EPISODE 27

843 49 11
                                    

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                          

loadιng...........✍🏻

*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*

© 2019

27

Sati yafi biyu rabon da wani abu ta hadata dashi, iyakar bukatuwa yakai gashi at times sai kaga Students sunyi shigar banza, yar dauriyar da yake tanemi k'are masa, saboda shi ba mazinaci bane in ya dauko dakon bukatarsa ya kawowa Jamila ita gamai ciki sai ta tsiri ciwon baya ciwon kafa ciwon mara, haka zatayi ta lissafa masa su, yau da ya dawo ya samu abincin kan dinning shinkafa da miya ce da nama, duba fridge yayi yaga da cabbage da sauran vegetables, zama yayi ya yankasu fato- fato don bai saba ba, ya zauna ya ci abinci duk lokacin kuwa mai ciki tana kwance kan kujera wai bayanta ne ya rik'e, haka kawai taji sha'awar cin coleslow daya had'a, gashi dan kadan yayi don daidai shi yayi, tab'arewa tayi akan sai ya bata yace " Bakisone shiyasa baki yankaba, yankan vegs ko akwance Wallahi kina iya yi, banson mai kike so kizamaba, kefa baki aman masu ciki kuma kina cin abinci so why the laziness? Haba" sai  ta shiga ruwan hawaye ta shiga mitar baida tausayi ai kowa dakalar ciwon dayake experiencing during pregnancy, abunda bata saniba shine yanzu kwata-kwata yagaji da iya shegenta, da duk taurin kanta baya kaiwa sati bai samu hadin kantaba, jiki da jini da lafiyarsa kuma yana jin abinci mai kyau ace bazai ajiye bukatarshiba, yana tsaka da tunanin ne yakai hankalinshi ga floor na parlourn yaga tabbas ba shara, karo na hudu kenan bata shara, yanzu yakai bedroom shiyake gyarashi, amma wannan baya damunsa don dama yakamata yake tayata haushinsa dayane  kawai rashin bashi hakkinsa, atleast ko wani abu da zaike sauke masa damuwane tayi, ranar haka ya kwana yana kunci in ta jashi da hira kan kayan babies sai ya kyaleta.

KANO

Aranar da akai kamu haka Adam yakasa ya tsare 2 hours kawai tayi ya taso k'eyarta sai gida, dinner yace ta yan matace dole ta hak'ura sai bayan kai amare taje gidajen nasu, yasha kuwa mita daga dangi har kaka sai da ta wankeshi tace so yake ya rabata da mutane.

  Yana zaune fuskarsa ba annuri ta fito da riga da zani na lace daya saya mata kwanaki  kallonta yayi yace " Gaskiya wannan ma baiyiba, ki sake" takoma ta dora mashi laffaya shima yace bai yarda ba,haka tasa kaya kala  hudu karshe ta dauko Dubai abaya mai budewa da ta saya wajan Algazaru,tsarinta kaman za'ai bubu amma da different style sam bata kamataba, ta dora mayafinta, anan ne yaga tamasa gashi dama bata yi wani kwalliya sai dai tayi fresh tayi kyau, gashi tayi dumurmur saboda cikar da ciki yasata, ahaka  yaje ya ajiyeta cikin Tahir guest palace nan ne taron zai wakana

Hall ne k'ato cike da manyan Doctor's da manyan Lab officials da kananu as representers amma basu da yawa, ciki kuwa harda Khairi  kansu ya d'au caji, don bakaramin programme akeyiba awurin abune daya had'a four states na na Northwest Kano, Katsina, Kaduna sai Jigawa, harda wasu turawa na wani organisations, harka ce ta boko  tsantsa awajan, yanzu k'arfe hud'u da rabine dawowarsu kenan daga sallah, aka dora da jawabi, kana kallon Khairi kasan tana cikin wani yanayi, don wani message ya turo mata, akan lallai ta ji tsoron Allah ba ruwanta da cewa zatayi wani bayani, matuk'ar ba dolene sai tayiba, duk damuwarshi karta fita bayani aga hannayenta da lalle, sannan kuma bayan in bata fita ba ai wani bazai ma lura da zamantaba, shiru tayi ta k'ara bud'e message d'in, daga bangarensu harda Maryam Tafida H.O. D, da wani Mus'ab, cikin kulawa Maryam ta rada mata "meke damunta ko baby ne yakeson fara cin abinci" murmushi tayi ta ce A'a, batun  yau ba Maryam take lura da Khairi na fama da matsala kan aikinta da kishi, duk da Khairi  bata tab'a zama ta bata wani labariba, ana haka sai manyan cikinsu sun shirya tambayoyi wanda ya sani zasuke amsawa, abangaren Doctor's Dr Kibiya ya amsa guda ukwu, inda su amatsayinsu na ma'aikatan asibiti d'aya sukaji dad'i, ana haka aka fara tambayoyi kan Lab, nan fa kake jin answers daga sauran states da wasu hospitals na cikin Kano, haka yasa H.O. D ya fara kallon team d'insa, har sai da ya rage saura 2 answers na bangaren Lab basu amsa ko d'ayaba har baturen dake jefa amsar yana cewa nasara nasara, shahada tayi ta mik'e ta isa ga stage ta shiga bayani, sosai ta burge especially in aka dubi qualification d'inta shine least, don koda akace zata sai da taga kamar wajan yafi k'arfinta duk masu degree afannin ne sai sama, kamar yanda akewa kowa tafi haka aka mata, baturen wajan ya kalleta yana " Thank you young lady" shi yaganta karama baima lura da cikinta daya tashiba.

Bayan magriba suna zaune suna taba hira iya team dun asibitinsu, haka suna tattaunawa kowa sai yabonta yake, dama Khairi da son fannin nata taji dadi, kowa yana encouraging dinta akan kara karatun, sai dai aranta tana basu san wanda zai dakatar da itaba, amma saboda tana son abun tana yawan research kuma lokuta da dama in suna aiki cikin Lab in taga abunda bata saniba takan tambayi H.O. D, daga nan suka koma Hall inda zasuyi taking dinner, abincine kala-kala da drinks snacks wasu cimar ma ba irin namu bane, haka taronsu ya cigaba da gudana sai 8 suka tashi, suna tashi suka fito gaba d'aya, kusan kowa yana da mota ga gari ya had'e bak'in kirin, wayar Adam taki shiga saboda tsiyar network har Dr Kibiya ya wuce ya dawo don hanyar gidansu daya sai dai shi yana gabansu, anan sukayi deciding ya tafi da ita sai da suka shiga mota H.O. D ya shiga tashi, sannan su Maryam ma, sai yau take jin haushin kanta da Abbanta yaso bata karamar Vibe tak'i, wai har tana cewa Insha Allah da Salaryn ta zata saya

    Abincin da ya karbo daga gidansune agabansa ya kasa ci, saboda tsabar bacin rai an nuna  taron nasu a NTA ne, yaganta kan stage " Wato tsabar taurin kai irin nata sai da taje tayi surutu ko, shikuma wannan mai jan kunnen uwar me yake gaya mata?"shi kad'ai yake sumbatu can kuma ya duba agogo yaga takwas harda yan mintuna, duk da yasan tace sai 8 amma sai da yaji haushi yaja tsaki ya fito kofar gida, anan ne yaga yanda hadari ya taso sosai da alama in ruwa ya b'alle za'ayi kaman da bakin kwarya, alokacinne suka isa k'ofar gida, cikin sand'a ta fito bataso yaganta dashi, saboda ta lura yafi tsanarsa da kowa amma ya zatayi bata da choice, kaman jira ake ta fito amotar ruwa yakece lokaci guda, ko godiya bata tsaya yi masa ba ta kwalwala zuwa gida, shikuma Adam banda ruwa ya balle wallahi sai ya isa ga motar ya zuba wa wanda ya kawota rashin mutumci, don duhun garij bai bari ya ga wayeba, sannan daga dan nesa da kofar gidan yayi parking ta opposite d'insu

Tana isa ga k'ofar gidan gabanta ya yanke yafadi, batayi tunanin zata ganshi awajeba kuma ga yanayin fushi dake kan fuskarsa, bai damu da ruwan dake jik'ashiba, ta rabeshi tayi cikin gidan don bataso yafara sauke fushinsa daga k'ofar gidan, cikin fushi ya d'oru abayanta zuwa falo, ita kuwa direct bedroom ta isa saboda jikewar da tayi, burinta d'aya ta ciresu tana kokarin daura towel ya isa bai yi wata-wataba ya sauke mata mari afuskarta, tsayawa tayi cak cike da tsoro mamaki hade da fargaba, hannunta dore kan kamatunta, abun Adam har yakai ya mareta to in ta tankashi tanaga rufeta da duka zaiyi, karkarwa kawai take tana ja da baya yana binta fuska d'auke da fushi, closet  ne ya tokareta anan ta durkushe ta fashe da kuka " Munafuka annami miya, wallahi kinyi asarar karatun ki, wai ke meye damuwarki da son fallasa kanki  ga wasu mazan" duk da kukan da take mai sautine bai hanata jin kalamansa kantaba " Wanne dan isakan ne ya ajiyeki amota?" yanzu idonsa har tsattsafo da hawaye yake  saboda b'acin rai, bata yi maganaba sai tayi kokarin gyara zaman towel din, tayi wuf ta shige toilet, tsayawa yayi jikin toilet d'in yana cewa "In banda rashin gaskiya mai yasa bazaki kirani nazo na dauke kiba,nagaji da irin wannan abun Wallahi yazama dole ki zaba Khairi" cikin kuka tace " Ai nayi kokarin kiranka taki shiga, kuma karka manta ruwa ke shirin zuwa don me zan tsaya, meye aciki don an rage min hanya ya kake so nayi" Haushi yaji ya bugi kofar " Karya kike dama u set-up this kinsawa ranki ku taho kuna tadi, saboda ki nuna masa kwalliyarki ko, yinin da kukayi tare baiishekiba" durkushewa tayi atoilet din ta cigaba da kuka, don kanshi ya gaji ya fita daga dakin yana bak'in rai

   K'ara kallonta yayi akaro na biyu, baccinta take hankali kwance, banda darajar cikin dake jikinta ba abunda zai hana ya sauk'e mata nauyinsa akanra yau, cike da jin haushi ya bubbuga mata kan pillow, cikin magagin bacci ta bud'e idonta yace "Jamila me kike nufine? Dama ciki ne ya had'ani dake ko me? Ba nan kike fama rokataba in kin karbo maganinki" yamutsa fuska tayi " Na shiga uku da gori da tada maganganu, koma meye ai dai kasan bani da lafiya ne" kallonta yayi cike da bacin rai yace " I dont care i need you right now" dafe kai tayi tace gaskiya nidai bazan yardaba, haka suka sha rikici in ya tabata ta botse ya tabs can ta tureshi karshe gudu tasa tabar masa d'akin, kwana yayi da ciwkn ciki dama yafi ssti yana fama dashi....

Da safe kuwa da ya fita school fuskarsa daure ba walwala, haka ya dinga fada cikin lecture hall kowa yakasa gane kansa, da yaji rashin murya ko motain da bai gamseshiba sai yace get out..

lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻

NAMIJIN KISHIWhere stories live. Discover now