EPISODE 8

1K 63 0
                                    

*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*

© 2019

08

Gidan  yayi tsit daga ita saishi,  kaman yanda kowacce budurwa akan sameta da fargabar irin wannan daren to haka yakasance ga Khairi,  shikuwa Adam da za'a bud'e zuciyarsa da tabbas za'a tabbatar bai taba tsintar farinciki ba irin na wannan lokaci, yau Khairi tazama tasa, kaman yanda Addini ya tanadar mana haka sukayi sallah sannan ya dafa kanta ya nema musu albarka Aure da neman tsari na sharri, lokacinne kuma idon Khairi ya k'ara tsuru-tsuru, shikuwa yagano har wani 'yar karkarwa take sai danne dariya yake, cikin salon son sata ta ware yace mata "kalleni Babyluv ko nacansa kamane na koma zombie? Na lura dake duka yau bakyason kallon fuskata' uhunm kawai ta iya cewa amma ba baki, dama already tayi wanka tasa kayan bacci manya duk anata salon zata rufe masa k'ofa kuma gashi ya rutsata, shiyasa yanzun take ganin bata da wata madafa sai dai ta mik'a wuya, fita yayi zuwa waje mintina kad'an ya dawo da containers da leda ahannunshi, dak'yar ta iya cin naman wanda har kwalla sai da ta share kan ya tilas ta mata, yanayi yana sako wasa amagana don ta ware, fita yayi zuwa dakinshi yayi brush sai da yadau lokaci yadawo wanda yana sane da hakan, kaman yanda ya zata hakanne tafaru, takwanta ta rufa da bargo taji shigowar shi sai tayi kaman tayi nisa abacci, daukarta yayi gaba d'aya ya nufi bedroom d'insa da ita, har yanajin bugun zuciyarta saboda tsoron da taji, zuwa dakinsa dayayi da ita shiya koya mata darasin da ba'a ganewa har sai anshiga ajin, sai da yafara tura yan aike kaman yanda manzo ya koyar (romancing/wasanni) aranar yayi nasarar fara karbar budurcinta cikin hanya maisauk'i da salo, bai gwada mata k'arfiba, duk da haka kuka tayi bana wasa ba shikuwa dayasan shiya kar zomon dole yayi ta lallashi da saka mata albarka, wani matsayi da so da kishintane ya darsu aransa.

Washegari da tsananin kunyarsa Khairi ta tashi, ita tun cire mata kaya dayayi tafada tunanin yanzu Ya Adam da tasanine ke lalubarta jiki, takasa koda kallon kafarshine balle asa rai da fuska, ga canjin jiki da takeji jitake ko'ina namata ciwo, hatta idonta ya canza dama ga saurin kuka balle kuma an tab'ata,tana zaune gaban mirror tayi kwalliya da wani rantsattsen voil maroon da milk flowers and black bak'aramin kyau tayiba, sai dan sauran kumburin  idon takasa fita palour sai takai bakin kofa sai ta dawo ga yunwa na dibanta. Shiru-shiru baiji fitowarta ba ya nufi d'akin tana jin shigowarsa tayi sauri ta juya bayanta, yar dariya yayi mai sauti kafin ya rungumeta ta baya yana shakar kamshin jikinta, cak tayi inda gaba d'aya wani kuzari nata ya tsaya, ganin taki juyowa yasa ya fara sinsinar wuyarta tare da bata kananun pecks masu fita da iska iska da sigar kashe jiki, aikuwa yayi nasarar hakan dan tuni taji tsaiwa na gagararta, ganin ta gama sukurkucewa ne yasashi fashewa da dariya, yace "Babyluv duk kunyane yahanaki fitowa kikeson wahalarmin da cikinki da yunwa"ya k'arasa fadar maganar tare da shafo cikinta ta cikin riga, kaman k'asa ta tsage ta shige haka takeji, dakyar ta iya cewa "Yanzu nagama shiryawa' juyo da ita yayi sukai facing juna yace "Ok, to mutafi don tun d'azu aka kawomana breakfast' cikin sarkewar fuska tace "To kayi gaba gani nan zan zo' Yace "Nope gaskiya tare zamu tafi' ita kuwa Khairi duk nauyi takeji karyaga yanda skirt din yamata don bakaramin fitarda shape nata yayiba, ganin zata cigaba da jayayya dashine yasa ya sungumeta tana mutsu mutsu yayi dinning da ita, ranar dai dak'yar idan taci abincin kirki saboda kunya...

F. U. D

"Umar inaga dai zaifi kyau yarinyar takawo details d'inta, saboda nakasa ganin gyaranta na level 3 d'in, kace tazo tasameni a office d'ina gobe' daga can bangaren Umar ya amsa da "Ok to Shikenan zansa ayi hakan, don damuwata shine wallahi so muke tasamu ashiga da ita camp batch A d'innan, da sunfito za'ayi Auranta' Yace "Tazo da exam card nata, kodan ta taho da komi nata it would be okay Insha Allah, ku kwantar da hankalinku' Bayan yagama wayar yacigaba da tsara questions da yakeyi a system, cikinshi yaji na k'ugin yunwa, cikin takaici yaja tsaki yanaga gara ya nemo wani student d'in amashi takeaway acafeteria, cikin satinnan kullum da yunwa yake fita, yasan gulmar dalibai kar su shaida fuskarshi ahakan suke cewa yanada aurenshi yana yawo cin abincin titi, fitowa yayi daga office d'insa ya nufi na Dr Umar yana shiga yaga Dr ya tak'arkare yana zuba loman chips dayaji sauce acikin katon flask da maza hudu sa iyaci harda wani bread agefe da kayi toasting dawani abu, k'amshinsane yasa yaji kwadayin ci, k'arasowa yayi yace "kai kuma ina kasamu wannan, sai had'a zufa kake nasan kuma madam batanan' murmushi yayi yace kaima kazo kayi joining kafin kaji wa yayi, ganin dayawa yasa Dr Ahamd gyara hannun riga suka d'ora, harda teaflask da 2 cups cikin basket agefe da plates, tsaban yunwane yahana Dr Umar  rufe flask din amma aplate yakeci, sunyi nisa aci Dr Ahmad ya tashi ya had'a tea tare da daukan break din ashe wani hadine ciki na kwai da baked beans akayi toasting, sai da yayi nak sannan sukai parking kayan gefe, gaskiya abincin yayi dad'i don shikansa chips d'in saida aka  mashi hadi na kechup da carbagge aka hadesu jikinshi chips din. Kallon Umar yayi yace "Wane restaurant kasayo wannan?' murmushi yayi yace "Daga hostel ya fito wannan da kake gani, ina wata yarinya danace maka d'iyar cousin dinace itace ta hadomin saboda tasan Sadiya batanan' yamutsa fuska Ahmad yayi yace "Student ce ta hado wannan kayan uhunmm har naji kunya, inajin kana fad'ar ta har yau bantaba ganintaba' yace "Eh tana nan kasan inada relatives dayawa anan maybe kataba ganina da ita amma bakasan ita bace' sosai suka yabawa niece d'in tashi, koda Ahmad yakoma gida bai damu da yasamu abinciba alokacin snacks daya saya su yaci da lemo.

Cikin lumshe ido da murya da tayi k'asa k'asa cikin yanayin jin bacci tace "Yawwa nan haka baka tab'a wurin' ta nuna gefen hagu na kanta, shikuma yace " Ok nan baisan anayiba kenan' yana yar dariya yana sosa mata gashinta gaba d'aya wani bacci bacci takeji, tana k'ara bararrajewa kan cinyartashi, bacci ya fara d'ibanta sai jitayi da salon tafiyar tsutsa yana wucewa zuwa k'irjinta, tana dan murmushi take tare wa da hannuta tana sakin sound "u'unmm plssss, karka fara' sunkuyo da kanshi yayi zuwa kunnanta yace " saboda me babyluv' cikin rad'a da wani salo kafin ya dawo saitin bakinta ya dora da kissing dinta...

Zaman lapiya ake gidansu Khairi bak'aramin kulawa da soyayya take samu daga wajan Adam ba, gaba d'ayansu sun samu nutsuwa, hakan yasa ta tabbatar bak'aramin so yake mata shiyasa kishinsa yake dayawa kanta, abokansa sunzo inda tamusu abinci mai rai da lafiya haka yasata ta zumbulo k'aton hijab suka gaggaisa.

Safiyya na tayata girki suna hira dake yau tazo mata yini don tuni Adam yakoma bakin aiki, cikin jin dad'i safiyya ke fad'awa Khairi yanda alak'arsu ke tafiya da Ya Muhsin, inkaga yanda Khairi ke fara'a kaman an mata bushara tace "Gaskiya naji dad'i zanso ace nanda wasu months ayi aurenku wallahi, kinga shikenan still jikokin su Abba zasu tashi kai ahad'e' itama Safiyya cikin nuna gamsuwa tace "Kwarai kuwa kinga  da ace mazan sun dauko wasu matan daban suzo su raba mana kan zuri'a'

Sun gama shirya komi "Sopie shiga wanka mana, nima bari nashiga na can d'akin' Safiyya kuwa d'aukar veil d'inta tayi tace "Ina ai yanzu zan kama hanya natafi banison mijinki yazo yasameni ku kafurtamin ido da fitsara, don ban manta last zuwa da nayi yanda yake ta janki jikinshi agabana ku a nema kumanta ina nan' kama baki Khairi tayi tace "Au shedar da kika mana kenan? Zakiyi auranne muga ke yazakiyi k'ila sai kin hana zuwa gidanki saboda cakumar miji' dak'yar tasamu tasata tayi wanka ta shirya, kafinnan tasaka abinci da snacks wasu cikin warmer akai gidansu danasu Adam d'in, suna cikin hira sukaji k'arar motarshi, yana shigowa ta tafi ta tarb'eshi ya rik'ota ta gefenshi d'aya tare da kama bakinshi, da hanzari ta gudu d'aki sai lokacin yasan ba ita kad'ai bace, ya kalleta bayan ta bashi ruwa yasha yace "wace ta gudu d'aki? 'Tace "sophie ce' yar dariya yayi yace "maganin masu zuwa tsurku gidan amare sukai yamma' naushin wasa ta mashi a kwanji tace " Haba nice na rik'eta fa kaga sai ka mayarta anjima kad'an' d'an matsa lips dinta yayi yace "Tunda kin sayamin rigima shikenan naji zan maidata, banda kece kikace da sai dai takoma dakanta meya kaita kaiwa irin time d'innan magriba fa kawai don ahana mutane sakewa ko' yak'arasa fad'a tare da shafar lips d'inta...

Yana kwance bayajin dad'in jikinsa duk da ya lura da yamakara amma yakasa tashi, wayarsace tayi k'ara kafin ya sauko daga gafo Jamila tashigo ta d'auka mistakenly ta tab'a screen ta daga taji muryar mace "salamu alaikum, ina kwana? ' saka wayar tayi handsfree ta mik'a masa wayar tare da kafeshi da ido

Firdausi S Ahmad

NAMIJIN KISHIWhere stories live. Discover now