26

703 39 15
                                    

💫 SANYI DA ZAFI 💫

        ✍🏻M SHAKUR

EPISODE 2️⃣6️⃣

SO WATA CALLED ME "M SHAKUR KIMANA POSTING DAN ALLAH I WAS LIKE TODAY IS NA BABAN SHAKUR!" TACE NABASHI TAI MAGANA DASHI "BABANA DAN ALLAH KACE TA MANA POSTING WLH KAFİN AKIRAMIN AMBULANCE"
THE POINT OF THIS LABARI IS I APPRECIATE YOUR LOVE, SEEING MUTANE DA DAMA LOVING THIS BOOK GENUINELY IS ABU DA I AM TRULY GRATEFUL FOR!!!
DAD SHAKUR YACE THANK YOU FOR LOVING HIS WIFE WRITE UP AND NAMUKU THANK YOU UPDATE.❤️❤️❤️

SO BETTER LATE THAN NEVER! UPDATE NA DARE💃

As usual wajajen 6 Rashida tabude idanunta da kyar sabida tsabagen gajiya da kuka, kaman ba itane tuntuni ake hayaniyan asibiti ana shiga da fice ba ko bude idanu batayi ba sabida nauyin baccinta, dasauri tamike tsaye ta tafi wajen glass door din ta jingina kanta tana leka Mama trying to see ko tana numfashi, taganta tana bacci and tana breathing, dan ijiyan zuciya tasauke takalli inda ta tashi tasan har tai bacci Riyad na nan koda yaushe yatafi oho wucewa tayi bayi tayo alwala bayan taciro brush ajakanta tayi ta tafi masallaci tai salla tama Mama addu'a sosai tadauki Qur'ani yau ta karanta tasake ma Mama addu'a bayan tagama, tana dawowa Dr Mumina tace "Your Mom wants to see you" jikinta har rawa yake ta gyada matakai abubuwa aka bata tasaka sannan tashiga dakin idanun Mama abude kadan take kallonta dasauri taje gaban gadon ta duka takai fuskanta saitin na Mama tace "Mama ya jiki? Are you fine Mama? Kinji sauki? Sannu Mama na, sannu kinji Mama, Mama ina sonki kinji, mezakici"? Girgiza mata kai tayi bakinta nadan motsi hakan yasa dasauri takai kunnenta saitin bakin Mama, murya chan kasa Mama tace "inaso namiki aure yau!" Dasauri Rashida tajuyo takalli fuskan Mama kodai bata hayyacinta ne kodai she's hellucinating ne? Ganin bakin Mama yacigaba da motsi yasa tasake kai kunnenta saitin bakinta ahankali Mama tace "I want someone that will take care of you koda zan mutu I want to die in peace, I told Riyad ya aureki!" Dawani irin sauri ta kalli Mama gabanta nawani irin faduwa naban tsoro murya chan kasa Mama tace "I trust Riyad! Yanada hankali zai hadaku ku biyu yarike amana! Rashida I need to hand you over to wani tun yanzu da raina kafin na rasu!" Hawaye ne yazubo daga idanun Rashida cikeda damuwa tace "Mama nace bazaki rasuba! Mama nothing will happen to you In sha Allah, Mama yaya zanyi idan kika tafi kika barni"? Kallonta Mama take saikuma tai yunkurin dago hannuwanta biyu dasauri Rashida takama hannuwanta takai fuskanta, hawaye na gangarowa daga idanunta cikin muryan Mama da baya fita da kyau tace "Rashida ina sonki, inasonki sosai my little Rauda, ina matukar kaunarki My Doctor my Rish Rish, my only baby, yarinya na kyakkyawa I love you" wani irin kama hannuwan Mama Rashida tayi saita fasheda kuka sosai, Mama itama hawaye gangarowa yayı daga gefen idanunta tace "I'm scared na mutu banyi handing naki over to anybody ba, Riyad is the only mutum da xuciyana ya yardashi aduniya! Riyad zabina ne Rashida! Riyad is my choice! Riyad is the only man dana kalla namiki sha'awansa as miji will you marry Riyad for me? For my sake? For my happiness"? Kankame hannun Mama Rashida tayi sosai tana kallon kwayan idanun Mama tana kuka itama Mama kuka take, cikin wani kalan murya Mama tace "wat if na mutum? Wakike dashi? I want to hand you over to Riyad kinji, zaki aureshi sabida inaso"? Gyadamata kai Rashida tayi at this point the only burin datake dashi aduniya is taga magaifiyarta ta warke jin kanta take idan Mama tacemata tai kisan kai zata iyayi tsabagen yanda takeso ta faranta mata rai and make her happy, cikin kuka tace "Mama I will marry Riyad sabida kince nayi! Nariga namiki alkawari bazan kara saki a damuwa ba, kome kikeso Mama shixan dingayi I will always keep you happy, Mama dan Allah karki mutu kinji, kinji Mama karki mutu ki banni kinji Mama? Kin tuna namiki alkawari zan zama likita and develop a cure for you? Mama you have to stay alive and wait for me! Mama kinga inaso kixama hope for mutanen dakeda HIV dudda already you're, kinyi rayuwa da HIV for 23yrs, you fought Mama ba dare ba rana, kika haifeni, you protected me Mama look at me yau na girma but banda shi, Mama karki banni kitafi kinji help me fulfill this legacy nawa after all this battle yarki likita Dr Rashida found a cure and Mama is HIV FREE!!! Kimin alkawari you will live for me and zaki jirani har lokacin Mama"? Murmushi sosai Mama tayi kawai tajawo kan Rashida tadaura akan fuskanta ta kankameta sosai tama kasa magana, sun dade ahaka sannan Mama tace "stop crying babu inda zani, I will stay for you, ranan graduation naki na saka exclusive super wax na kafa gwargwaro akai harda glass" dan murmushin kuka Rashida tayi tama kasa magana Mama tace "kiramin Baba Liman" gyadamata kai tayi tadauki wayan takirashi, yace "gashinan zuwa" around 8 Dr Bugaje tashigo duba Mama ahankali Mama tace "inaso nama diyata aure" shiru Mrs Bugaje tayi tana kallon Mama wanda somehow she understand Mama, she knows daga inda decision na Mama is coming from, gyadama Mama kai tayi tace "shine mutumin nan"? Gyadamata kai Mama tayi, Dr Bugaje tace "ba'a bari mutane su shigo ICU sukazo zansa akawoki office dina sai ayi awajen" gyadamata kai Mama tayi Mrs Bugaje zata tashi Mama tace "Mrs Bugaje" dasauri tajuyo takalli Mama, ahankali Mama tace "kina ganin zan warke?" Tambayan yazoma Mrs Bugaje wani iri amman ta daure tai murmushi tadawo tasake zama tace "Mama mutane na mutuwa amusu wanka akusan binnesu ma su farfado balle ciwo, the point is shi cuta da mutuwa duka suna hannun Allah Mama kuma Allah sai warkar dake in sha Allah kinji" daidai lokacin ta hango Riyad ya shigo tareda wani tsoho dakuma wani matashi,  Mrs Bugaje tace "Ina Rashida"? Ahankali Mama tace "taje siyomin abinci dudda na ce mata banson cin komi" dasauri Mrs Bugaje tace "you need to eat Mama, bari na musu magana" fitowa tayi cikeda fara'a ta gaisa dasu tace "bismillahan ku a office dina za'ayi komi" ahankali Riyad yakalli Munir da Buba yace "kuje ina zuwa i need to get something in the car" yayi maganan yana juyawa sukuma sukabi Dr Bugaje.

Samin kanshi yayi da fitowa waje yana kalle kalle just to look for her lura da yayi batanan.

Daga cafeteria take, swallow tasai ma Mama da miyan kubewa sai bottle water ahankali take tafiya dukta rame batada karfi kawai gatanan ne, idanunta har yanzu basu washe ba sunyi ja sun kumbura, gashin idanunta sun tattare, tip na nose dinta is still looking very reddish sabida kuka, lips nata sun kara yin pinkish sosai sabida kuka, she's is looking tiredly beautiful, daidai tazo ta wajajen A&E din taji an kwala mata kira. "Rashy" dasauri tajuyo Bilal ta hango yafito daga parking space yana tahowa wajen da dan gudu gudu sauri sauri yana sanye da riga da wando na jean da riga yazo daidai gabanta ya tsaya cikeda damuwa yace "tun jiya bana online ina jirgi coming back from Dubai ina dawowa kuma nahau baccin gajiya da asuban nan naga message dinki a group ya jikin Mama"? Yayi maganan cikeda so dakuma damuwa soyayyanta nawani dawomai fresh arai, ahankali dan batada karfin hayaniya yanzu ko fada tace "Alhamdulillah da sauki" dasauri yashiga tura hannu a aljihunshi yaciro wraps na kudi yan 500 guda biyu that's 100k yana mata wani irin kallon soyayya smiling and feeling kanshi yamika mata yace "nazo nabaki this and to assure you cewa you're not alone I'm here for you, Dad na UK but he will send his accountant to take care of all the bills kinji Rashy ko miliyan hundred ne Daddy will pay I got yo......." Kasa karasa maganan yayi ganin wani hadadden guy yazo wajen ya tsaya dab da Rashida ga bakin shade a idanunshi yazuba hannu a aljihu kaman military, ko kadan Rashida bataji alamun tafiyanshi ba kawai taji tsayuwan mutum kusada ita dakuma kamshin turarenshi daya cika mata hanci hakan yasa ta dago kanta ahankali ta kalleshi daidai shima yana kallonta batare daya kalli Bilal ba, cikin warm yet controlling voice yace "daga ina kike?" Ya Allah! Wani irin kyau Riyad yamata dayasa takasa daina kallonshi like a little girl innocently tace "abinci naje siyoma Mama" yana kallonta still batare daya dauke idanu daga kanta ba yace "and who is this?" asanyaye tace "dan ajinmu ne" bayabo ba fallasa Riyad yace "let's go" ko musu batayiba tajuya tafara tafiya yama Bilal wani banzan kallo da hannunshi har yanzu yake position na bada komi sannan shima yajuya.

SEE YOU ALL ON MONDAY

SANYI DA ZAFIМесто, где живут истории. Откройте их для себя