16

558 25 6
                                    

💫 SANYI DA ZAFI 💫

          ✍🏻M SHAKUR

EPISODE 1️⃣6️⃣
Rashida tadade awajen tsaye ranta na kunan wulakancin daya mata sannan takoma ciki Mama tace "ina kikaje"? Kudinsu ta nunama Mama tace "naje rage kudin daya kashe mana ne amman yaki kulani" yanda take maganan kasan ranta abace yake Mama bata cemata komiba idan sabone tasaba da halin Rashidan nan na batason ataimakesu, itafa kawai bataso ne sabida gori da wani abu dazaije yadawo.
Har dare duba Mama ake akai akai ana zuwa auna BP da sai sauka yake ahankali ahankali, kawai Mama is at stage da batason damuwa da wani abu dazai tsoratata ko tadamata da hankali ko kadan, tare suka sauko sukai isha'i suna idarwa tazare hijabinta ta ijiye nan kan dadduman yanda kanta kemata nauyi sabida jiya batai bacci ba jiya batasan lokacin data wuce tahau kan gadon ta shige cikin chan bango danta barma Mama dake azkar space nata, taja bargo ta rufa ko 1min bata karaba sai bacci tafara jan munshari juyowa Mama tayi dagakan dadduma ta kalleta sai kawai ta cigaba da jan charbinta tana zikiri,  knocking akayi tareda budo kofan Mama tace "bismillah" ahankali ya shigo rikeda basket na kayan abinci wannan karan yana sanye da jean da riga dasukamai kyau, dasauri Mama tace "Riyad kaine sannu da zuwa" zata yunkura dasauri yace "No Mama karki tashi" yataho inda take ya duka basket din ya ijiye yace "abinci nakawo miki Mama na gida, nasan abincin asibiti ba dadi" murmushi Mama tayi tace "sannu da dawainiya Riyad, sannu Allah saka da alkhairi, ni bandama bakin maka godiya again" dan satan kallon Rashida yayi daya hango a gado tarufa da bargon gadon sabida AC amman kana ganin fuskanta karaf a kan idon Mama dauke kai yayi dasauri daga kallonta yamike tsaye yace "Mama bari naje" dasauri Mama tace "nagode Riyad saida safe ayi tuki ahankali" "Toh Mama" yafadi yajuya hakanan yasami kanshi da sake kallonta yana tafiya harsaida ya bude kofa sannan yajuyar da kanshi ya kalli kofan yafice Mama tadanyi murmushi kadan tareda bude kulan, she just feel wani irin strong trust for Riyad connection that she feels towards the boy yawuce misali, bude kulan tayi taga tuwo da miyan kuka ga man shanu da yaji a gefe da namomi sai kuma 3rd kulan pepper soup ne, shiru tayi tana kallon abincin tana tuna rayuwan datayi abaya ire iren abincin nan sune cimarta dan abincin da Baban Rashida yafici kenan, he always complements abincinta especially pepper soup yace baitabacin pepper soup mai dadin nataba, spoon tadauka ta debo naman takai baki wato duk kalan dadin rayuwa da mulkin dakake ciki idan Allah yaso kwacewa it takes seconds yayi hakan, alokacin bata taba sanin zatai rayuwan da abinci zai gagaresu ba! Ijiyan zuciya ta sauke sai kawai ta ture tunanin kafin kanta yafara ciwo.

Mota Riyad yawuce da Munir keciki yana jiranshi yabude gaba yashiga Munir yatada mota yace "hope she's feeling better tunda you don't want me to go with you" yatsine fuska yayi yace "thanks for the food daka karbomin daga wajen Ammi"baicemai komiba suka wuce gida, ta side nashi suka shiga as usual, parking Munir yayi yawuce yafita dan yaje side nasu shikuma yawuce flat dinshi, zaune yaga Mom afalo tana ganinshi ta taso da saurinta tazo wajen kawai ta rungumeshi saikuma ta dago tahau taba fuskanshi tace "you have not been eating Son, look at you, duk ka rame" ahankali yace "I'm fine Mom" waje yasamu ya zauna Mom ma tazauna tace "kayakuri kayafema Haleematu is not her fault banson kayi fushi da ita over petty mistake, she's just 25 yanzu so kagani she's still a small girl, kishi take batason ka kula mata which nayi supporting hakan" kaman bazaiyi magana ha saikuma yace "Mom she needs to learn to respect my privacy, tadena bincikamin kaya and tadena....." yadanyi shiru Mom tace "tadena me?" Baki yabude saikuma yayi shiru sai chan kuma yace "tadena sharing my private affairs with my Mom" dakuwa Mom tamai tace "she shared private affairs naka dani da duniya tai sharing? Zanje nagayama duniya baka iya kwanciya da matanka kullum ne"? Lumshe idanu yayi sai kawai ya kalli gefe duk Mom na kallonshi sai kawai ta mike tsaye tace "if you don't want that then kaima do the needful, kama yarinyar nan ciki kagani, I just need heir to the king, gabaki dayan masarautan nan jira ake aga matarka ta haihu so kake ace ita juya ce? Yanzu gashi kayi fushi kabar gida 2 nema ko 3days yanzu bakuyiba, I will tell her to come now kuma wlh kamata maganan fadan nan saina sabamaka umarni na baka, tarayya nace kuyi kui bacci good night" tai maganan tawuce tana fita daga daki yabita da kallo wondering wat happened? Mom bata damunshi ada tana duk abinda yaga dama yanzu ko she dictate everything. Tashi yayi ahankali kawai yafada bayi yashiga wanka fitowa yayi ya shirya cikin pajamas yadan gaji so he just wanna sleep kwanciya yayi yana kashe wuta yana ji akai iso Sarauniya zata shigo ta telecom ana neman izininshi dan barinta danna boturin yayi alamun a barta, da saurinta Haleematu ta shigo taci gayu tasaka gold alkyabba wucewa ciki tayi da sallama ta shiga bedroom nashi dayayi sanyi sosai ga duhu hannu tamika zata kunna wutan strictly yace "karki kunnamin wuta" da sauri ta tsaya saikuma ahankali tashiga cire Alkyabban wasu arnan kayan bacci tasaka tataho ahankali ta hayo gadon kawai ta rungumeshi tana manna boobs dinta awuyanshi tace "I'm sorry Ranka shi dadi bazan kara maimaita kallan laifin dana maka ba dan Allah ka gafarce ni kaji".

SANYI DA ZAFIHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin