12

365 13 0
                                    

💫 SANYI DA ZAFI 💫

       ✍🏻M SHAKUR

EPISODE 1️⃣2️⃣
Bucket na moping din tadauka da gudu tawuce bathroom na office din  ta tara wani ruwa ta taho da sauri jikinta duk rawa yake zata fara mopping ruwan kunfan kasan jikinta duk yana tsiyaya kaman daga sama taji sassanyar muryanshi yace "stop!" Dasauri tadago manyan fararen idanunta ta kalleshi, hada ido tasakeyi dashi for the second time da sauri ta dauke kai aranta tace "sai shegen kallon mata mtsww" fitowa daga dakin yayi ahankali, cikeda tsantsan kulawa yace "step aside" dasauri ta matsa gefe ga mamakinta sai kawai taga ya tsugunna yadauki bucket na mop din ya matsar gefe da vacuum cleaner, yashiga nannade carpet din na tsakiyan office din yadaga yadauka yawuce wajen kofa yabude yafitar dashi ya ijiye bakin kofan nan yashigo yasameta tana kokari fara mopping wajen cikin kwantacciyan murya yace "go and change" dan kallon daga kasan riganta har zuwa crocs na kafanta tayi  dake tsiyaya tace "karka damu I can do it banda wani uniform, zai bushe ai" yanda take kallon jikinta tana maganan yake kallo with her voice dake piercing kunnuwa sabida dadinsu, calmly yace "go take them off kisa kayan gida" kawai dan tasan office din mai hotel dinnan ne, sannan shita gani cikin offive din so dole tai assuming shine mai hotel din banda haka data gayamai me ruwanshi da yanda zatai aikinta yabarta tayi abinta tagama mana ha'a, sai gwadamata yanda zatayi yake, sai kawai tawuce kofa batare datace komiba tana zare handglove din, tabude kofa tafita yabita da kallo kafin kawai yazaga yazauna kan kujeranshi na office yayi shiru.

Changing room dinsu tawuce ta chanza kayan tasaka doguwan rigan atampanta brown ne da milk just straight gown babu wani ado ajiki, dan kwalin kayan ta daura aka sannan ta zari gyalenta brown ta yafa daya kara haskata hasken fatanta yayi bau aciki, ta kwashi kayan bayinsu na staff ta shiga ta dauraye kayan ta wanke cinyanta da kafanta da takalmin tama wanke fuskanta kawai gaba daya hakan yasa tai wani haske mai kyau dinnan na bayan ka wanke fuska, tawuce baya ta shanya kayan sannan tafito tana tafiya da sauri sauri sabida tasamu tai sauran ayyukanta tabar office dinshi, tashiga elevator zuwa 5th floor tawuce office din kofan office din ta bude ahankali tashigo tunda ta bude office din ya kafamata ido, the first time daya ganta uniform ne jikinta, yauma haka yanzu ne yafara ganinta da kayan gida, kasa dauke idanunshi yayi akanta, ta taho direct cikin office din batare data kalli wajen dayake bama, zubamata idanu yayi yana kara tantancewa itace dai wannan mara kunyan ta airport, bai cika manta face ba idan yasan mutum, hade fuska tayi batacemai komiba dan jikinta yabata kallonta ake, tadauki moping stick din tafara moping wajen ahankali tana gamawa tadan juyo ta kalleshi karaf suka dake hada ido dauke kai tayi tace "zan iya shiga dakin na gyara"? "Yes" ya amsa calmly hakan yasa kwai ta shiga ta sharo tai arranging bed din dataga ba'a gyare ba, ta wanke bathroom din, kusan 5min tayi sannan tafito tawuce bayin nan office ta gyara shi in 3min sannan tafito tai arranging abubuwan datai amfani dasu tafita dasu waje sannan tadawo tazo gaban table dinshi tasa hannunta tana kwasan wayanta na wajen yanabin white long fingers dinta da kallo that looks so feminine, ahankali yace "wat is your name?" Batare data kalleshi ba tace "Rashida Almustapha" tana maganan tajuya dasauri zata wuce kaman daga sama yace "is your back hurting you naga kin fadi tabaya"? "No it's not" tabashi amsa atakaice tacigaba da tafiya da sauri bataso yayi wani maganan kuma, hartakai kofa tasa hannu zata bude yace "Rasheedahhh!" Wlh batasan meya faru ba hakanan gabanta yafadi chak ta tsaya takasa motsi sabida yanda yakira sunanta, kawai she felt something strange in her dayasa dasauri tajuyo ta kalleshi sake hada ido tayi dashi saikuma ta dauke kai tace "na'am" kusan 30secs yayi shiru saichan ahankali yace "Thank You" Da sauri ta kalleshi zatace thank you for wat saikuma ta tuna maybe na gyaran ne hakan yasa ta gyadamai kai kawai tama kasa magana sabida yanda heart nata yafara racing tajuya tafito dasauri ta kwashi komi tawuce kasa ta maida komi store tawuce taje dakunan dazata chanza duvet nasu takai washing machine takai sannan tahau gyara Allah yasota bata hadu da Madam ba balle ta tambayeta ya akayi tasa kayan gida ba.

Wuraren 6 tafito daga hotel din sai fama take da wayanta dayaki kunnuwa sai cire battery tana maidawa take sabida ya kunnu yaki kunnuwa, ga jakanta goye abayanta. "Hi Rashy" Aisha receptionist dake night zuwanta kenan tai waving nata tana murmushi awkwardly tadaga hannunta saikuma ta maida ta gyada mata kai kawai tawuce tafito waje tana hure huren waya, Munir da Riyad na tsaye awaje wannan karan ya chanza kaya zuwa jumper na milk yadi suna magan kaman daga sama ya hangota tafito tana hura wayanta, yanda hankalinshi da attention nashi yatafi wajenta saida Munir yajuya dasauri dan yaga meyake kallo haka ganin wacce yake kallo wacce kallo daya yamata she looks like worker nasu not guest yasa yace "who is she?" Batare daya dauke kanshi daga kallonta ba yace "my savior" dasauri Munir yadauke kanshi daga kallonta ya kalleshi dasauri yace "kaman ya your savior?" Yana kallonta yace "the girl that saved me from those goons a airport" dasauri Munir yajuya ya kalleta yace "wow the clearner damuka dade muna nema wat a small world ashe anan hotel namu take aiki, but did you tell her"? Girgixamai kai yayi daidai tasha kwanan layin yadauke kanshi yace "No bangayamata" Munir yace "why?" mota yashiga yace "bata ganeni ba" tada motan Munir yayi yace "ai da saika gayamata, How will you reward her yanzu?" Kai tsaye yace "I will ask her kome takeso arayuwa i will grant her any wish take da shi she's part of the reason I'm alive today" murmushi Munir yayi yace "wat got you so angry today?" Yatsine fuska yayi yace "I don't wanna talk about it" ahankali Munir yace "to mutafi gida? Mom tasa an sanar bakada lafiya just to manage situation din harda kiran Dr, tace na tabbatar mun dawo gida tare" hannunshi yasa yasauke glass na window ya lumshe idanu bai sake cewa komi ba, ganin baison magana yasa yace "azumi saura 7days fa bakai approving fund na kayan abincin daza'a rabama al umma da ma'aikatan ka ba" dan ijiyan zuciya yayi yace "i forgot bani file din da pen lemme sign" ahankali Munir yace "bari mukai i will give u yana file dake back seat.

SANYI DA ZAFIWhere stories live. Discover now