*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*HIKIMA WRITERS ASSO
© 2019
06
Kuka sosai Khairi take sanda tashiga gida, bayan gama fad'an ya biyo bayanta cikin gida, kafin nan mahaifiyarta ta tasata da tambayoyi amma tsabar kuka takasa maida mata yanda abun ya faru, sai gashi ya shigo main parlour na gidan, cikin kallon tuhuma Ummi ta kalleshi tace "Adam ko da kai wani abu ya had'aku?' Sai da ya saita nutsuwarshi yace "Kwarai kuwa amma ni nakasa gane mene yasata kuka, saboda solution nasama mata, ta taba baki labarin wani malaminsu dake bibiyarta?' Dan zaro ido Ummi ido tayi bayan fad'uwar gaba da ta ziyarceta tace "Bibiya kaman yaya? Ni bamu taba maganar wani da itaba, amma yimin bayani yanda zan gane' Kallonsu gaba d'aya take da ido kawai, shikuma sai da ya kalleta yace "Ummi yanzu naganshi wallahi tsohone yayi Abba (mahaifin Khairi ) ahaife amma yazauna yana tsara mata wasu zantuka, wannan kad'ai ya isa asan ba Allah ranshi waya sani ko irin munafikan lecturer d'in nan ne masu son lalata yara' Take hankalin Ummi ya tashi tace "Ke khairi kinyiwa mutane shiru kimana bayani' sai da taja zuciya tace "Nifa bawani maganar banza daya tab'amin kar ad'au alhakinsa, bai taba mun doguwar maganaba in aka wuce cikin class ayi tambaya kawai, amma Ya Adam baka fuskanci maganar nan daidai ba, gashinan yanzu kamashi wulak'anci zaka jami, kamanta result dina zai iya samin matsala kuma.. .. Kawai sai tak'ara saka kuka, shiru Ummi tayi shikuma Adam ya fad'awa Ummi exactly abunda yaji, anan Ummi takwantarwa da duka su biyun hankali, inda ta nunawa Adam zai iya yiwuwa bai zo da niyyar cutarwaba amma tunda yariga yace mashi Aure zatayi tana tunanin maganar ta wuce, ita kuma Ummi tace mata karta damu indai dagaske sonta yake bazai d'au abunda Adam yayiba against her result, alokacin ta nuna komi ya wuce mata amma aranta ba haka bane, don sosai tasaka abun aranta tana jin tsoro....
Malam Yahuza bak'aramin jin kunya yayiba kuma baiga laifin Adam ba, kowaye zai iya kawo negetive thoughts idan akayi la'akari da ansaba samun issues a Universities, amma bakomai sai dai zuciyarshi taji ba d'adi mummunan zaton da akayi masa, shi mutum mai k'imane kuma yanada kamun kai ajiyar zuciya ya aje tare da furta "Bazan k'ara son kowacce yarinya ba gara na nemi bazawara zai fi'.
DUTSE..
Dr Ahmad ya bawa Class Rep papers yayi sharing ma students, sai dai kowa da yayi yasamu banda Salima, hankalinta in yayi dubu ya tashi, wane irin masifa ne wannan kenan zata goya carryover tashiga level 4,ina bazata zaunaba, tunkarar Rep tayi da maganar yace zai wa Dr Ahmad magana zuwa gobe, duk da tasa hope sai da ta share k'walla...
Jamila cikin shigar da skirt na atampa da suka amshi jikinta ke kai kawo tana ajiyewa Ahmad abinci a dinning, sai murmushi yake kwana biyu suna d'asawa shida ita komi zam zam, tun ranar daya bud'e mata ido yayi mata fad'a ta saitu, fatansa d'aya ta d'ore serving d'inshi tayi tare da komawa gefe ta zauna,yanda ya saba yi haka yayi mata godiya, sannan yafara cin abinci... Yana tsaka da cin abincin wayarshi tad'au k'ara Jamila ta tashi ta d'auko masa yace "waye ke k'ira? ' tace "Rep 3' yace bani wayar ta mik'a masa, bayan sun gaisa sai Rep yamashi akan wata tayi test bata samu paper d'inta ba ko zai duba record na scores , yace bamatsala zai duba amma yamashi text na admission no da sunanta.
Yana zaune kan kujera ita kuma ta d'ora kanta kan cinyarshi tana game awayarta suna d'an hira jefi jefi abun sha'awa, irin wannan rayuwar yake so agidansa gashi ya fara samu, murmushi yayi tare da shafa fuskarta itama tamaida masa martani, sallama mai gadi yayi yace ana nemansa ak'ofar gida ya fita. Yana dawowa ya tuna da maganar paper nan ya shiga d'akinsa ya duba yaga still ba sunan abun yabashi mamaki, amma ko meye zai ga fuskar yagani ko tayi sai yasan yanda zaiyi da ita...
KANO
Kwana Khairi tayi tana juye juye dama matsalar ta kenan ga tsoro ga saka abu arai, da safe suna fita driver na jansu ita da Safiyya ta labarta mata abunda ya faru amarairaice tace "Don Allah meye shawara wallahi tsoro nake ji kinga sune manyan dake kula da exams na department d'inmu' kama hannunta tayi tace "Ina ganin kawai Addu'a zakiyi sannan muje mu bashi hak'uri har Office, amma ki kwantar da hankalinki, wallahi kina k'ok'ari da Ya Adam' Dan yak'e tayi tace "Shikenan sai mun shiga dai tukun, anya zai barni na dora karatuna kuwa naga abun nashi ya fara yawa' da hirar dai suka shiga school d'in, dake sai 11 zasuyi Exams sai suka samu wuri suke kara karatu, suna wajan Khadija ta kira Khairi taji inda suke, bayan tazo ta samesune Safiyya ta tafi wajan course mates dinta suyi discussion
Tagama mata labarin abunda yafaru khadija tace "Gaskiyane shawarar Safiyya tayi yanzu yau yakamata muje musameshi mubashi hak'uri, amma kidaina ganin laifinshi don Allah yazaiyine kinsan Allah ya haliccemu mabanbanta maybe nashi yanada zafi komi zai wuce indai kunyi Aure Insha Allah' Ajiyar zuciya Khairi tayi tace "In anyi aure kikace anya kuwa nifa wallahi banda karna maida hannun agogo baya da anfasa bikinmu an bari saina gama Degree d'ina, ina ganin kaman zai hanani' jijjiga kai Khadija tayi tace "Gaskiya karma kisake wannan tunanin shifa aure lokacine tunda naki yazo bai kamata kike wannan tunaninba' Khadijace taita kwantar mata da hankali sannan ta samu relief, shikuwa oga kwata kwata Adam sai da ya tsara message mai kyau ya tura mata kafin tashiga exam tare da wishes, bazatace bataji dadiba sai dai ta mashi fatan Allah yasa yarage hali da tayi masa..
Suna gama paper suka nufi office d'in Malam Yahuza tin daga yanayin tarb'ar daya musu suka fara samun nutsuwa suka bashi hak'uri anan yanuna musu bakomi kuma yana musu fatan Alkhairi ita da Adam sannan kuma abashi hak'uri, sosai sukaji dad'i cikin walwala suka koma gidajensu..
F. U. D
Yana zaune a office d'insa tare da Rep akan maganar papern Salima, cewa yayi ya nemo mashi d'alibar yaga face d'inta ko zai ganeta indai tabbas tayi zai sake mata wata, tunda baiga paper dinba kila ahad'awa aka yada mata nata,ya fita yaje ya kirata, cikin nutsuwa ta shiga office din tana sanye da laffaya da ta nade jikinta, sai da ya d'aure fuskarshi sannan yace "ke tsakaninki da Allah kinyi test d'innan?' yanayinta na shagwaba yasa bawuya tafara hawaye rau rau tayi da idonta tace "Tsakanina da Allah nayi koda za'a tambayi wasu cikin class din' Yasan yaganta ranar kawai baiso ya nuna mata yasan da zamanta class dinne don dama haka yake akan kowacce mace cikin school d'in, yace"Shikenan ya wuce then since you wrote my last paper u must be ready to answer any questions" ana cikin office d'in yabata paper yace taja gefe tayi yamata wasu questions nadaban, yabata lokaci..
Suna tafe cikin mota itada Samira zasu Fatara estate sai Samira tace "Kinga na tuno ma k'awata danake fad'a maki mai saida tsumi yar Sokoto tabawa kanwarta sako dake nan cikin F. U. D hostel ko zamu shiga mu karba, shikenan ma mun huta' Sun gama yanke shawara suka nufi cikin F. U. D. Bayan sun shiga sai Jamila taga fitowar Dr daga office sai dai shi baigantaba dake ya juya bayanshine,tacewa Samira "Ajiyeni nan naje nayi magana dashi kafin nan kingama'
Yakoma cikin office d'in kenan ya d'an sunkuya yana had'a wasu papers kawai yaga tashigo ba sallama wanda tana sane tak'iyi, saboda tayi bazata ko zata kamashi da wata Cak ya tsaya tare da k'ura mata ido cike da mamaki inda ita kuma ta cigaba da wulga idanuwanta ta ko'ina acikin office d'in tanayi tana k'ara takowa cikin office d'in.. ....
Firdausi S Ahmad..

YOU ARE READING
NAMIJIN KISHI
RomanceKhair gara nak'ara maimaita maki bake ba Aikin nan ke bari na tak'aita maki wallahi wallahi ban yarda dake da Dr Umar ba.... Cikin Kuka tace " Zargina kake? "Hawaye yana zuba a idonta... "Wallahi Ahmad sai kayi nadamar abunda kayi yau, zan tabbat...