EPISODE 13

832 45 7
                                        

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                          

loadιng...........✍🏻

*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*

© 2019

13

Wata uwar tsawa ya daka dasu kansu saida suka tsorata " Yace wanne irin abune hakan, wai meyasa idonki ke rufewane, bakya tunanin ko friends dinta ne su' zata sake magana yace "Wallahi kika sake kikayi magana ranki sai yayi masifar baci ki wuce mota kuma' tuni itakuma Salima tafara hawaye ta juya tabar wajan, d'an waigawa tayi taga Jamila ma ta nufi parking space d'in,  aikuwa tace bari kiga dai yau na rama bak'ar magana koda d'ayace ta juya zuwa inda taga Jamilan tayi inda motarsu take,  tana zuwa ta saki murmushi ta kalleta sama da k'asa sai ta kwashe da dariya kuma tace "Hmnn gaskiya 'yar uwa action d'inki yana burgeni saboda kin cancanci kike hargagin kishi akan mijinki idan akayi la'akari da zubinki da tarin nak'asu da kike dashi daga halitta har zuwa wayewa, gaskiya ki dage don nakyasa mijinki kuma tunda yamin zan bi duk hanyar daya dace don nasameshi kodan ma wazaiga galleliyar budurwa kamata yakasa amsa tayin soyayyar ta' cikin  bacin rai ta zaburo daga zaman da tayi cikin motar da niyyar cakumar Salima don yanda ranta ya taso jitake zata iya shak'eta har lahira, ja da baya Salima tayi alokacinne BG friend d'inta daya kawota amota ya hangota ya taho da sauri yazo "Subhanallah  meya faru kuma?' cikin masifa Jamila tace "Malam ka matsa naci kan uban yarinyar nan wallahi yau sai naga wanda ya isa agarinnan yahanani koya mata hankali' hak'uri ya fara bata tana kokarin sai ta cafko Salima, suna haka su Ahmad suka k'araso wurin ranshi bak'aramin b'aci yayiba, kuka kawai Salima tasaka tana buga k'afa cikin  muryar shagwaba da b'aci tace "BG ka k'yaleni wallahi matarnan ta dad'e tana cimin fuska wallahi darajarshi take ci' ganinshine yasa ta juya BG ya na bata baki suka nufi mota, bayan ya gaida Ahmad shima student ne, da kumfar  baki suka bar wajan wanda tsabar b'acin rai da Ahmad yashiga kasa magana yayi sai tunane tunane yake kan matakin dazai d'auka kanta , da alama ta rainashi tunda bai isa ya mata magana tabar abu ba.

Suna shiga ya nufi d'akinsa ya kwanta cikin kuka ta shigo d'akin "Wallahi bazan yardaba har yarinyar can ta isa ta wulak'antani kaji maganganun da tagayamin? Kodan kai kajamin tunda ka nuna takai kuyi soyayya tare' tashe yayi  da niyyar wanka mata mari amma sai ya rarumi wayarshi ya cillata jikin bango ta bada wata k'ara tare da fashewa, ya nunata da yatsa idonsa tuni sunyi ja yace "Wallahi kishiga hankalinki Jamila' jikinsa yana rawa jijiyar kanshi kuwa duk sun fito, bata tab'a ganinsa a irin wannan yanayin ba hakan yasa taja k'afarta ta tafi gabanta har dukan uku uku yake, amma wallahi zata saka k'afar wando daya da wannan yarinyar

KANO

Tun bayan cin abinci da sukayi ya fita sallar Magriba bai dawoba, sai da yayi Isha'i ya dawo, lokacin tana zaune tana kallon wani Indian series, bai damu da ya amsa mata sannu da zuwan da ta mishi ba ya wuce d'aki,sai da taga yayi  kaman 3 minutes da shiga d'akin sannan ta shiga, yana  kwance arigingine yayi nisa atunani ta k'arasa  inda yake tare da zama daga inda kanshi yake tace " Hearty meyake damunkane duk naga kayi wani iri? Ko wani  ne ya tab'amin kai' kallonta  yayi wanda yafi kala da harara yace "Pls ki fita kibani wuri  banason kalen yaudara' gabantane ya buga tace  "Yaudara kuma kaman ya?' sai  da yaja tsaki yace "Inaso kisan darajar aure, don aure bawasa bane kuma wallahi wallahi karkiga nabarki yin aiki kidauka zakije kiyita warewa kowanne kato bakinki, kiji tsoron Allah!! kiji tsoron Allah Khairi!!' yak'arasa fad'a yana ishara da yatsansa wani irin takeji  ak'irjinta, meya kawo wannan maganar ne? Dole akwai dalili kallonshi tayi tace "Insha Allah zan kare hakkin Aure, sai dai yanda kake maganganun nan meya faru ne?' Da yayi niyyar fad'a mata sai kuma yayi wani tunani na daban yace "Kawai dai na jadda damikine saboda inada labarai kala kala kan masu  aiki a asibiti, at times sukan yi cheating abokan  zamansu' bataji dad'in furucinnasa ba amma sai ta kanne tace "Hmnn lallai basawa kansu adalci ina tarbiyyar da aka bas? Kadaina kawo wannan tunanin akaina kasan yanda nake jinka araina kuwa, inaganin tamkar ba wani namiji kamarka balle asamu wanda zai d'au hankalina' yadanji dad'i sai dai da yaso ya tambayeta meye hadinta da wancan, sai ya d'an saki murmushi ta sunkuyo kan fuskarshi tare da rage muryarta kad'an tace "Wad'annan labaran ne suka birkitamin kai kenan?' ta fad'a tare da murmushi yace "Uhmmn kinsan bani da sauki kishi akanki'  dariya ta saki mai dan sauti da salo na jan hankali shikuma ya janyota sosai kan jikinshi yace " Yau bakimin welcome  kisses ba fa' D'an ware idonta tayi tare da had'e bakinsu tare, bayan wasu minutes tace " Me zan dafa makane something light' yace "A'a karki damu bari nafita asayo suya koya kikace' murmushi tayi tace "Duk yanda kace Hearty' Tashi yayi zaune tare da daukar jallabiyarshi da ya cire ya d'ora kan short najikinshi yafita, har yaje waje tace " Hearty da yoghurt na Habib ko Rufaida' cikin son zolaya yace " Wannan bakin naki da son kwadayiko?

Yana tafe yana tunanin abunda yagani "A'uzubillahi minash-shaid'aninrrajim' yayi ta maimaitawa don sai shaid'an ya maida masa da abinda ya faru don ya tunzurashi, da k'arfin Addu'a ya dawo normal har ya dawo gida suka ci tare sannan sukayi shirin kwanciya.

Bacci ya fara d'aukarta taji yana mata tafiyar tsutsa ak'afarta, tun tana daurewa har tafara gantsarewa tana dariya "Don Allah Hearty bacci fa' tafad'a da shagwaba "Aikin lada yafi wannan baccin ai, karki damu 20 minutes kawai zaki aramin' yafad'a yana lalubar bakinta

********          *******       ***
K'arfe biyu da rabi na dare yana kwance sai juye -juye yake yakasa runtsawa, tabbas yafara gajiya da halayen Jamila, shi bazaice ta k'ware afanni kula dashiba hakanan kuma ga taurin kai da rashin jin maganarsa, gefe d'aya ga zuba d'anyen aiki da zubar mutumci, yana takaicin abunda tayi masa a asibiti yanda yayi popular agarin dutse hardly wani abu ya k'etara awajan al'umma ace wani wanda yasanshi bai ganshiba, gashinan mutum sunfi uku suka kirashi kan abunda tayi, yanzu har maganar taje kunnan mahaifinsa, yakirashi ya tamabayeshi sai wata k'arya da yayi masa sannan ya kaucewa abun, ita kuwa mahaifiyar sa tana jiransa gobe yaje don bata yarda da k'anzon kuregen da yayi ba,  tashi yayi ya tallafi fuskarsa sannan ya maida kallonsa gefen gado, bata nan yasan kuma dama za'ayi hakan kalar hargagin da ya mata yasan dole ne taji tsoron zama ad'akin nasa. Yana shiga d'akinta yasameta tayi bacci akan chinese carfet dake bedroom d'in nata ko kayan jikinta bata cireba, yanayin fuskarta zai tabbatar maka tasha kuka bakad'anba,kallonta yayi fitinarta tayi yawa duk da yasan sone yasa kishin amma nata ya kauce hanya, saka mata hular bacci yayi sannan dazai fito ya kashe bulb da ta bari.

Nafila yazo yayi tayi har zuwa k'arfe uku da rabi sannan yad'an kishingida kafin lokacin Asuba.

F. U. D

"Kinga yanda idonki suka kumbura kuwa? Tab kalli mirror d'innan kigani' tafad'a tare da kwashewa da dariya, jan tsaki Furaira tayi tace "Nucy sai tunzurata kike kinsan dai wallahi abun da ciwo, ga duka ga tsinka jaka. ' Share kwallar da ta fito a idonta tayi tace "Kedai bari wallahi bawanda yake cimin kashi duniyar nan kamar matar can, ni bani da alak'a da mijinta amma ta takuramin thank god cikin week d'innan zamu gama exam nabar garin nan, darajarshi take ci da tuni na biya 'yan  iska sun gigitamin shegiya' Mik'a mata cup tayi da tea tace "Hakane ki rabu da ita saura nawa ma mubar garin, amma kidaina kukannan tun jiya  abun nan yafaru k'ila ita tana can hankalinta kwance' da hirar case d'in suka yini sunayi, su Furaira mak'otan su Salima ne ahostel dakinsu jere yake, suna mutumci sosai... Wannan kenan

Tana ji yana k'wankwasa mata k'ofa takasa motsi kanta ya mata nauyi bakad'an ba, sai 6 ta iya mik'ewa tayi sallar Asuba,  adaddafe tagama ta kwanta tana azkhar daga kwance, shima Ahmad yana dawo daga masallaci bai iya yin karatun dayake yiba ya kwanta da tunanin yanda zasu k'are da mahaifiyarsa, ahakan bacci ya saceshi asannan yasamu nutsatsen bacci...

lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻

NAMIJIN KISHIWhere stories live. Discover now