14

411 20 0
                                    

💫 SANYI DA ZAFI 💫

         ✍🏻M SHAKUR

EPISODE 1️⃣4️⃣
Wuraren 3 Mama na zaune tsakar gida tana gyaran shinkafa ta kunna radio ta ijiye gefenta saman tabarma tana sauraro taji an turo kofa an shigo hakan yasa ta kafa ido taga wazai shigo bakuwa tayine saitaga Rashida sosai gabanta yafadi ganinta cus bata taba ganin Rashida ta shigo gida around this time ba, kallo daya ta mata tagane tai kuka dawuya ne Rashida tama wani abu tai kuka, ita kadai ke iyasa yarta kuka dasauri ta ijiye tray shinkafan tace "lafiya menene kika dawo dawuri haka?" Murmushi ta kakalo tace "Mama kaina ke ciwo sosai saisa nadawo" tai maganan tana zama kusada Mama kanta Mama ta taba tace "bari na kawo miki vitamin C kisha tashi ki cire jallabiyan kisha iska" tashi tayi tawuce ciki Mama tabi jakanta dayay strange girma da kallo sai kawai ta jawo tabude ganin karikitan ta ne ciki yasa da sauri ta tashi tabita daki tana tsugunne  gaban ganamasgo tana neman kaya Mama tace "an koreki wajen aiki ne"? Dago kanta tayi ta kalli Mama zatai magana Mama tace "karki kuskura kimin karya an koreki daga wajen aiki ne?" Ahankali tace "Madam dina tace yau ne last day na aiki na a hotel dinsu" waje Mama tasamu dasauri ta zauna jin jiri zai dibeta tace "Meya faru tell me everything" Mama tariga ta ganota hakan yasa tafadima Mama komi ba karya, ba karamin baci ran Mama yayi ba tace "sau nawa zan gayamiki ki dinga hakuri arayuwa Rashida eh? Zagi na kari ne? Koko zagi na nunawa ajiki ne? Dan an zageni sai mene" dasauri Rashida ta kalli Mama, Mama tace "yes dan wata ta zageni and so wat dazaki hau fada awajen aikin ki kina hankade Madam dinki har sau biyu mai hotel din gabaki dayama shima kinmai rashin kunya" ahankali takai hannu ta goge hawaye tace "Mama bazan iya daurewa azageki agabana ba ko ace wani abu mara kyau wlh" saikuma tarushe da kuka tace "narasa me nayima yan layin nan duk inda nake aiki sai sunsan yanda sukayi sukaje suka batani su fallasani, wlh kowaye meyi ban yafemai ba" tabama Mama tausayi amman kawai saita wuce tabude drawer tadauko hijabinta har kasa ta saka da sauri Rashida ta mike tace "Mama ina zaki?" Cikin dan masifa tace "ina zani? Ina kuwa zani inba wajen aikin naki ba naje nabada hakuri itama yarinyar a nunamin gidansu naje nabada hakuri, idan babu aikin nan tayaya zaki gama makarantan ki eh? Me zamuci? Dame zaki sami kudin siyan tufafi? Ga wayanki ta lalace baki dawo da itabama that means bata gyaruba duk ina zamu samu kudin nan kafin kisami aikin nan kin manta kalan wahalan dakikayi eh? To zuwa zanyi nabada hakuri" dasauri ta taho takama bakin hijabinta tace "Mama dan Allah dan Allah karkije kinji Mama" fizge hijabinta Mama tayi tace "inda bakiso kisani naje nabada hakuri ai da bakiyi abinda zai tursasani inje ba, yau ko basu karbeki ba dolena naje na bada hakurin abinda kikayi kinma mutanen dake gaba dake reni sannan kin fasama yar mutane hanci da baki" baki Rashida tabude zatai magana Mama ta nunata da hannu tace "kimin shiru anan" ta fiziğe hijabinta tajuya tafita fuu Rashida nada zuciya so tasan yarinyar didn't even realize how important this work is to them most especially towards karatun ta she will do everything ta tabbatar Rashida tagama karatun ta lafiya.

Kafa Mama tasa ahanya tana tafiya ahankali kanta na sarawa amman ta daure cus she knows what school din Rasheeda means to her, she will not allow her to sabotage mean na school fees payment nata ba, she just hopes darajanta zaisa sumata afuwa.
Tanakai junction ta tare keke da taso taje da kafa ne, amman taji jiri na dibanta bazata iyaba, har hotel din aka kaita ta sauko tabiya kudin tajuya ta kalli tamkeken hotel din almost duka inda Rashida take aiki ta sani musamman take binta dan tasan inda diyarta ke aiki incase wani abu yafaru she knows inda zataje neman diyarta amman bata taba shiga wajajen aikinta ba, ijiyan zuciya ta sauke jin yanda heart nata ke beating saita dan natsu kafin ta shiga building din motoci cike anyi parking, hotel din yahadu bana wasaba, karasawa tayi zuwa entrance door din zata shiga from yanda take looking security guard dake gadon kofan shiga reception din yace "Hajiya wakike nema? Idan zancen taimakone Oga yace jibi ranan juma'a za'ayi rabon abincin azumi you can come by 10AM" ahankali Mama tanuna kanta tace "nine Maman Rashida sannunku da aiki, Rashida na aiki anan maybe kasanta, to tayi laifi ne shine nace bari nazo nabawa Oganta hakuri dan Allah akomar da ita sannan nabama yarinyar hakuri" kallon Mama sukayi sannan suka kalli juna kafin daya ya nuna mata kujera dake chan gefe wani plastic chair yace "guest da ma'aikata kadai ke shiga ciki jeki zauna achan Oga nada baki amman zai fito anjima kadan sai a gayamai" Mama batai musu ba tace "toh" wucewa tayi zuwa kujeran dasuka nuna mata ta zauna tabuga tagumi tai shiru burinta kawai karsu kori Rashida addu'anta kenan, gabanta sai faduwa yake cikeda fargaba.



SANYI DA ZAFIWhere stories live. Discover now