17

525 19 5
                                    

💫 SANYI DA ZAFI 💫

          ✍🏻M SHAKUR

EPISODE 1️⃣7️⃣
Tana shiga gıda Mamag tace "ke kuma an ina kika tsaya?" Ahankali tace "waje" kawai tashiga ciki zata kwaso kayan abinci dan daura girki Mama tace "kibar girki inada abincin da Riyad yakawomin har yanzu da zafinsu a kula shi zanci, kizo kije school daganan ki wuce aiki, Riyad yace kidawo" dasauri tafito daga dakin ta kalli Mama tace "Mama nifa yau na dauki permission bazanje school ba" saikuma ta taho ta zauna wajen Mama tace "Mama wai kinsan mutumin chan ne"? Mama na kallon kwayar idanunta tace "wani mutumin"? Cikeda mugun hali tace "shi wannan mutumin daya kawomu naga kunatayi kaman daman kunsan juna ne tun chan" dan murmushi kadan Mama tayi tace "a'a amman kawai zuciyata ya natsu dashi kaman na sanshi daga wani wuri, kema kinsan dawuya nake natsuwa da mutane amman shi kawai yayi fuce araina, mutumin arziki ne mutunci da dattaku, yanada halaye da dama nagari, bantaba gani a idanunshi yamin kallon mai wata cuta ba, gakuma yanda yabiya kudin asibiti akamin komi, wanda yamaka Akhairi kasoshi" ranta adan bace tace "Mama ni na tsaneshi" baki Mama tasaki tana kallonta ganin da gaske take, yunkurawa tayi tace "kuma konawa ya kashe miki a asibiti saina biyashi alkawari ne ko zanyi shekara dari ina neman kudin" dan dariya Mama tayi tace "zo ki juye abinciccikan ki wanke kulolin nidai fitina'u" wucewa tayi ta kwasa batai musu ba haka dai tai aikin komi Baba Liman ma yashigo gaida Mama wuraren 1 ta shirya ta tafi aikin sabida yanda Mama tace "saitaje" ga mamakinta ko kallon banza Madam bata mata ba hakama sauran ma'aikatan dudda bataga Hussy ba, kin zuwa office na Riyad tayi tadaiyi duka ayyukanta idan tana gaban desk aka kira ana neman cleaner a so so room ta taje, harta tashi by 6 bata ganshi ba bakaramin dadi tajiba ta tafi gida.

Washegari da sassafe ta tafi hospital nasu yau pediatric surgery departmant zasu to watch not to do itada team dinta zasu, direct tawuce inda suke ijiye bags nasu ta ijiye aka dan musu lectures kadan sannan tawuce tashiga shirye shiryen shiga surgery tsayawa tayi tana wanke hannunta wata tazo itama ta tsaya kusada ita tai murmushi tace "Hi" saikuma ta kalli Labcoat nata tace "Rashida I'm Maimuna but Maimoon ake cemin, tun ranan monday nake noticing naki, can we be friends pls"? Dan tsayawa Rashida tayi tana kallonta like a weirdo dasauri Maimoon tace "please" dan lumshe ido Rashida tayi yarinyar seems very cool and calm ahankali tace "I don't know yanda ake friendship gaskiya" murmushi sosai Maimoon tamata tace "I know and I will teach you, let's go" shiga cikin operation room din sukayi duk hannayensu a sama aka sassaka musu handglove ga yaron da za'ama operation din da baifi shekara biyar ba anyi sedating nashi shigowa surgeon din yayi wanda Babba ne bawai yaro ba aka samai nashi handglove din yawuce surgical table din student Doctors din dasuke su bakwai duk suka tsaya a gefe, Dr yace "yaron nan dake kan table din nan nada hydrocele wazai gayamin procedure da zanbi in this surgery, and ya sunan surgery din"? Maimoon ce tafara daga hannu tabata amsa yace "wrong" almost dukansu saida suka bada amsa yace "wrong" yakalli Rashida dabatai magana ba dan ita bata show off ko a aji, yace "make attempt miss" dan ijiyan zuciya ta sauke Rashida confidently cikin turencinta that is good muryanta kuma makes it sweet a kunne tace "zamuyi Hydrocelectomy surgery to remove the hydrocele daga scrotum din, zamuyi making incision anan....." tafara bayanin procedure din da sai kawai Dr ya tsaya yana kallonta exactly abinda zaiyi tafadi kaman ta tabayi, hannu yamikama head nurse yace "scalpel" samai wuka akayi a hannu yarike yadauki marker yamikama Rashida yace "come close" ahankali ta matso kusada surgeon din gabanta nadan faduwa yabata marker yace "draw the line" karba tayi ahankali taja, to her biggest shock yace "make the cut" dasauri ta kalleshi, confidently yace "I'm here you won't make a mistake so go ahead" dan tsayawa tayi Dr yace "we all start ahaka, go for it, I'm right here ina kallonki" bismillah tayi ahankali ta karba tana kokarin kallon fuskan yaron yace "don't look at his face" ijiyan zuciya ta sauke tareda rufe ido what is her biggest motivation da inspiration na son zama likita? Ahankali tace "Mama! I want to become the best Doctor for Mama! I want to make research nagano yanda ake curing HIV for Mama! I want to make Mama better, I want to be the best Dr in Nigeria da kewaye da al umma zasuyi alfahari dasun samu" daidainan tabude idanunta kawai tashiga cutting Dr na tsaye kusa da ita yace "suction" aka kwashe jinin, wasa wasa da shi da Rashida sukai surgery din nan tass yasake barinta tai stitching yaron up, her stitching style kadai saida ya kalleta almost 10yrs yana aiki in this surgery student Doctors daban daban interns but baitaba ganin skilled yar baiwan Dr like this girl ba ita kanta for now bama tasan wacece itaba imagine abinda take iyayi in year5, sallaman su yayi yakalli Rashida yace "makesure you become a surgeon Doctor R" dan sunnar da kanta tayi batare datai murnushi ba cus she hardly smile outside tawuce tafita Maimoon tabiyota tace "wowwww you are amazing Rash kai! I can never do that" ahankali tace "thanks" dasauri Maimoon tace "let's go grab some drinks" wayanta Rash taciro daga jaka taga 2:30 tace "ohh no I have to go to work" taciro log book dinta da sauri tawuce taje aka mata signing tajuyo takalli Maimoon tace "gobe" bata jira amsanta ba tajuya dasauri Maimoon ta tsaya awajen tai shiru tana kallonta, tace "she's unique, Bilal you loose a rare gem".  Wajajen 3 takai hotel din dan saida ta tsaya tai salla tana shiga tawuce changing room tafito kenan saiga Madam tace "yanzu ne lokacin zuwa aiki i will deduct 5k from salary naki" sauke kanta tayi kasa tawuce tashiga aiki thank God yau Friday gobe ba aikin, tass tagama aikace aikacen ta wuraren 5 Madam ta kirasu hall duk suka wuce, abinci tagani an kakkasa buhun shinkafa, jarkan mai, indomie, madara da milo sugar sai gero da taliya tace "kowa ya tafi da abincin azuminshi gida courtesy of  Oga" sai murna ake, tunda tafara aiki dasu da Ramadan ana basu abinci last year an bata is not new thing amman saitakeji yanzu kaman karta dauka sabida Riyad but kuma idan bata dauka ba za'ayita surutu daman ance tanada girman kai, Madam tace "zansa security su taya kowa fita da nashi sai kuje ku kira keke, Happy Ramadan to everyone" ihu duk sukayi ana shouting thank you Ma sannan ta sallamesu wucewa tayi ta chanza kaya ta goya jakanta tafito taje ta taho da keke tana zuwa security suka tayata lodawa abayan keken ta tafi.

SANYI DA ZAFIWhere stories live. Discover now