13

533 21 2
                                    

💫 SANYI DA ZAFI 💫

       ✍🏻M SHAKUR

EPISODE 1️⃣3️⃣

Gida tashiga around magrib agurguje tai alwala tashigo ciki Mama nakan dadduma hakan yasa ta tsaya kusada ita ta kabbatar sallan.

Tana idarwa cikeda damuwa tace "Mama ruwa yashiga wayana taki aiki wlh" tai maganan tana jawo jakanta taciro wayan cikeda damuwa itama Mama tace "garin yaya meya sameta?" Cikin damuwa tana kara huhhure wayan tace "faduwa nayi ruwa ya kwaromin shine ruwan yataba har wayan" dasauri Mama tasa hannu ta karbi wayan itama tana huhhura duk wani huji na wayan ta maida battery din kozata kunnu amman bata kunnu ba hakan yasa ta tashi tawuce chan wajen yan kayan abincinsu tabude ledan shinkafa tasa wayan ta zuba shinkafa akai tace "bari mugani kozata kunnu idan bata kunnu ba saina tattara kudin dake wajena kije ki sayo wata wayan dashi, kina bukatan waya kodan school, Allah kiyaye bakiji ciwo bako"? Gyadama Mama kai tayi tace "banji ciwo ba" Mama tace "to ai mun gode Allah tashi kiyo wanka kici abinci" dasauri tace "Mama girki kikayi"? Gyadamata kai tayi tace "eh nayi shinkafa da wake da mai sa yaji" murmushi tayi tace "Mama banace ki dena girki ba" ture mata hanci Mama tayi tace "to banji maganan ki ba Anty Rashida" kwashewa da dariya tayi hakan bakaramin dadi yama Mama ba ganinta duk cikin damuwa sabida wayan tasan lissafi take ta yanda zata taba kudin saving dinsu tasai waya dashi kafin takara samin wani kudin fa, rashin lafiyan Mama fa, abinci fa, kudin wuta fa, tasan duk abinda take tunani kenan ganin tayi dariya yasa hankali ta ya kwanta, cikin shagwaba tace "kai Mama nine Anty Rashida" Mama ta kama haba tace "yooo ai hakane, Mama karki kaza, karki kaza, kullum command kike bani yarnan kinga ai kinzama Anty Rashidan" sake bushewa da dariya tayi kawai saita kwanto jikin Mama tace "Mama stoppp wlh ni ba Anty Rashida bane, Mama ina hanaki ne fa sabida karki fadi, kinga kinada yawan ganin jiri, kınada migraine kuma, Mama I have to take care of you gwara namiki komi ko ruwan dazakisha na ijiye kusa dake sabida karki wahala wajen daukowa" tabe baki Mama tayi tadagata daga jikinta tace "jeki wanka kizo kici abinci" tashi tayi ba musu ta rage kayan jikinta tadaura zani ta kwashe kayan da lab coat da kayan Mama data cire yau dasafe tafito saida ta fara wankesu tsaf ta shanya sannan tawuce bayi tai wanka tadawo Mama tabata abincin ci tayi bawani sosai ba batawani cin abinci abin yabi jikinta sannan takai kwanon waje ta kuskure baki ta dawo tahau salla kusa da Mama tana idarwa ta kwanta awajen ko 2min ba'ayiba tafara minshari Mama tai shiru tana kallonta sai kawai tasa hannu tadauki feet dinta ta daura kan cinyanta dudda uban tafiya akasa datakeyi bata da kaushi kafanta still looks very fine ga nails dinta farare kal masu kyau, ahankali take massaging kafafun ayanda ta gyara kwanciya kasan tanajin dadin tausan Mama is just looking at her babu salloli biyar dazatayi arana da zatakai goshinta kasa dabazatama Rashida addu'a ba, banda kiyamun Layli datakeyi kullum, kullum addu'an ta shine Allah yakawo ma diyarta karshen wahalan nan Rashida ita ke ciyar da ita, itace cinta shanta suturanta magungunanta da komi na rayuwan su Rashida ke nema,  babu yanda zatayi ne dan batama da karfin aikin ne da itace zata fita ta nemawa diyarta abinci da komi ba diyarta tayi ba, kullum addu'an ta is Allah ya tsare yarinyar ya tsare imaninta kar wata rana tagaji da aikin wahalan nan tace zata shiga duniya tabi maza dan shine hanya mafi sauki da akebi asami kudi, addu'anta koda yaushe shine Allah yabata ikon kammala wannan karatun likitan, kowani shekara da hayya hayya take tara kudin school fees nata na last year bai musu wani wahala ba sabida tasami aikin hotel din nan ana biyan ta dubu 50k duk wata a nan ta tattara tabiya, fatanta shine Allah sa wannan shekaran na biyar kar kudin makarantan yayi yawa dubada yanda aka kakkara kudin makarantu, hawaye ta share ahankali daya zubo mata bata taba sanin dan Uwanta na jini zai iya juya mata bayaba sabida wannan cutan dudda da ranshi da lafiyanshi, bata da kowa sai Rashida, yau shekaru ashirin da uku kenan tana wannan wahalan tun Rashida na cikinta, ta haifo yarinya cikin wahala ta tashi cikin wahala sannan itama tana rayuwan wahala, batabama yarta komiba sai wahala, babu wanda ya yarda ya auri Rashida, ga yanda yar karaman yarinya ke aiki kaman namiji wata kalan uwace ita, hawaye ne suka kara zubo mata sai kawai ta jinginar da kanyon a bango takalli sama murya chan kasa that is very weak tace "Ya Allah idan mutuwata shine mafi alkhairi agareni dakuma y'ata, idan mutuwata zai cireta daga cikin wahalan nan datake ciki Allah ka kasheni, ka aurar da Rashida gidan dazata huta,  karufama Rashida asiri, ka lullubeta cikin nimarka Ya Allah.
Tadade ahaka yawanci tana boyema Rashida damuwanta da dama sabida kar yarinyar takasa karatu idan kanaso kaga Rashida ta birkice tarasa sukuni to Mama tace kaza namata ciwo tuni yarinyar zata rude, damuwa, tunani ga constant ciwon kai koda yaushe shiyafi damunta, saisa kullum tane asibiti BP ta is high, magungunan BP nema ke cinye musu kudi cus maganin HIV free ake bata a clinic dinsu.

SANYI DA ZAFIWaar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu