EPISODE 28

852 50 13
                                        

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                          

loadιng...........✍🏻

*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*

© 2019

28

Sai da yagama lecture d'inshi sannan ne ya koma office d'insa ya dasa tunanin yanda zai shawo kan matsalarsa, sukuwa d'aliban daya dauka sai mamaki abun suke wasu suce kila matarshi ta kunnoshi, wasu suce babu ce tasa shi hakan, shikuwa anasa b'angaren kansa ne ya kama ciwo ko haduwa da Umar baiyiba ya koma gida, bai damu da ganin taba kawai direct d'akinsa ya wuce, wallahi banda Jamila nada juna biyu ba abunda zai hanashi kwata da k'arfi, amma bakomi inta k'ureshi zai bata mamaki.

Khairi kam kwanan bakin ciki tayi, masifar Adam ta isheta abun sai cinta yake azuciya, to wazata fad'awa k'awarta kanwarsa ce sannan iyayensu komi daya suke, karo na farko arayuwarta da tasan ta kwana tana nafilfili in tayi sallah sai ta huta ta k'ara d'orawa, b'arawon baccine ya saceta kan sallaya sai da tamakara a sallar asuba, tana gama sallar Asuba ta shiga ruwan zafi tayi wanka, shaf-shaf ta had'a breakfast ta ajiye duka lokacin bakwai da kwata tayi, ta sabi jakarta tayi Asibiti, don ba fashi tunda meye ya rage ya  zabga wa fuskarta mutumcinta mari, yanzu yazama bata da saura gara ta cigaba da chasing dream d'inta she already lose Adam, shima dake kwana yayi kishi na Addabarsa shiyasa ya makara, bai fitoba sai bakawai da rabi da minti hudu yana fitowa ga komi ta ajiye amma bata gidan, wani mahaukacin haushintane ya taso masa, wato tayi laifi amma ko ta tsaya taji makomarta ta k'ara tafiyarta asibiti meaning she dont care, cije lips d'insa yayi tare da buga hannun shi kan dinning table d'in, ko shakka baya yi k'arfin alak'arta dasu Dr Kibiya ke ingizata ga son Asibiti, wallahi aka cigaba da haka sai yayi k'arar su, bai iya cin abincin ba sai zama da yayi yana cin alwashin wulk'ancin da zai cigaba da karta mata har sai ta ajiye aikinta infact sai ya mata kulle don zai hanata fitane  cikin  sumbatu yake fad'in " Khairi tawace nikad'ai ba'ayita don kowaba sai ni Adam, dole na katangeki Khairi wallahi kika sake na rabaki da aiki fita sai ta gagareki, ni kadai nake da ikon kallon ki fiye da sau daya amma kash su Abba sun jamin kina yini cikin wasu k'atulan-mak'atulan"

Duka yau a Lab yazama rabin hirarsu kan jiyane, cikin farin ciki ake komi hakan kuwa bak'aramin taimaka wa damuwarta yayiba, duk da jefi-jefi takan shiga d'an tunani, bayan sun ragu kowa ya kama gabanshi, lokacin ne ta fito daga wajen staff ta tsiri waya da 'yan uwanta musamman anties d'inta don wasu basu whatsapp irin sune zakaga ba'a fiya gaisawa ba sosai, magana take da Anty Murja sai kakarta dukansu na bangaren uwane, yan Jahun ne suna mata korafin aiki ya hanata zumunci, tafi awa  d'aya awaje tana gaishe-gaishe, sai da tagama takoma ko minti biyu batayiba kiran oga ya shigo, k'in dagawa tayi bata shirya karbar shoutings dinsa a asibiti ba, shikuwa Adam ganin ya mata 3miss calls batai picking bane yasashi sending mata text " Khair ya miki kyau, ni zan kiraki kik'i dagawa bayan tulin laifin da kikai ko? To ko'ina kike ina son ganinki yanzu agida, don kin fita bada izini naba" sai da ta maimaita text d'in sau uku, ta ajiye wayarta cike da damuwa kanta har ciwo yake, amma bata tashi ba sai da lokacin yayi, shikuwa yana can ya cika fam don ko office bai jeba knowing ya bata order ta dawo, tana shigowa ta ganshi gabanta ya fad'i seems like ya zame mata abun tsoro ko ganinsa tayi ji take taga tashin hankalinta don sai ya k'irkiri abu, tun daga yanayin hararar da yake mata tasan akwai tsiya, amma tasawa ranta yau ko kasheta zaiyi sai dai ya kasheta, sunkuyar da kanta tayi ta wuce kujerar da yake kai zata nufi bedroom d'inta bai jira komiba saboda tunzura ya tashi ya kwad'a mata maruka aduka side na chicks d'inta, wata iriyar tsanarsa ce ta shigeta alokaci guda ji take bata taba nadamar abu ba arayuwarta irin son Adam da auransa, bai tsaya daga nan ba ya fincikota ya mik'ar da ita don saida ta fad'i daya mareta, ya fara zuba mata zafafan kalamai masu dawwama arai " Lallai kin tabbatar mun Dr yasha gabana, in banda kin raina ni kiyimin laifi wani shege ya kawoki k'ofar gida, amma ki iya tsallake  gidana batare da umarni naba ki tafi wajan aiki saboda kinsan zaki ganshi, ohhoo wato ya rud'aki jiya ko? Khairi wallahi ni kad'ai nake da mallakin ki tunda kikai involving wani sai nasaki nadama" wani irin  zugi zuciyarta take yau ko d'igon hawaye babu afuskarta sai kallon tsana da ta kureshi dashi, bai damu da rashin maganar ta taba yace"Khair gara nak'ara maimaita maki bake ba Aikin nan ke bari na tak'aita maki wallahi wallahi ban yarda dake da Dr Umar ba.... Cikin Kuka tace " Zargina kake? " don yanzu hawaye ya fara zuba a idonta " Oh zargi ne ma? Karki nemi raina min hankali, nima dan zamani ne kamarku, kalleni Khairi meya fini dashi?" yasan bazata amsa mishiba " mena rageki dashi kin daina aikin nan, matan da sai sufi wata uku basu taka k'ofar gidaba amma ke kullum bisa titi, kina nunawa duniya ni'imar da Allah ya miki, look Khairi i had enough of this shit bazan k'araba, dole kidaina zuwa aiki ehe, rashin bin umarni na kuma bazai zame miki Alkhairi ba,  im warning you karki ga munada  alak'a wallahi bazata yi miki kyauba, mark my words" k'ura mishi ido tayi ya fuzgi car keys dinshi a dinning ya fice ya barta da tulin takaici...

NAMIJIN KISHIDonde viven las historias. Descúbrelo ahora