🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*© 2019
15
Da sallama ya shiga falon lokacin k'arfe shida saura, cikin yauki ta k'araso gareshi tare da mashi sannu da zuwa ta karbi ledar hannunshi, amsawa yayi yana binta da kallo,ta nufi kitchen ta kawo masa ruwa da lemo ta ajiye kan centre table, yana cikin shan ruwan tace masa "Wanka zaka fara ko kuwa abinci' Bai daure fuskaba hakanan kuma ba fara'a yake ba yace "Sai na dawo daga sallar magriba sannan zan zauna cin abincin' Gani yayi ta shiga dakinsa da alama yau ya samu arzikin had'a ruwan wanka, dan murmushi yayi ya furta ahankali Hajiya Jamila ta Ahmad, shima ya d'oru abayanta zuwa d'akin, koda ya fito daga wanka ta fito masa da moroccon jallabiya ta jiye masa duk abunda yake buk'ata..... Ashe dai Jamila ana sane ake watsar da miji.
Ta tashi yanzu ba zazzabi ajikinta sai kanta dayake dan ciwo kad'an, kuma jikinta ba k'arfi baya nan ga fita masallaci, a daddafe ta isa toilet tayi alwala sannan ta dawo ta tada sallah, sanin ya barota batajin dad'ine yasa ya wuce wani eatry ya masu order farfesun kayan ciki da friedspaghetti sannan ya sayo fruits da yoghurt, yana shigowa yaga bata d'aki nufar kitchen yayi yaga ta d'ora tukunya kan wuta, da sauri ya k'arasa kusada ita ya rik'e hannunta "Me zakiyi ke da baki da lafiya? Ko wani abu kikeson ci?' Jijjiga kanta tayi tace "A'a abinci da zan dafa mana nasan kana jin yunwa' wani tausayintane ya kamashi ya rike chicks dinta yace "A'a basai kin wahalar min dakankiba, na sayo mana abinci please karki sake wani abun, ok?' ya daukota ya dawo da ita falo ya ajiyeta kan L shape couch dake falon yasa k'aton pillow ya dan kishingida ta, ya koma kitchen ya yanko fruits d'in sanin k'aunarta ga banna and pineapple sai yasakosu da yawa da folk, ya zauna yake bata tana ci ahankali, sai da yaga tasha daya sannan ya dauko abinci tace sai anjima zataci, bai tursasa mata ba yasan zatacin, ya shanye sauran fruit na bowl d'in kana ya fita zuwa sallar Isha'i...
Mamakin Jamila Ahmad kawai yake sai nan nan take dashi, shikuwa ya kyaleta yaga gudun ruwanta yana dawowa daga sallar Isha'i ya tarar harta kwanta ad'akinsa cikin night wears na riga da wando 3-qtr, kwanciya yayi ya na d'an danne danne awayarsa, kawai sai jin mutum yayi abayansa an zira hannu ta cikinsa ta rungumeshi dake kwanciyar gefe d'aya yayi, cikin sanyin murya tafara bashi hak'uri da alk'awarin ta daina sharrin zuciyane, bai juyoba yace mata shikenan ya hak'ura, bata dai sakeshiba tadinga jansa da hira tun baya warewa har yadan sake mata kad'an, ganin haka yasa tayi ta seducing d'inshi har saida ya fara romancing d'inta suka nufi wata hanya tadaban..
Tun d'azu yake lallashinta akan tayarda taci abincin tak'i, k'ara yamutsa fuskarta tayi tace " Wallahi banjin cin komine ko sphagettin balle wancan ta nunashi farfesun da yatsa, kawai ka k'ara bani banana shi zan kuma ci' shafa fuskarta yayi na wasu seconds sannan yace "A'a yakamata kici wani abun kuma, kinga kar yunwa ta lahantaki fa' saboda yadage yasa ta bud'e bakinta yadinga bata farfesun kan dole lomanta na biyar ta tureshi ta nufi toilet tun akofarshi aman ya k'wace mata ta dingayinshi ba sauk'i, yana rik'e da ita ta baya, sai da tagama yajata zuwa ciki ya wanke mata bakinta da fuskarta, yana ta jera mata sannu, tundaga wannan kaman an bud'e wa amaine kafin safiya sau uku tana k'ara yin aman gashi bawani abun kirki acikinta, gaba d'aya ta galabaita. Da safe ya nufi da ita asibiti aka buk'aci yimata test, sai sannu yake mata wasu sun san ta tunda staff din asibitinne, ba b'ata lokaci aka fara musu komi amutumce
Sakamakon daya gani ne yasa ya k'ura mata ido sai dai bai mata maganaba sai smiling yake, kafin nan suka nufi mota sai da ya bud'e mata k'ofa yasan ta shiga sannan ya rufe tare da cemata zai dawo tabashi 5 minutes, yakoma gun likita aka bashi shawarwari daya danganci masu ciki, sannan ya dawo yana driving d'ayan hannunshi ya rike nata, fuskarsa kaman gonar audiga, duk ya cikata da mamaki ita bai fad'a mata komiba, da suka je gida hanata taka k'afarta yayi ya kaita d'aki, sai da suka gama nutsuwa sannan ya fad'a mata, wani irin abu takeji na shiga ranta sai hawayen farin ciki tanayi tana hawaye tare da k'amkame hannunsa...
BAYAN KWANA UKU
Kwance yake yana d'an danne danne awayarshi gefe kuma Jamila ke tsintar wake aplate, yau ogan yace shinkafa da wake yakeson ci jefi-jefi suna hira, gyara muryarta tayi tace "Myone ya maganar kud'in bikin nan kuwa kaga abun sai k'ara kusontowa yake' tashi yayi yazauna yace "Eh ina sane dashi anjima umar zai kawomin kud'in dake ya shiga bank yau' cikin jin dad'i tace " Allah yasaka' yace "Ameen'
Aikuwa da yamma saiga kud'i an kawo masa ya d'auki 60k ya bata, ran Jamila k'al tunda harda k'ari yamata mai neman 50 yasamu 60,tasan zata samu damar yin bikinta cikin fantamawa, cikin kwanakin yasamu nutsuwa agidan nasa har ya fara d'an murmurewa.
Bak'aramar kulawa Khairi take samuba daga bangaren Adam harma da familynsu, adalilin haka har gida iyayen sai da sukazo wanda shine karo na farko bayan kawota da sukazo, ranar bak'aramin farin ciki tayiba, dake sun taho da kanwarta Humaira nazaman placement zatake tayata aiki agidan, kuma tasamu sauki sai abunda baza'a rasaba irin na ciki, don haka takoma aikinta, shikuma oga Adam yana danne zuciyarsa naganin bai daga mata hankaliba, don yaji cewar damuwa na iya zubar dashi musamman yanzu dayake k'arami.
Tana zaune kan mirror stool tana shafa powder afuskarta, ya shigo d'akin ta mudubi ta k'are mishi kallo sai ta tub'ure fuska kaman zatayi kuka, sanin dalilin dayasa tayi hakan yasa ya saki dariya mai sauti yace " Sai hak'uri naje wajan an rufe nikuma sanin nawajan kikeso shiyasa ban sayo makiba' mik'ewa tsaye tayi tana gyara zaman towel din jikin nata daya fara mata kad'an saboda fara cikar da ciki yasata ta fara buga kafarta ahankali da sigar shawagwaba tace "Kana shigowa naga ba leda nasan baka sayomin ba, kuma yau bamai bacci agidan Allah' tare da kirkirar kukan shagwaba ganin yazauna yana mata dariyane yasa ta cillamashi tube d'in lipgloss da tashafa, ya cafeshi da hannunsa kara daukar wani tube tayi ta cilla mashi sannan yace " Yi hak'uri Babyluv nasayo nasakashi a fridge ne ganin kina wanka saboda kar ya fara narkewa okhh?' ya k'arasa tare da jan hancinta da d'an k'arfi sai da tayi kara ta biyoshi shikuma ya gudu ya nufi falo, dole ta koma don saka kayanta...
Gidan bikin cike yake da mutane kasancewar gidan mai girmane, daga cikin karamin falo kana iya hango yan mata sunfi yawa ciki saboda amaryar ma naciki sai hira ake jefi-jefi, wayartace tayi k'ara ganin sunan angone yayi appearing kan screen dinta ta mike tare da fita don tasamu daman dagawa, yan matane su biyar suke hira akan maza lumsy ta kalli faty tace "Wallahi in kinsan yanda malam Ahmad ke burgeni har jinake inama yazamo mijina' wani irin zafine ya taso azuciyar Jamila amma sai ta kanne tanaso taji waye wanda ake maganarsa, itama Fatyn sai ta kalleta tace " Ai bake kad'ai ba mata dayawa acikin department suna sonsa, gashi ance matarsa gwanar kishine kodan banga laifintaba in akayi la'akari da had'uwar mijin nata' Tagefensu ce ta cafe tace "Wallahi da Dr Ahamd Jahun zai mikomin tayin soyayyarsa da gudu zan amsa ba ruwana da wani kishi irin na matarsa' wani irin zafi take ji zuciyarta nayi ta ture hannun samira dake cinyarta suna hira ta fara takowa zuwa kan kujerar da yan matan ke zaune tana zaro ido ga gumi yana yankowa daga fuskarta....
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻

YOU ARE READING
NAMIJIN KISHI
RomanceKhair gara nak'ara maimaita maki bake ba Aikin nan ke bari na tak'aita maki wallahi wallahi ban yarda dake da Dr Umar ba.... Cikin Kuka tace " Zargina kake? "Hawaye yana zuba a idonta... "Wallahi Ahmad sai kayi nadamar abunda kayi yau, zan tabbat...