🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*© 2019
Wannan shafin complete na masu voting da comment ne.. Im appreciated
21
Sati Biyu Jamila tayi bata k'orafi akan duk wasu al'amura da Ahmad zaiyi da jikinta, in ka k'are masa kallo har d'an kumatu ya k'ara, shikuwa ya dage da shigo da fruits da su zuma abunda yasan kan k'arawa mace ni'imah through cima, itadai burinta d'aya wata ya cika da karb'o magani taje amata test taga ko akwai, don an fad'a mata gaskiya malamin yawanci in ya bada magani akan dace 99 percent, yana zaune kan carfet ya mik'e k'afafuwansa ya baza takaddu yana aikin result saura kwana tara students su dawo zasu kafe masu result before dawowarsu, ita kuma Jamila tana kitchen tana had'a banana shake aka doka sallama falon, ya gane muryar wace k'anwarsa ce Naja'atu cikin sakin fuska ya amsa mata ta shigo cikin d'auke da bucket k'arami da had'in gyada nayin kunu, sai da tafara gaidashi sannan ne yace "Wannan sak'ona ne ko kuwa na wani gidan" Dariya tayi tace " Anya kuwa nakane, ni banji sanda ka nema ba, gidansu Yaya zan kai" yace " Shikenan tunda sai an rok'a akeyi da mutum idan na shiga gidan gobe sai na ce nima ahad'amin" daidai lokacin Jamila ta shigo falon fuskarta ba yabo ba fallasa suka gaisa har tana tambayar Naja'atu Jahun, dake satin da ya wuce taje musu kwana biyu, tashi tayi tace "Bari na wuce saboda kaiwa sak'on, sannan Umma tace tanason ganinka cikin satin nan" yace "To shikenan ba matsala ki gaidasu" ya zaro 2k yace gashi tasa kati ta amsa tamishi godiya, ita kuwa Jamila tunda taji ance Umma keson ganinshi gabanta ya yanke ya fad'i tsoronta d'aya kar ace maganar Haihuwa za'a mishi, kamar yanda Samira ta nuna mata kan dangin mijinta zasu iya kawo mata cikas su saka ai mata kishiya, idonta tuni ya kawo ruwa, yafi minti biyu yana rubutu ya d'ago idonsa yaganta cikin wani yanayi cikin nuna kulwa yace " Ya yadai wani abu ya farune?" Jijjiga mishi kai tayi yace "Gashi yanayinki ya canza da alama kuka kike sonyi, tunanin me kike?" yanzu ya mik'e ya nufi kan kujerar da take ya zauna akan hannun kujerar ya janyo fuskarta zuwa facing d'inshi yace " C'mon indai akan haihuwane yakamata ki kwantar da hankalinki, Allah bai manta damuba matuk'ar kinga bai bamu yanzuba lokacin mune bai zoba" Sai hawaye shar shar ya rungema kanta ak'irjinshi yana mata maganganun lallashi ita kuwa kaman ansaka ambaliyar ruwa a idonta, hangowa take kawai anmata kishiya ya zatayi? ....
KANO
Tun bayan bikin Safiyya sai yau ta shirya dake yakama Saturday Adam zai kaita yini, sanye take cikin lafaya da ta mata kyau sosai, tun ahanya yake nanata mata ba ita ba fitowa tunda dai tasamu ya barta ta nad'a lafayar, itadai sai binshi take da "to' don bak'aramin dad'i take jiba, zasu had'e da k'awayenta sunyi da Khadija ma zata zo gidan amaryar next month kenan, yana parking cikin d'oki tayi cikin gida da d'an gudunta " Aahh wane irin abu kike kika sani ko maigidan yana nan" burki tayiwa k'afafunta sannan ta saita kafafunta suka shiga tare, sai da sukayi sallama sau uku sannan amaryar ta fito cikin kwalliya mai kyau ta nufi Khairi ta rungumeta sai ga Ya muhsin shima ya fito, da alama fita zaiyi tunda yaji jiya tana Khairi zata zo yace bazai zauna ba yasan zasu cika gidan da hayaniya ne, sai da ya zauna suka d'an tab'a hira da Adam sannan suka fita gab'a d'ayansu suka bar matan agidan, kamar jira suke suka b'alle bakin hira anan ne Safiyya take cewa Khairi "Dama haka auran yake? Gaskiya Aure wata makaranta ce ta daban da baka isa kagane taba sai ka tsinci kanka aciki" Murmushi Khairi tayi tace "Kwarai kuwa ko ya wani zai zauna ya baka labari bazaka ganeshi kai tsayeba, Ina fata dai komi lafiya" suna cikin maganar sai ga Khadija ta shigo nan dai gida ya d'au hira, rabin hirarsu ya ta'allak'ane ga shawarwari da kuma abunda ya danganci kitchen, sannan ne suka fad'a kan hirar bikin Khadija da za'ayi...

YOU ARE READING
NAMIJIN KISHI
RomanceKhair gara nak'ara maimaita maki bake ba Aikin nan ke bari na tak'aita maki wallahi wallahi ban yarda dake da Dr Umar ba.... Cikin Kuka tace " Zargina kake? "Hawaye yana zuba a idonta... "Wallahi Ahmad sai kayi nadamar abunda kayi yau, zan tabbat...