🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad *@jannahjay8*© 2019
49
Sai da tayi salla ta sake wanka ta shirya kanta cikin silver english gown tayi turban mai kyau, tana fitowa taga Aslam yana yawonshi a corridor da tsaiwarshi wadda batai k'arfiba yanayi yana fad'uwa, duk ya b'ata kayansa komawa tayi ta masa wankan dake lokuta da dama in ta daukoshi tamasa wanka wanda ta cire masa hadawa take da undies dinta ta wanke a washing machine dinta don haka akwai kayansa adakin, bata buk'atar zuwa balle yau taga matar akusa take, tasaka mashi ta hada masa tea ta bashi, bai jimaba yayi bacci tana zaune tana zikiri da counter taji shigowarsa lokacin ana kan kiran sallar Isha'i na farko, da hanzarinta ta sauka k'asa sai da ya shigo falo ta tareshi inda ya d'an saukar mata da nauyinsa ya furta wash da dariya afuskarsa tace " Sanne Hero yau duk an wahalar min dakai baka ga yanda ka komaba" lokacinne yaga hakimar zaune ya kalleta yace " Sweety ya k'arfin jikinki? Im sorry i was busy da rana shiyasa ban kara kiranki naji ya kike ba" dakyar ta amsa tace " Da sauki" wai don ba ranar ta bane sannu da zuwan ma sai taga daman yi, suna k'okarin hawa stairs da Saleema yake cewa " Ina jinki ya nakoma? " ta kwashe da dariya tace " Tab ai yanzu in ba nida maman Aslma ba bamai sayanka naira hamsin" kama baki yayi yace " Eyye lallai zan kamakine yarinya" ta dinga dariya tace " Zaka shiga toilet ka gani, duk shatan birone inaga akumatunka" ta had'a mashi ruwa yana shiga tana k'ok'arin fita ya ruk'ota ya sunkuya kan kafad'unta inda taji nauyinshi yace " please na gaji sosai fa dak'yar nake daga hannuna can you wash me up" zaro ido tayi tace " Sorry sir" ya dungure kanta yana dariya usually haka take masa in ranar tanso tanuna taji kunyarshi sai ta kirashi da sunan da suke fadamasa a school...
Su Sayyid sun samu aiki a Norhwest lecturing tunda dama dukansu sunyi masters ne kafin dawowarsu, an musu hanya duk da suna kan service ne sai yazamanto suna service a Northwest din, Soyayyar Hafiz da Umaima sai habaka take don su Alhaji Abdullahi sun je nema masa kuma har anyi alk'awari, jira ake tak'arashe karatunta ad'aura in yaso ta d'ora degree din ad'akinta, Khairi taji dadi ko bakomi Umaiman zata dawo kano atleast ta samu wani a yan uwan Umminta akusa.
Bangaren Khadija Alhamdulillah tayi amfani da shawarar kuma yanzu tana samun sauki, takan jure shima kuma yanzu ya fara sauyawa don in taga hadi mai amfani agroup daya danganci kayan naturar ko herbals takan musu, don yaka yanzu Alhamdulillah sai da takira Khairi ta mata godiya tace mata bakomi ai haka shine zumunci.
Yau Saleema ta shirya tarar Ahmad da maganar Jamila, tun safe take nuk'u-nuk'u tazauna ta auna ta rasa ta ina zata fara, yanzu haka yana gabatane yana cin fried egg da mint tea, ta k'urawa k'asa ido ya dan zungreta yace " Baby wai meke faruwa dakene yau? Duk kina ta tunani fadamin waye ya tab'a min ke?" ta nunashi da bakinta da ta turo yace " Ni? lallai i must punish myself ya za'ai na batawa ruhie rai my oxygen and water" sai tayi yar dariya tace " Ai daga yau in dai baka canzaba na daina kulaka ma, kuma ba ruwana munyi baran-baran" ta karasa da sigar da yara kanyi na shagwaba yace "Cewa zakiyi kinaso na koma mad man don in kika b'ata dani nabi ina naga haske" dariya tayi kawai yagama ci yanzu ta tashi ta kwashe komi, zuwa yayi ya wanke bakinsa kafin nan ita tadanyi chewing mentos bubble gum, zama yayi kan kujera dake suna falonta ya janyota yana cewa " Tell me im ready to apologize" sunkuyar da kanta tayi tana murza yatsansa na d'ayan hannunshi dake ajiye " Tace kayi hak'uri zan maka shishshigi tsakaninka da matarka, amma gani nayi wannan shine zaman tare, bazan so Allah ya kamaka da laifi ba kuma bazan ji dadi ka take hakkin taba don nima zan sawa raina wataran zakamin hakan ko fiye, kada kamata ba iya ci bane hakkinta kurum don me zaka daina had'a shimfida da ita? Duk girman laifin da tamaka kasan Allah bazai barkaba, domin zamanka take wazai dauke mata kewa?" ransa ne ya shiga baci kuma gefe daya yasan gaskiya ta fad'a amma ai batasan me ta masaba yace " Waya ce miki hakan, ni nace maki bani yi? " tace " Please dont pretend wallahi bakayi, infact nagane bakwa shiri baka damuwa da ita kwana biyu shes too silent and she seems lose ka duba lamarin nan, bai kamata ka biyeta ba komi ta maka kasan matsayinta a wurinka, don Allah ka shirya don naga alamun nadamar komene ta maka tunda gashi tana shiga damuwa akan watsar da ita da kayi" duk ta marairaice shiru yayi yana nazari sai kuma ya tashi tsaye, addini ne ya bawa miji damar k'auracewa matarsa in ta fara masa hakan na wani lokaci, amma bakomi shikansa ya lura Jamilan tayi sanyi don ko jiya sai da yaji tausayin ta ganin yanda ta zama ba kuzari ba wani falli, ita kuma Saleema ganin haka sai tayi tunanin ransa ne ya b'ace, take taji wani iri na shiga abunda ba ruwanka tace " Hero idan ranka ya b'aci don Allah ka yafemin" idonta har ya fara kawo k'walla, zuwa yayi ya zauna tare da had'ata da jikinsa " Ko d'aya bawai raina ne ya b'aciba, ina nazarine akan maganganun ki kuma insha Allah zan duba zan san me zanyi nan gaba" murmushi tayi tace " Yawwa nagode" kuka ne ya nemi k'wace mata da sauri ta ruga zuwa d'akinta ta fad'a gado tadinga kuka " Yau itace sai wata ta saka baki tsakanin ta da mijinta? Lallai ta yi kuskure tabar damarta don gashi tana zaune wata tafita matsayi da sanin shawo kan Ahmad, wanda ta rigata saninshi da komi akansa, ji yanda take masa kalami da ladabi, ashe shiyasa kowa yanzu adangi yasan Ahmad yafison Saleema sai dai in baka mallaki hankalinka ba" ranar tayi kuka tayi nadamar abunda take bata k'ara shiga tunani ba sai da ta k'ira Samira tana d'agawa tace " Kawa wannan kira haka da dare, gashi ina shirin zuwa wajan oga ne inaga sai gobe gaskiya mayi maganar dama ina son shigowa" bata jira amsarta ba ta kashe wayar, ashe itace sakarya takasa jure komi sabida son jikinta, ita kanta tasan tasha bak'antawa Ahmad yana jurewa don ba wadda batasan hana miji hakkinsa laifine mai girma, koda kuwa mutum baida ilmi addini sosai.. ..

YOU ARE READING
NAMIJIN KISHI
RomanceKhair gara nak'ara maimaita maki bake ba Aikin nan ke bari na tak'aita maki wallahi wallahi ban yarda dake da Dr Umar ba.... Cikin Kuka tace " Zargina kake? "Hawaye yana zuba a idonta... "Wallahi Ahmad sai kayi nadamar abunda kayi yau, zan tabbat...