EPISODE 35

830 58 20
                                        

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                          

loadιng...........✍🏻

*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*

© 2019

35

Rashin Jamila agida bai damu Ahmad ba tunda dama koda tana nan wataran sai ahankali, sai dai zaman shiru ko bakomai wataran zakaji motsin mutum, kullum sai dai yaje gidansu ya karb'o abinci, ya dawo ya raba dare yana tad'i awaya, yawanci da mutum biyu zakaga ya d'au lokaci yana waya sai kuwa Umar, su Umar 'yan taya b'era b'ari tunda Jamila ta haihu ya k'ira Ahmad yace " To yanzu lokacinmu yayi zamu making move to that girl"

Ranar suna set na akwati aka wa Jamila daga gidansu Ahmad haka shima yaje algazaru ya samo mata mini set ita da yaransa, abun sai wanda yagani bikinsu atsare, sai da akai shagali kaman wani kamu da rabon robobi da mug mai sunan jariri Muhd Jahun, sunan baban Ahmad kenan bakinta har kunne sunan uban miji, take Chief of justice Muhd Jahun ya bawa takwaran nasa kyautar gida, nan danan Jamila takeji tayi karfi adangin Ahmad tunda gashi tayi uban miji...

Kwance take suna waya da Sayyid, sai sako mata maganar Adam take tana kaucewa don kwata-kwata batason maganarshi ayanzu, dake su basusan wainar da ake soyawa ba, daga shi har Hafiz d'in dakyar take daurewa take bashi  amsa, kiran Ya Ahmad ne ya shigo batasan sanda ta saki fara'a ba,  hira sukai takai ta minti goma sha biyar rabi akan tafiyartane don nextweek end zata tafi, kwana biyu sai jadda mata tahowa Ummi keyi ita takasa gane dalilin hakan, dole tafara shirye-shiryen tafiya,sai da Adam ya zauna yamata typing long text akan bada hak'uri da neman yafiya, sannan yace ta k'ara bashi chance insha Allah bazatayi regretting ba, ko replying batayiba ta watsar dashi..

Wani sabon abu kuma kullum sai an kirata da new number ak'i magan haka zatayita hello-hello aki amsa wa, wanda wannan aikin Adam ne zuwa yayi shago ya sayo sims har mai shagon sai da yafara zarginsa, ganin kullum sai ya sayi guda biyu sai kace wani mara gaskiya, dalilin hakan kuwa shine in aka kirata aka ki magana to in aka jima taga kira da number sai tak'i dagawa shikuma sai ya sake saka wani new sim din ya k'irata, kawai yaji muryarta ma kwanciyar hankaline

Kullum Adam sai yaje gidansu ya gurfana gaban Mama akan tasa baki kan Komensu da Khairi, ta murshine idonta da toka ta yab'a masa maganganu masu ciwo, amma saboda shi yake so haka yake cijewa ya k'ara dawowa yanda kasan d'an maula haka yake zubewa kasan falo yana mata magiya, gwanin tausayi wataran ma tashi take ta shige bedroom d'inta ta rufe k'ofa tace masa in ya gaji ya tafi, ya faru yakai sau biyar rannan sai ga Jidda tazo gidan, agaban idonta yasha wulak'ancin nan har sai da ya bata tausayi, har cikin ranta duk da tasan bai kyautawa Khairiba amma tana ganin duk duniya bawanda zai sota kamarshi, kuma tunda yayi nadama ai shikenan, tana yin sallama da Mama ta shiga gidan su Khairi ta sanarwa Ummi abinda ake ciki, anan itama Ummi tace taji hakan na faruwa wanda baya mata dadi, don duk wanda yaga yanda Adam ayanzu ya koma sai yayi tunanin wani ciwon ne yakamashi, ya motse ya fita hayyacinsa ko tsabtar kirki baya iyawa saboda rashin nutsuwa, amma zataje suyi magana da Mama akan haka suka rabu da Jidda..

Adam yana tafe yana tsiyayar hawaye dawowarshi kenan daga gidansu, inda yake tuno kalamin Mama tana cewa " Itafa tagama shiga lamarinsa aduniya, tunda ya runtse idonsa ya saki Khairi bayan tulin rashin kirkin da yamata ta rufe masa sirri, amman sai da yabankada mata rayuwa tunda ya saketa yamaidata bazawara, don haka yaje wahala yanzu ya fara yinta arayuwarsa amma kada ya kara tunanin ita Hafsatu zata kara shiga rayuwar auransa, babu hannunta yaje duk inda zaije ya nemo hanyar komensu" buga goshinsa yayi da hannunsa yana fad'in " Adam ka cuci kanka gashi tun ba'aje ko'inaba soyayyarta na neman kaika ga halaka" shikad'ai yasan ciwon da zuciyarsa kany, lokuta da dama sai yaji kewayen zuciyarshi na kud'a especially idan yana tuno rashin yiwuwar dawowar Khairi arayuwarsa, a ahaka ya k'arasa gidansa ya ciro key ya bud'e,  bai damu da knocking ba don tunda ya tsumduma kogin tunanin da rashin nutsuwa Abida ta sake samun lasisin yawo, yanzu ko takanta bayabi damuwarshi kawai Khairinsa, shiga yayi ya kwanata yana sak'e-sak'e aransa, yafi awa d'aya ahaka sai ga Abida ta shigo d'akin daga ganin yanayinta daga unguwa take, don kwalliya ce ajikinta sosai, ya fara zarginta tun kwanaki dayaga yanda take warewa wani guy da tace cousin d'intane, amma sai ya kawo na mujiya ya zuba mata shi kansa sai da yayi mamaki, bayajin haukar kishinta kaman na Khairi shiyasa ya tabbatar so shine silar Kishi, amma duk da hakan yana jin kishi sai dai irin wanda zai iya kawar dakai, bai mata maganaba sai ta hau 'yan kame-kame " Meyake damunka naganka wani iri?" bayason magana da kowa ayanzu saboda haka yace mata " Bacci nake ji kawai ina son na hutane" daga haka ta kama bakinta tayi waje, dama daga wurin Zuma take don soyayya suke ba kama hannun yaro ko sanda suna saurayi da budurwa bai kai hakaba, kana ganinta kasan bata da damuwa har yar k'iba ta k'ara..

NAMIJIN KISHIDonde viven las historias. Descúbrelo ahora