EPISODE 30

819 51 16
                                        

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                          

loadιng...........✍🏻

*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*

© 2019

Jinjina ga masu comment da voting hak'ika kuna kara karfafamin gwuiwa. Nagode much luv😍

30

Tun da yafita daga gidan nasu yake b'acin rai, wane irin rashin Adalcine wannan ba'a bari ya fadi abubuwan da take masaba, amma shikenan yasan ko ba dad'e ko ba jima dole sugano alokacin ne zasu san bashi da laifi, kwata kwata baiyi nadama ba, abu d'ayane ya soki ransa shine rashin d'ansa da yayi, amma bakomi ai zai k'ara aure zai samu yara da yawa, shikad'ai ya koma gidan ak'ofar falon yaga jakarta da shatan wurin jinin nata sai da tausayinta ya sokeshi amma ya cije, ya shige daki ya watsa ruwa ya kwanta...

  Tashi tayi ta k'arasa inda yake yana kuka da sauri ya ja baya yana " Karki sake ki tab'ani don wallahi sai nayi k'asa-k'asa dake" take hawaye ya fara zubowa a idonta, ita ba jahila bace tagano wani abun tabbas Ahmad bak'aramin kariya gareshi ajikiba, karfin Addua da imani ne yasa Allah ya kawo dalilin da ya dawo hankalinsa, don tasan shid'in kamiline baya zina gashi Allah ya kawo dalilin da yasa bazai aikata ba, yana durkushen nan yana jin yanda zazzab'i yake shigarsa don lokaci d'aya yaji wani irin sanyi na shigarsa har rawar zazzab'i yake, dakyar ya tashi ya nufi toilet d'inta yayi wankan tsarki ya fito yayi sallah, akasan tiles sannan ya zube awurin, nauyin takaicin abunda ya aikata ke cin  k'irjinsa don haka numfashinsa ma fita yake dak'arfi, itama kokari tayi tayi yanda yayi ta, d'aukar bargo tayi ta rufa masa,lokacinne taga wayarsa na ta uban haske alamar kira na shigowa, ganin sunan namiji ajiki sai ta d'auka daga can b'angaren Umar yace "Oga ka rud'a hankalin uwargida fa, ina kashigane?" jikinta ne yayi sanyi tace " Gashi nan bashi da lafiya, amma kazo gidana" ta sanar masa address d'inta, agigice Umar ya taho zuciyarsa cike da wasi-wasi, kafin fitarsa yanayin da matarsa tagani kan fuskarshi sai da tayi mamaki, yana tuk'i kiran Jamila na shigo masa tana so taji ko yasamu information kan Ahmad shikuwa yak'i d'agawa, don baisan me zai ce mata ba...

K'arasowa yayi cikin bedroom d'in inda Ahmad ke zube ak'asan tiles, jin muryar Umar yasashi bud'e fuskarsa cikin k'arfin hali yace " Umar na cuci kaina, abunda banyiba ak'uruciyata ba shi na aikata" hawaye ya cigaba da zuba idonsa, gaban sane ya fad'i yace " Ahmad me ya kaika haka? " d'aure fuska yayi ya juya ga Bubly yace " Wallahi nasan halin abokina sai dai wani abun kika zuba masa ko asiri, ki fadamin gaskiya ko kuma nasa arufeki" hawayenta ta share tace " Wallahi ban mishi komiba, kuma maganar da ake yanzun ma hakan wallahi iyakar kiss ta shiga tsakaninmu" hayaniya ya cigaba da mata harda zaro belt zai zaneta, sai da Ahmad ya kamo shi yace " Gaskiya take gaya maka, ba itace sanadi ba rashin juriyane irin nawa da kuma taimakon Jamila, wallahi nayi regretting Auran ta" kan Umar ya kulle shi bai san asalin meke faruwa gidan Ahmad ba duk da yanda suke, bak'arami tashin hankali Ahmad ya shiga ba sai da suka dangana dashi asibiti, sai da takai ansa mashi oxygen don birkicewa yayi ,tun kafin asibiti Umar yayi niyyar Jamila Ahmad ya hanashi, shiyasa batasan me akeyiba tana can tana tanadar wulakancin da zata mashi,ga kishi ya turata akan dole yana tare da mace ne....

Da safe ya dawo normal sai dai kallo d'aya zaka masa kasan yana cikin damuwa, shi tulin zunubin daya d'auka ne ke damunsa, kaishi gida Umar yayi sannan ne suka sanar mata baida lafiya, bin Umar tayi da harara kafin ta maida idonta ga Ahmad "Gaskiya bakamin adalciba, ayanayin da nake ciki ka fice ka kwana awani wurin sannan k'arshe ace baka da lafiya, to meyasa Umar bai fad'a  minba tun jiya atleast nasan cewa You are safe" kallonta kawai yayi da ido ya shige toilet d'insa, kodaga yanayin da taganshi da mace ce mai nutsuwa ai yakamata ta adana korafinta, kana ganinsa kasan ba ciwone damuwarsa ba  akwai abu azuciyarsa, sai da ya fito daga ciki ya shirya duka tana zaune tana kumbure-kumbure, duk da baijin k'arfin jikinsa haka ya wuce kitchen don shan tea shima bawai don yana soba sai don yasamu yasha magani da wani abu acikinsa....

NAMIJIN KISHIDonde viven las historias. Descúbrelo ahora