28

259 12 0
                                    

💫 SANYI DA ZAFI 💫

        ✍🏻M SHAKUR

EPISODE 2️⃣8️⃣
Gyadamata kai Mama tayi cikeda farin ciki dudda maganan ta baya fitowa da kyau tace "Alhamdulillah Mrs Bugaje wlh ina cikin wani irin farin ciki da bazan iya misalta miki shi ba" murmushi tayi.

Wucewa Riyad yayi yatafi yabar Rasheeda awajen, fitowa Mrs Bugaje tayi takalli Rasheeda tace "scrub in kije wajen Mamanki" da sauri ta taso tayi cikin ICU din bayan tasaka abubuwan Mama na ganinta cikeda karfin hali tasa hannunta asaman hanci tace "ayiri....." saikuma tahau tari da sauri Rashida tazo wajen tace "Mama stoppp" ijiyan zuciya ta sauke tace "Rashida kinsan yanda nake murna kuwa naga aurenki Alhamdulillah kinga na warke tass kalli kafafuna harsun soma sakewa" kafafun Rashida takalla saikuma takalli Mama yanda taketa murmushi is not like tanason auren nan, infact ita bamata taso da burin tai aure ba sannan one single feeling batada shi for Riyad kawai dai daga jiya saita fara kallonshi ta fuska daban compare to before data tsaneshi, jiya ta gane Riyad shi mai sonsu ne ba kyamatan su ba, yana kula da Mama, shine the first person that genuinely know them kuma yasosu ahaka sannan ya tsaya musu, kallonta Mama tayi tace "me mijin naki yace? Ina yaje"? Dasauri ta kalli Mama jin kalman mijin yamata wani banbaran, murya chan kasa tace "wai zaije yakawomin kaya da abinci nai wanka" wani irin blushing da Mama keyi saida Rashida kawai ta maida Mama tv tana kallo is this aure of a thing yakesa Mama farin ciki haka ko wani abun ne dabata sani ba to wani abuma? Is just auren nan, sai murna Mama keyi. Wajajen 4 Riyad yadawo tareda Munir dake rike da basket na abinci shikuma yana rikeda wani paper bag dan babba Mrs Bugaje ta kallesu tace "yauwa I was waiting for you to come inaso na maida Mama wani daki kodan this big occasion she seems very happy, her biggest fear and worry is yartane yanzu data damka maka ita kaman 90% of matsalanta sun tafi" anatse Riyad yace "I prefer private single room" gyadamai kai Dr Bugaje tayi tasa Nurse ta gunguro Mama daga dakin tana fadamusu dakin da za'a kaita, dan satan kallon Rashida Riyad yayi dayaga idanunta sundan soma sabewa, first floor aka kaisu wani single room mai kyau da komi ciki akai connecting Mama da machine na zuciyan still sannan Nurses din suka fita ijiye abincin Munir yayi shikuma Riyad ya kalli Rashida tareda bata bag din, dan kallonshi tayi saikuma tasa hannu asanyaye ta karba murya chan kasa ta yanda dagashi sai ita zasuji maganan yace "shower before I come back, zanje mosque" gyadamai kai tayi suka wuce mosque Mama tawani yunkuro ta tashi kaman maison gulma tace "zonan mugani meya kawo miki? Imaza jeki wankan ke to karya dawo ya ganki daka daka" kallon Mama kawai Rashida take with a huge suprise kaman ba Mama ba, farin cikinta yaki boyuwa, bag din tamikama Mama, Mama ta zazzage tana fito da abin ciki tana washe baki sosai abaya ne kala uku acikin jakan duka black black amman sun hadu duba tsayinsu tayi taga 58 wlh tsayin yarta, sai cream dakuma wasu lafiyayyun turare guda biyu, daya cikin abayan Mama tazaba tadauka tabata tace "ungo wannan zakisa jeki wankan, ki chanza breziya da wando kuma, akara wanke baki ba kyau miji yaji wari" sokoko Rashida ke kallon Mama wai ba Mama ce mara lafiya ba take maganan wani miji? Ita Mama tadauka ta Riyad take she's just after her taji sauki kawai shine burinta, just to make her happy ta karbi wanda ta zaba mata tawuce, akwatinsu tabude tadauki bra da pant tashiga bayin dakin that is very neat tai wanka ta shirya tai alwala tabude turarukan ta fesa wow saida ta lumshe idanu sunada wani irin feminine scent mai dadi, yafa gyalen tayi akai tafito Mama ta bita da kallo sabida yanda yarinyarta takoma tsaf kalan yar masu kudi tai murmushi itakuma ta shimfida dadduma tai salla Mama tace "zoki zubamin abincin bikin ki" dasauri ta juyo ta kalli Mama dake murmushi sai kawai ta tashi tawuce tadauki plate tana bude warners din ta debama Mama tuwo tazauna gaban gadon tana feeding Mama ahankali tace "Mama ai kin warke ko?" Gyadamata kai Mama tayi tace "na warke tass bakiga inacin abinci ba" murmushi tayi tace "thank you Mama dakika warke" tana cikin bata abincin suka shigo dakin duk yanda Riyad yaso ya daure karya kalleta kasawa yayi baitaba ganin abaya yama wata kyau kaman yanda yaga wannan yama Rashida kyau ba, dudda Mama bata cinye tuwon ba but taci rabi, sai satan kallon yanda Riyad ke kallon yarta take kaman tace yadauketa su tafi kawai dai dan rashin lafiya ne, Mama tace "deba kici kema" girgizama Mama kai tayi alamun bazata ci ba, Mama tace "Riyad kaga yarinyar nan batason cin abinci fa wlh sai kayi da gaske" murmushi Munir yayi duk suka zazzauna tareda Mama har magrib sannan suna tafi.

Yau kwanan Mama 3 a hospital she's recovering like magic tun jiya sukai resuming amman kiri kiri taki zuwa taki maganan ma sabida kar Mama tace ta wuce tatafi, tana zaune tareda Mama around 8 na safe Mrs Bugaje tashigo dakin ganinta tareda Mama yasa tace "ba some of yan class naku naga a A&E ana wardround dasu ba? Wani department kike this week?" Ahankali Rashida tace "Gynae" hararanta Mrs Bugaje tayi tace "my friend stand up and go" Mama tace "wai dama sun koma?" Mrs Bugaje tace "tun jiya ma taki zuwa" dakanta Mama tayi abaya bada zafi sosai ba tace "wuce kafin na saba miki" tashi tayi tawuce wajen drawer daki tadauki jakanta taciro gogaggen lab coat dinta, daya daga cikin abayan da Riyad yasaimata ne ajikinta hakan yasa ta warware gyalen tai rolling aka sannan ta warware lab coat din tasaka tadauki stethoscope nata pink ta makala a wuya tadauki pink crocs nata tasa sannan ta dauki turaren ta fesa, tunda tana asibiti yasa bazata  dauki jaka ba, pen ta dauka ta makala a pocket nata sannan tadau wani dan jotter tasa a aljihu, earpiece nata ta dauka zatasa a pocket ta tuna haryau Riyad bai bata wayanta ba kuma takasamai magana ahankali ta maida ear piece din jaka ta rufe, ta rufe wardrobe din sannan tajuyo takalli Mama da Dr Bugaje ke dubawa tace "natafi" "adawo lafiya Amarya" dan turo baki tayi tana kallon Mama sannan tabude kofan tafito tafara tafiya tawuce staircase daidai ta sauka kasa Riyad na zuwa wajen hada ido sukayi yana sanye da wani jumper dark brown daya haska fatanshi yasa bakin glasses a ido, ranan nan Mama tagayamai tanaso ya tsaya akanta tagama karatunta na likita hakan yasa yasan yes she's doing medicine but today is the first time yake ganinta cikin kayan dake nuna ita likita ce, ahankali yakai hannunshi ya zare glasses daga idanunshi yazuba mata mayun idanunshi, da sauri tasauke kanta kasa gabanta na faduwa azuciyanta tace bantaba ganin wanda baya kunyan kallon mace irinsa ba, murya chan kasa tace "ina kwana" batare daya amsaba koya dauke ido akanta ba yace "ina zaki?" Ahankali tace "department namu munyi resuming" yana kallonta still yace "which department" da dan kankanuwan murya kaman ba Rashida ba tace "this week ina outpatient department a gynae" gyadamata kai yayi yace "let's go" dasauri ta kalleshi but haryayi gaba hakan yasa tabishi suka jera har ward dinsu yabita sannan ya tsaya yace "go" agabanshi tawuce tashiga consulting room 2 yadan jima tsaye saikuma yajuyo.

Mama na zaune ita kadai tai shiru tana tunani though good tunani yau take akai knocking kofan tareda sallama daga ciki tai murmushi jin Riyad ne tashigo "shigo d'ana" bude kofa yayi yashiga yana murmushi yawuce wajen gadon yaja kujera yana zama yace "you look good Mama, ya karfin jikin?" Murmushi tamai tace "Alhamdulillah ya iyalinka?" Ahankali yace "Alhamdulillah Mama" murmushi tamai tace "ka kwatanta adalci kaji, mata munada kishi dan haka ka lallashi matarka da kyau kaji Riyad" gyadamata kai yayi yace "toh Mama" cikin farin ciki tace "kaga nasoma samin sauki sosai ana sallamana muka koma gida sai afara shirye shiryen bikinku ko sabida Rashida ta tare gidan ka" gyadamata kai yayi feeling happy ganin how excited she's with the whole wedding yace "Mama kome kikeso haka za'ayi" wani irin murmushi tayi harda dan kyalkyala dariya kadan tace "inaso ama Rashida lalle a hannu amata kwalliya saikuyi hoto kubani amaidashi frame nasaka a falona ina kallonku kullum" dan murmushi Riyad yayi yace "to Mama haka za'ayi" murmushi tayi sosai saikuma tace "tayani daga gadon na zauna" tashi yayi ya taba botur din dake dago gado gadon yataso Mama tai kwanciyan zama ya gyara mata bargo sannan yakoma ya zauna ganin tai shiru tana tunani yasa yace "tunanin me kike kuma Mama?" Ahankali tajuyo takalleshi cikin dan damuwa kadan tace "kana gani nakira mahaifinta na sanarda shi an daurama yarshi aure?" Shiru Riyad yayi, dan murmushi Mama tayi ganin baice komiba tace "I put you in a tight spot ko? Kona kirashi ma bazan sameshi ba yayi blocking dina tun lokacin amman nakan turamishi sakon waya duk ranan birthday Rashida na gayamai yarshi ta shiga shekara kaza kaza dakuma lokacin dataci jamb taci UTME aka bata admission medicine na aikamai sako amman haryau bansan ko yana ganin sakona ba ko baya gani ba" ijiyan zuciya ta sauke takalli Riyad tace "bari nabaka labari na yau Riyad".

SANYI DA ZAFIWhere stories live. Discover now