EPISODE 50

1.4K 80 13
                                    

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

loadιng...........✍🏻

*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*

© 2019

50 🔚

Bak'aramar wahala tashaba sai dai Alhmdlh asbubar fari ta sauka tasamu d'a namiji sak mahaifinsa farine dai bai kai na Adam ba, fad'in farin cikin da family suka shiga kaman b'ata bakine, kafin gari ya waye har sunzo inda aka tafi da ita gidansu Adam nan dai inda tayi jegonta na farko, yan uwa da abokan arziki sai b'ulb'ulowa suke ga yan Asibiti, tana ganin tarairaya awajan ogan, alokacinne kuma ta dage da cin farfesu da su nono da zuma mai dumi, sam bata k'i gashin da ake yiba takan hau garwashi again shima don gyara, shikuwa Adam kusan kullum sai an koreshi ahakan ma cikin dare zai k'irata awaya sai bacci ya saceta yake k'yaleta, kullum sai yazo da safe kafin ya wuce office, soyayyar da Adam kewa babyn ko ita Khairi albarka don cewa yayi sai anyi suna special yanda yarasa baby sau biyun nan dole ya godewa Allah..

Ahmad yayi alk'awarin kawo matansa suna aikuwa haka akai suna yakama ranar Asabar ya taho dasu da safe, inda aka tsara wuri mai kyau Khairi tafito tas acikin lace mai azabar kyau shima baby an masa kwalliya cikin kaya Navy blue masu kyau, yaci sunan baban Khairi Aliyu kenan, an ci ansha hatta su Safiyya da Khadija kwalliya sukai na kece raini, can na hango su Maryam tafida da matan su Sabeer da Ak don sune yan rabon suverniors, Jamila da Saleema kuwa bazakace kishiyoyi bane don Ankon wani paper lace sukai da Ahmad ya musu tare, sunyi tsaf abun dai ya k'ayatar sai wanda yagani, sai dare suka keb'e dasu Saleema inda zaman nasu rabi na karuwane daga Khairi, lokacinne kuma Jamila tak'ara ganin haukar da tayi abaya, adaren suka koma dutse don sai past 9 suka isa gida...

Duk wani gyara daya dace mace tayi wanda bana cushe-cushen haukaba Khairi nayi, yanzu tasamu kimanin Sati uku da haihuwa, Adam yagaji soyake ta dawo ya rasa yanda za'ayi ya tari Mama da maganar, in yazo yana mutsu-mutsu yanason mata magana sai ta kawar kuma tagane inda ya nufa, kamar yanda yanzu ya sabarwa kansa cikin dare in yakasa bacci haka zaisa Khairi ta tashi ta kunna data suyi ta vedio call, yauma hakan takasance tana baccinta mai dad'i taji vibration na wayarta dole ta tashi bata damu da taga waye ba don tasan oganne, muryarshi cike da damuwa yace ta kunna datar ta, bayan ta kunna ya ajiye wayar yana jingine yana kallonta yace "Wai Babyluv don Allah bakya tausayina ne? Nikad'ai nake haukana ma kenan baki damu kidawo gidaba"murmushi tayi tace " Kaima kasan nima nayi missing dinka, ba yanda zanyine" jan tsaki yayi yace " Ba yanda zakiyi fa kika ce? Haba sai dai in bakiyi niyyaba wallahi" tace " To me kake so nace? Naje nace musu zan tafi ko ya?" yace " To in kince hakan laifine ko sab'o?" tace " Nidai gaskiya bazan iyaba" fushi yayi ya kashe wayarsa ita kuwa takoma baccinta, washegari da yazo yaje ya tunkari Mama tace sai tayi kwana talatin da biyar ko talatin duk yanda tagani, haka ya zungumi baki ko naiman Khairi baiyiba ya fice, ita kuwa da tana jinsu da Mama ta dinga dariya...

Bayan kwana biyu da hakan ya je yasanarwa iyayen mazan kan ko zasu bada baki bako kunya, aikuwa take Abban Khairi ya saka baki dan sawa yayi aka kira Mama, bayan wasu mintuna sai gata ta shigo d'akin da Khairi take tasan yana nan ta sa hannu harda masa dundu tace " Rasa kunya harda kai k'arata ko? To jibi kazo ka kaita yawan dangi sannan washegari kuje Jahun da ita sai ku tattara ku kama hanya ku tafi gidanku" dariya ce ta tasowa Khairi na dundun da aka masa sai da Mama tafita ta kwashe da dariya harda rik'e ciki b'ata rai yayi yace " Au dariya ma kike ko? Ai koma meye akanki akamin kuma sai na fanshe kayana" Hakan kuwa akai sai da suka zaga dangi taje Jahun tadan lalleka dakema wasu sunzo mata suna don haka sunje Dutse wajan Saleema, bayan dawowarsu daga Jahun an gama mata shirin komi sai komawa gidansu..

*DUTSE*
Ba laifi yanzu gidan Ahmad ana zaman lafiya, kuma yakan sakewa Jamila duk da bata isa kamo Saleema fagen kula dashiba da sanin makamar miji, don Saleema kilibibin ta ya isa da sanin salon jan ragamar miji, zaune suke gaba d'ayansu suna kallo Baby Aslam sai gwalangwalantun sa yake ak'asa su suna kallon wani movie, abun gwanin sha'awa dake yana d'akin Saleema ne tana daga gefenshi gefen cinyarta na jikinshi, sai da tasbihi Jamila tasamu kishin daya taso mata ya kwanta don bazaka raba mutum da kishi ba, ita kuwa Saleema bata daukar hakan a komiba saboda ai mijintane da dai bata dakinsane bazatayi hakan ba, yanayin rayuwar gidansune yasa bata jin komi dom Mummy ko agabansu tana iya yin haka akusa da Daddy tsarin turai ne su, shiyasa take da salon abu dayawa, sai anyi abun dariya zakaga da wani salo tayi lu jikinsa irin dariyar nan taci k'arfinta sai kaga shikuma yana d'an tuttureta da salon wasa yana cewa " Kwanan nan za'aji kashina ya goce, duk kinvi kin takurawa jikina" da salonta ta kalleshi ashagwaba tace " Yanzu kaman ni har na isa karya maka k'ashi Hero nikarka had'ani da Ummu gaskiya" itakam Jamila tashi tayi ta d'auki Aslam asunan zata je ta gyara masa jiki don dare ya fara yi ta musu sallama, kaman jira yake tabar wajan yad'an kishingida kan couch d'in ya birkitota samanshi gaba d'aya yace " Kwana biyu so kike kidinga overact ko?" zaro ido tayi tace " Kaman ya kenan? i thought this is normal things that each one of us can do" yana lasan gefen kunnanta yana cewa "No.. No kawai ki rage karki ballo mana rigima i know My Woman in ke kishinki baije kaman nata ba ita tanaji, beside in sona baida yawa aranki kaman nata baza kike jiba amma ita ina ganin kaman mood dinta na canzawa, kuma banga laifintaba arage please Baby in mukadai ne you can do morethan this" shiru tayi tana nazari sai kuma tayi dariya gaskiyar shine amma tani wani kishi ya taso mata har yana ikirarin Jamila tafisonshi wato ma yafi shaidanta kanta, amma sai ta dake (barikin iya takun rayuwa kenan) tace " Insha Allah Hero zan kiyaye, dama hakane kowa da yanayinshi kaga" amma daga baya sai daga baya suna other room bayan sunagama shan love take mashi mitan ashagwaba " Yanzu Hero baka yarda da son da nake maka ba ko?" yace " Yaushe nafadi hakan? " tace " Dazu mana kace ma bana sonka fa" yace " Niba haka nake nufiba, dama don naji me zakice ne amma nasan kina sona just nasan harda yanayin rayuwarki yasa kika dauka bakomi bane, kuma kinga so shine silar kishi kila nata yafi naki dats why bata iya controlling kaman ke" ya karasa da sigar zolaya sai tashiga kukan tab'ara tace " Kawai nasan ni na sameta sannan nasan kuna shiga other room ma meyasa dan tana shige maka afalo zan damu kaina, amma kasan ina da kishi just ina mantaining ne" Dariya yayi yace " Is that so? " sai ta hau tureshi "Tunda baka yarda bama bari na tafi dakina" ta mik'e da gayya tayi hakan don kuwa tasan yakanso ganinta da bra and pant ta mik'e tsaye ta janyo rigarta dake gefe wai zata tafi dakinta adaren, aikuwa tuni ya sauko ya rungumota ta baya yana lallashi daga baya ta koma sukai baccinsu.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Dec 06, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

NAMIJIN KISHIWhere stories live. Discover now