, baya mulki like others, he hardly let anyone a side nashi, daga Muneer sai Mom da Haleema.

Shida Muneer suka jera fadawa na binsu abaya ana kaiwa gate din kowa ya tsaya dan babu bafaden dake shiga ciki ko matarshi bata isa tashigo side dinba without izininshi, sake bude another door sukayi that will lead them to compound din da interlock ya cika ko'ina ga bishiyan mango dake wajen da flowers ko'ina sai wata arniyan jeep bulletproof dake compound din gawani secret gate dayake wajen any private outing tanan yake fita.
Shiga mainflat din sukayi WAN'ı irin crazy sitting room ne dakeda fadi na bala'in yasha funitures that are very beautiful, zama Muneer yayi yadauki laptop dake kan table yace "almost 2yrs bake leka hotel ba Riyad, its only right kaje mana" wucewa sama yayi dan yaje ya cire kayan nan dasuka isheshi.

Binshi da kallo kawai yayi kafin ya shiga replying mails, kai tsaye aka shigo falon dasauri Muneer yadago kanshi dan mamakin waye ya isa yayi hakan ganin Mom tana sanye da wani alkyabba da akayi da crystal yasa yadan taso yace "ina yini Mo...." Baima karasa gaidataba tawuce stairs tai sama fuuu.

Riyad yariga yasaka wandon wani yadi brown da farin singlet ajikinshi yana kokarin saka rigan aka bude kofan bedroom nashi, dago kanshi yayi suka hada ido da Mom data haderai kana ganinta kasan ranta abace, dan lumshe idanu yayi yakarasa saka rigan Mom takaraso ciki har zuwa gabanshi dab dashi ta tsaya cikin tsananin bacinrai tace "yau kwanan ka nawa rabonka da shiga turakan Haleema Riyad"? Hannu yamika ya dauki agogo daga saman bed yana kokarin sawa yace "Mom kinsan I've been busy dealing with lot of things, my business, this sarki thing, everything ma" "and so?" Mom tai maganan da fushi tana daga murya tace "sabida business da sauransu bazaka kula matanka ba kusan 1months da 1week baka shiga gidan ta ba, and baka bari ta shigo nan ba, sai gulma ake tell me menene banbancinka da su Muneer da basu da mata"? Dan yatsine fuska yayi still baice komiba yadauki links na hannun riganshi yana kokarin sawa Mom ta fizge links din cikeda masifa tace "Riyad wlh zan mugun sabamaka I hate this new attitude din naka, I'm talking to you baka kulani, ka shiga turakan Haleema koka kirata tazo nan your choice, people are watching and you know that, 1yr kenan kunyi aure ba ciki and it's all thanks to you, ni bantaba ganin mai gudun mace har mace ba sai kai, badadan na tambaya tacemin kalau kake functioning ba dana fara tunanin kokai mace ce" sauke kanshi yayi kasa yayi shiru why will Mom be asking Haleema irin this kinds of question? Ahankali kanshi na kasa yace "kiyakuri Mom" cikin fushi tace "nayakuri nayakuri me? Get your wife pregnant nagayamaka dagayau nakaraji kun raba kwana" ta ijiye links din akan gado tajuya zata wuce hartakai wajen kofa zata fita ahankali yace "Mom" juyowa tayi tamai wani mugun kallo saikuma ahankali ta tako zuwa gabanshi ta tsaya tana kallon kwayan idanunshi, ahankali takai yatsanta tadaura kan kirjinshi cikin kakkausan murya tace "ni mahaifiyarka na umarceka dakai tarayya da matarka, make her pregnant within period na this sabon month da aka shiga, inba hakaba wlh saika gamu da fushina sosai Riyad" tajuya fuuuu tafice yadade tsaye ahaka idanunshi sunyi jaaa mode nashi ya chanza, he hates yanda Haleema tells Mom literally everything about marriage nasu, koma yace he hates yanda Mom ask everything akan aurensu, he hates both kawai, yana bala'in son sirri, he loves everything about shida matarshi nazama about them, anytime yakalli Haleema he doesn't even feel like shine mijinta, he feel like Mom ne mijinta, kokarin saita muryanshi yayi yadauki wayanshi dake kan gadon, Munir yakira cikin muryanshi da bata fita sosai tsabagen bacin rai yace "ka aika akiramin Haleema pls" yana maganan ya katse wayan, tashi Munir kawai yayi yafice bayan yabada sakon yashiga mota yabar gidan cus yaji komi da Mom tafadi he just pity his brother, Mom is just over controlling Riyad, she's in his matter, and baya iya cemata no, itakuma Haleema akanme zata dinga gayama Mamanshi komi gameda aurensu? Sabida taga baya iya tsallake maganan Mom ne, haba it's annoying mana, Riyad dakeda kunya tagama fallasashi, it doesn't matter koda Mamanshi ne some private mata barinma harkan auratayyan su baikamata Mom tama sani ba, the girl is sick wlh batasan menene boye sirrin mijinta ba, dashine matarshi tamai haka Allah he will deal with her, yayi tsaki aranshi.
Office yawuce abinshi inyaso yasameshi daga baya.

SANYI DA ZAFIWhere stories live. Discover now