EPISODE 43

905 58 4
                                    

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                          

loadιng...........✍🏻

*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*

© 2019

43

Ranar da su Jamila suka koma sauk'i daya Ahmad ya samu shine batai k'ok'arin yin komiba, illa bak'ak'en maganganu wanda agunsa bai daukesu komiba, hatta baby Aslam yasan gidansu ba sauk'i don nono gagarar bashi tayi sai cikin dare da taga yana kuka yana neman shid'e mata, acikin daren ta lalubi number Samira ta gaya mata tasan wace ce wane mataki take ganin zasu d'auka? Alokacin mijinta ya farka ya daka matsa tsawa yace ta kashe ba shiri ta kashe wayar..

Jibine tariyar Khairi hakan yasa akaje har gida aka mata sabon jere tamkar na sabuwar amarya, shikansa Adam kwaskwarimar da yayiwa gidan tayi kyau sosai, sai rawar jiki yake. Da misalin k'arfe hud'u na yamma suka hallara gaban iyayen nasu inda suka musu nasiha mai tab'a zuciya, sun nunawa Adam illar fushi da zargi da tsananin kishi, itama sun mata nasiha akan k'ara kiyaye martabar Auranta, dama wasu abubuwan da suka shafi zamantakewa, daga bisani har k'walla sai da Adam ya share don bak'aramin shigarsa abun yayi ba, a ransa yake ayyanawa ba abunda zaisa ya maimaita kuskurensa na baya don shikad'ai yasan wahalar da yasha, ana gama musu ya durk'usa yayiwa su Abban Khairi godiya da Ummi, ita Khairi sai share hawaye take dabatasan na mene ne ba, suna tashi daga wurin dama magriba tayi shiga tayi toilet ta d'auro alwala bayan ta idar da sallah Ummi ta aiko Humaira k'iranta, bata wani b'ata lokaciba ta nufi d'akinta,  sabon darasi ta d'ora mata had'e da jan kunne, anan ne tace mata tabata mamaki da sun zuba mata ido haka zata cigaba da nuna k'inta ga Adam ko kara bazata iyayiwa Hajiya Hassu ba, sunkuyar da kanta tayi cikin  kunya don wallahi shaf kanta ya kulle, sosai ta mata nasiha  da k'arin dabarun gidan miji, sai da jikinta yayi sanyi sai kace lokacin ne take amarya, da dare Adam ya k'irata a waya ta d'aga yad'inga janta da hira tana Un da un'um, batason ta sake masa da wuri so take taja mutumcinta kosan gaba duk da tasan ya wani kuma tana da hope akan ya shiryu, yanda tad'inga gwada hak'urinsa akwanakin taga yana iya daurewa koda yaganta da wasu. Dama an jima ana mata gyaran jiki don haka tsaf take hatta skin d'inta shek'i take,  koda sukai waya da Umaima ce mata tayi nanda Sati zata zo musu hutu tace sai Allah ya kawota..

  Jamila tunda akai abun nan ta bud'en shika-shikan rashin mutumci , bata shara sai ta ga dama girki kuwa daidai cikinta take haka zaiji k'amshi ta hanashi, shikuwa a nasa b'angaren bai fasa ajiye mata komiba da duk wani hak'kinta, sau tari in ya zauna afalo ko d'aki yana hutawa kawai ta tsiri  k'ure volume d'in tv ta kamo channel d'in wak'a ta k'ure, haka zai yi kaman baya ji don yasan neman magana ne kurum, in yaga ranar bazai iya hak'ura da baccin ba sai ya fice ya bar mata gidan yaje gidan Umar, a bangaren soyayyarsa da Saleema sai muce sai shukra don k'ara mannewa suke da juna, a duk sanda Jamila ta k'ureshi da haukarta daya kira Saleema zaiji kwanciyar hankali

    Daga b'angaren gidansu Saleema kasancewarta mace diya tal awajan iyayenta bak'aramin shiri suke mataba, duk wasu kayan gyare-gyare an tanada don yimata, haka kayan d'aki ba'a magana don Alhaji Ibrahim Moddibo yana da kud'i bakad'anba, mahaifiyarta yar maidugurice Yagana an dad'e ana tsumin k'amshi don Saleema don haka jira ake tayi grad ta dawo a mata gyaranta balle da akaji gidan kishiya zata shiga.

   Khairi takoma gidanta da rakiyar Anty Asiya da matar Kawu bala, tunda suka tafi ta tashi ta zagaya gidan abunda taga yakamata ta gyara ta gyara shi, shikuwa Adam sai d'ari-d'arin fuskantar gidan yake saboda yaga kaman har yanzu bata sauko ba, su Ak sai zolayarsa suke suna cewa kar ya bada maza, a haka dai ya daure takwas da rabi ya shiga gidansa tare da parking, yana fitowa ya bud'e bayan motar ya fito da ledodin kayan ciye-ciyensa ya dan tattaro dauriya ya shiga falon bakinsa d'auke da sallama, tana can cikin bedroom d'inta fitowarta daga wanka kenan tana sanye da bathrob silver colour, amsawa tayi tare da zira hijab k'ato ta fito falo bata kalleshiba ta amshi kedodin tana furta sannu da zuwa, so yake ya had'a ido da ita amma tak'i bashi dama, takai  ledodin kitchen tare da dauko masa ruwa da  cup ta kawo masa, tayi shigewarta d'akinta tacigaba da shiryawa  sai da tad'au 30 minutes tana shafe-shafe daga kan creams zuwa oil perfumes, tuni  tad'au k'amshi koda can gwanar turarece balle yanzu an k'ara shiryo makaman kama miji, ta d'auko wani kayan bacci k'irar jumpsuit saidai  su iyakarsu gwuiwa ta maida hijab  d'in nata kai ta tada sallar shafa'i da Wutri, a can Adam shima yayi wanka yasa pyjamas cream colour ya nufi d'akin nata, sai ya tarar tana sallah cewa yayi " In kin idar kisameni a falo please"

NAMIJIN KISHIWhere stories live. Discover now