*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY* (Firdausi S Ahmad)
Wattpad @ *jannahjay8*HIKIMA WRITERS ASSO
© 2019
04
Tun bayan abunda yafaru ranar da Salima tasha mari wani tashin hankalj bai k'ara gittawa ba tsakanin Ahmad da Jamila, yau kimanin kwana goma kenan da wucewar abun, kamar kowanne bayan sati biyu na kowane wata Ahmad yakanje School of healthtechnology dake garin Jahun yimusu lecture, ya shirya cikin shigar suit sai dai ya cire jacket din yabar shirt d'in, bak'aramin kyau yayi ba ya fito daga d'akinshi ya wuce dinning table domin yin breakfast har yazauna akan kujera bata kawo break d'inba duk da cewar goma da rabi tayi, tasan usually 11 yake barin garin Dutse inda kafin 12 yake isa Jahun amman hakan baisa ta tanadar mashi komiba, sai da yayi minti biyar da fitowa sannan ta fito d'auke da uban tray ahannu sai ka rantse abincin dayawa tayi, bai sha haushiba saida yaga zallar bread ne da tasaka cikin k'wai ta soya, tunowa yayi da uban muryarta da tadinga ce mashi bank'arsaba sai kace wani abinci kala daban daban take, bai nuna mata fushinsa afuskaba sai ma cewa yayi da " Sannu da aiki sweety' washe baki tayi tare da gyara zamanta kan d'aya daga kujerun dinning d'in tace "Yawwa My One' shi ya had'a tea d'inshi yasha tare da d'aukar slice na bread guda d'aya sam baiji dad'iba, shi mutum ne mai girmama breakfast d'inshi saboda sau biyu yake cin abinci arana, hakan yasa zakaga gidanshi baya rasa danginsu irish, plantain, yam da buhun flour saboda adunga sarrafa mashi yanda yakeso....
Mik'ewa yayi bayan yagama da slice din daya d'auka ya nufi cikjn palourn ya d'auki jakar system d'inshi mai d'auke da 1set nashi da jallabiya da wasu abu da zai iya bukata irisnu brush da perfumes, dake yakan kwana wani lokacin,har tabarshi zai fita da ita sai taji kunya kuma tace "Kawo na tayaka d'auka mana ko yau ba'ason rakiyata? ' ta karasa da yanga d'an yak'e yayi yace "Haba wane ni na hana sarauniyar mata rakani koba komai nayi bye bye da wad'annan fararen idon naki' Aikuwa tuni tayi masa far dasu ita an yabeta, tsabar shirme bataji aranta duk yawan abincin yaci kwaya bataji zata tambayeshi dalilaba bayan tasan yama cikinshi kad'an. Sallama sukayi bayan yamata kalamanda suka sanyaya mata zuciya ya shiga motar sannan takoma cikin gida. Tana komawa ta d'auki wayarta tayi dialling number k'awarta Samira tana d'agawa ko gaisawa bata tsaya sunyiba tace "Yaushe zaki shigone mu cafcafke yariga yatafi don Allah karkice sai bayan Azahar don zai iya shigowar Yamma fa" daga can bangaren Samira ta amsa tace "Ai nariga nafito nanda minti goma zaki iya ganina cikin gidanki inaso naji labarin ai' dariya sukai gaba d'aya sannan takoma dinning taciga da yin break d'inta
Ko minti goman bata cikaba sai taji sallamarta cikin fara'a ta amsa inda ita Samiran tayi cilli da handbag d'inta da veil kan Sofa ta zauna tace "Zokiban nasha Uwargida kuma amarya agidan Dr Ahmad Jahun' kai wannan maganar da Samira ta fad'a tayi mata zak'i k'warai cikin yauk'i ta taso ta taho cikin parlourn dake dinning d'in na daga dan tudu da zai sadaka da kitchen tace "Ai dole abaki labari kinga wutar da na bud'e mashi cikin school har marin wata yarinya nayi nasan hakan da nayi dole ya tsorata wasu su kyalemin miji, gara da Allah yasa kika fad'amin da wuri ai akan sonshi da ake, tunda nayi hakan bakiga lallab'a dayakemin ba' tafawa sukayi Samira tace "Kai k'awata kin bada wuta kin bada show wallahi, gaskiya kin burge to amma mai kika tanadawa yaran healthtech Jahun? Kodan tunda kika gama da gogaggun yan Jami'ar kinsha round k'awata' nan suka cigaba da hira wanda rabi alwashine kan bazasu bar mazansu su k'ara aureba ko ta halin k'ak'a. Suna tsakiyar hirane Farida childhood friend d'in Jamila tazo, bayan gaisawa suka cigaba da hira tare, kalar kalamansu ne ya bata mamaki inda tadinga basu shawara akan sassautawa kansu k'arshe sai taga zai iya zama masu rikici tayi masu sallama, dama biyowa tayi don su gaisa dake ta shiga Quaters d'in su Jamilane wajan yayarta... Sun dad'e suna hirar har 5 na yamma suna tare
Ahmad dayaga yagama komi akan lokaci shiga yayi gidan yayar mahaifinshi ya karbo nono da fura sai kwan zabi dake ba laifi Jahun suna dashi, yama Jamila text akan zai dawo gida wurin magriba Insha Allah, duk da kuwa har lokacin bata kirashiba balle taji ko ya sauka lafiya. Tana tsakiyar yin sallama da Samira taji text d'in taja tsaki tace " Nabani yanzu sai nayi girki? Ohh kash' dake ita da Samira kayan k'walama suka ci da rana sai awara da suka sayo mak'ot, don Jamila malalaciyace bawai iyawane batayiba tsabar k'iwane da son hira yahanata yi, gyara zaman mayafinta Samira tayi tace " Aikuwa ya kamata kiyi masa koda simple spaghettine da stew, karki manta da d'inkinmu pls "ta amsa mata kan zata fita jibi ta amso masu zata shigo Estate d'innasu takawo mata
KANO
Bangaren iyaye kam sai shirin lefe suke inda Ahamd ya k'ara kasawa ya tsare akan Khairi gani yake tazama tasa, dama can da dokoki kanta dayasa yanzu sai ya k'arasu, itakuma gudun fitina da hak'uri irin nata yasa take kiyayewa. Kamar yanda yakan kasance duk week end ita da Safiyya sukanje wani islamiyya da tayi fice akan karatun Fiqhu da Hadith wanda mafi Aksarin matan ciki masu Aurene, sun je Islamiyyar sun tashi ahanyarsu na dawowa gida suna tafe da manyan hijabansu har k'asa sukazo wucewa ta wajan majalisar samarin da ke kan corner na shiga layinsu, wani saurayi da bai dad'e da dawowa unguwar ba ya hangi Khairi inda take yaji bazai iya shiruba duba da baiwar diri da Allah ya mata, suna d'an wucewa daga inda samarin suke ya tab'o na kusa dashi yace "Baba kaga wata Haja anan la'ilaha illallhau Allah yayi halitta anan, bala'i!!!! ' ya fad'a tare da murza hannunsa bai lura da shirun da nagefen nasa yayiba ya cigaba da zuba " Kaiiii wallahi wannan za'a huta da ita kaga yanda Ukwunta ya cika fammmm!!!... Kafin ya k'arasa yaji sauk'ar naushi abakinsa sauran samarin suka tashi agigice duka yakeji tako'ina gashi bamai niyyar k'watarsa, tsabar zafin nama irin na Adam ko damar kare fuska Saurayin bai samu damar yiba, kan kace kwabo yayi jina jina dashi, sai ga saurayin ya zub'e ak'asa yana don Allah kayi hak'uri ya juya ya kalli abokin dayake bawa labarin yana "Batozi don Allah kubashi hak'uri wallahi bansan k'anwarsa bace' Adam kuwa saboda tsananin k'ulewar da yayine yasa ko magana yakasayi, yanzu jikinsa har karkarwa yake saboda b'acin rai, khairin tasa ce ake irgawa diri har ana cewa cika fam wai harda cewa za'a huta da ita, wani abune yazo ya soki zuciyarsa da sai da ya duk'a k'asa, hakanne yabawa su Batozi damar k'watar gwaska ahannun Adam, sai Batozi yace " Kaima aboki baikamata kake maganganun kan siffar mace ba bakyau, irin haka ai sai ayi zaton kai din mabiyin matane, idan yimaka tayi ai gara ka bita ka nemi soyayyar ta' Adam dayaji k'arshen statement na Batozi sai abun yabashi haushi ya cakumo Batozi yace " kai dak'ik'in ina ne da zaka bashi shawara akan ya nemi matar wani, ko so kake ka nunamin duk zaman ka a unguwar nan bakasan Khairi ce zan auraba' cikin yanayin tsoro Batozi yace "Wallahi mu duka anan muna kallon ai dake ku 'yan uwane k'anwarkace kurum amma kayi hak'uri yallab'ai' sakinshi yayi yace bari nakira commisioner of police azo anan koya muku hankali don inaga nan gaba zaku fara bin matane kuna lalatawa, ai tuni wani asauran samarin wajan yayi hanyar guduwa Adam ya buga masa tsawa yace "tsaya anan wallahi nagane ka ko tafiya kayi sai an kamoka agidanku' rok'onshi sukai tayi sannan ya k'yalesu, daman suna shayinsa kasancewar shan kamshi da kama girma irin na Adam banda gaisuwa ba abunda ke hadashi dasu, yanzuma wani yazo nema wanda gidansu jikin inda ake kafa majalisarne yasa yaji komi.... Adam yana tafiya sauran samarin sukayi kan gwaska da masifa yajamasu bala'i dole yadaina zama awajan, shidai Batozi k'ok'ari yayi ya kaishi chemist aka gyara masa ciwukan da Adam yaji masa....
Adam duk da bala'in da yayi baisa ya dawo normal ba, koda ya koma gida kwantawa yayi yana ta tunanin yanda zai kawo k'arshen wani yake tanka Khairinsa, tabbas ba yau aka faraba domin duk wanda ya kalleta yasan tanada jiki maikyau duk da afanni kyau Safiyya tafita, ammafa in dirine zaka jera mata dayawa bakaga mai irin nataba, baiwar da Allah yamata kenan, tunowa yayi da furucin gwaska na za'a huta da ita, dafe zuciyarsa yayi kai gaskiya gayen nan yacuceni Allah ya isa, ya muskuta ya d'au wayarsa dole na kira Khairi...
Khairi da suka jima da shiga gida tana zaune tana cin sakwara cikin farin ciki don tanasonta sosai taga wayarshi, bayan ta d'auka tace "Salamu Alaikum' dakyar ya amsa yace " Babyluv wato fad'an da namiki kan canza tafiyarki bakiyiba ko, gashinan kinsa wani yana neman ya kasheni, wallahi bana iya jure jin wani yana yabonki koda kuwa halinkine balle halittarki' shiru tayi ita batasan mai ya faruba kuma dayake maganar tafiya ya zatayi da nature d'inta, cikin sanyinta tace " Yaya meye ya faru kuma? Wazai kashemin kai?' sai da ya had'iyi miyau me d'aci yace "Dazu kun dawo daga Islamiyya wani d'an iska yana ta zuzuta jikinki, wallahi banda sun bani baki da sai an daureshi na shekara da horo mai tsanani, shiyasa nace ki canza tafiyarki, za'a canzo miki hijaban Islamiyyar' shiru tayi aranta tana jinjina abun kai itakam Ya Adam har tsoro yake bata wannan wane irin abune, haba dole yayi hak'uri duk munin mace sai an tankata balle amajalisa, kuma ma ai ba ita kad'aice mace Aduniyaba, amma don takwantar masa da hankali tace "To kayi hakan kuma zaiyi k'ok'ari na gyara, amma don Allah kacire damuwar nan bakaji yanda muryarka tayiba, banason jinka adamuwa pls, nasan k'ila bakaci abinci ba i cant forgive myself' kwarai bayajin yunwa amma yanzu da ta marairaice mishi akan yaci yaji wasai donshi yanason shagwaba, yace "Shikenan zanci yanzu' tace "promise? 'Yace "Yeah, promise babyluv d'ina nikad'ai' sai da ta danne dariyarta tace "Bye'...
JANNAH JAY... I would like to see your comments

YOU ARE READING
NAMIJIN KISHI
RomanceKhair gara nak'ara maimaita maki bake ba Aikin nan ke bari na tak'aita maki wallahi wallahi ban yarda dake da Dr Umar ba.... Cikin Kuka tace " Zargina kake? "Hawaye yana zuba a idonta... "Wallahi Ahmad sai kayi nadamar abunda kayi yau, zan tabbat...