EPISODE 37

897 51 7
                                    

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                          

loadιng...........✍🏻

*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*

© 2019

37

  Tunda suka nufi gida bawanda yake magana acikinsu, sai sheshshekar Khairi ke tashi,  su Muhsin kansu ya kulle gaba d'ayansu suna zaune acikin falo ne, sa'arsu d'aya Mama tana part din Abbansu, sai kaga yanda Adam ke kumbure-kumbure Safiyya ce tace " Don Allah Sis ki daina kukan nan, kar wani abu ya sameki na tabbata shima Ahmad bazai d'au abun da zafiba, tunda yasan kowane namiji zai iya hakan" yamutsa fuska tayi tace " Haba ya bazan tada hankalina ba mutumin nan yana mutumtani, kuma don ni yazo kofar gidannan ace yasamu wannan humiliatons d'in, gaban jama'a for godsake this is not fair" dafa kafad'arta tayi tace " Yeah i can feel your pain amma ki share hawayenki, mu fuskanci yanda za'a warware abun nan saboda abun idan ya cigaba gaskiya za'a iya samun matsala" still Adam bai magana ba sai ma rawa da jikinsa keyi na b'acin rai, cikin had'e rai Muhsin yace " Ke Khairi meyesa da girmanki zaki  ke tsayawa da saurayi awaje, koma wanne irin wulak'anci aka masa ai ke kika jawo masa, kuma ki adana hawayenki kukan ya isa haka" Adam cikin ranshi baya jin dad'in kukan da take amma he had no choice dole ya fito yamata zabu-zabu, don tasan he won't let her go dole takoma masa gida yace " Muhsin kaga yanda tamin jiya wai har tana ik'irarin bata sanniba, agaban wancan wawan take fad'in haka wai ni d'an maula nake bibiyarta" cije  lips Safiyya tayi saboda yanda Adam ya tak'ark'are yana magana duk gumi ke tsatssafo masa ga ramar da yayi duk yakoma wani kala sai yabata dariya da tausayi,  jan tsaki Muhsin yayi yace "Baki da hankali zakice bakisan shiba? Wanne irin hali kike so ki d'auka da ba nakiba, komi Adam yamiki yafi karfin ki dizgashi gaban wani har kice baki da alak'a dashi, ko ba aure Adam yafi k'arfin haka don ya isa dake, karki sake don wallahi ranki zai b'aci" cikin ranta take ayyanawa wato ita ake so aga laifi duk abunda yayi sai ta zuba masa ido ya hana ta farin ciki ko, tashi tayi ta sake fasa wani kukan mai murya ta na nuna kirjinta da yatsa tace " Wai shin ni ba zuciya ak'irjina ne?Da ake son tauyeni nace bana son alak'a dashi ya fita rayuwata!! Ya fita arayuwata!!! jikinta har rawa yake hawaye yana ambaliya a fuskarta , tashi Safiyya tayi zata ruk'ota ta goce tace " Ki barni na zubar da takaicin dake raina, wallahi banason ko ganins, ya daina shigewa lamurana in ba hakaba zan b'ace arayawarku ko na had'iye zuciya na huta" gaba d'ayansu kalamanta sun kad'asu, abun har ya kai haka awajanta? sun san tana da hak'uri kuma ko maida martanin da tayi bayan maganar Muhsin da mamaki, don kowa yasan tana da tsananin biyayya, daga fad'in haka ta juya da niyyar fita daga gidan, ba wanda ya iya yunk'urin hanata sai shi Adam da yake jin zafin kalamanta na bin zuciyarsa, ya tashi yana binta yana fad'in " Da baki sona sai dai ki dau wuka ki kasheni, inba hakaba wallahi bazan daina bibiyarkiba ke d'in tawace bawanda ya isa  ya aureki muddin ina numfashi" batason kalamansa don haka da gudu ta fice daga gate d'in gidan, agun ya durk'ushe yana haki don bugun zuciyarsa na ya k'aru da yawa lokaci d'aya yaji k'afarsa bazata iya d'aukar saba, yafi minti biyar a hakan kafin ya koma cikin gida  inda sukuma su Safiyya suka rasa me zasuce, azuciyoyinsu akwai tulin wasuwasi, gaba d'aya su biyun abun tausayine, don Adam yana cikin wani yanayi da kowaye yagani yasan yayi nadama ba abunda yakeso sai dawowar Khairi, ita kuma ayanayinta tana nuna batason sake rayuwa dashi in aka matsa mata nan ma matsala ne, yana shiga yaga tagumi a fuskar Safiyya ya samu ya kwanta akan kujera, cike da tausayi Muhsin yake kallonsa yace " Tashi kije ciki ki kawo masa abinci daga yanayinsa nasan baici komiba duk bakinsa abushe yake" tashi tayi ta nufi kitchen kafin ta dawo yake wa Adam magana " Ka kwantar da hankalinka nasan bawanda zai bi bayanta akan ta ki komawa gareka, kana bukatar nutsuwa karka sa wani ciwon ya kamaka" sai da ya ajiye numfashi yace " Bazaka ganeba irin kalaman da take su suke sage mun zuciya, naji tamkar bazata komaba jadda dawa take bata sona kallo  yanda take kuka, wallahi ina sonta bazan kara daga mata hankali ba, sontane yake sakani kishi naji sam bana son naga tana alak'a da kowa" daidai lokacin Safiyya ta shigo dauke da babban tray da tahado abinci da ruwa kai, ta ajiye da kalamai masu dad'i Muhsin ya samu yaci, ita kuma Safiyya shiga d'aki tayi ta shiga tunani, gaskiya tafara jin tausayin sa  gefe daya kuma bazata bi bayan a takurawa Khairi ba, sai bayan sallar magriba Mama ta shigo part d'in tagansu inda suka mata sallama sannan suka fito tare da Adam suna k'ara kwantar masa da hankali, yad'an ji sauk'i amma yana son yasan halin da take ciki....

NAMIJIN KISHIWhere stories live. Discover now