EPISODE 22....Career issues

912 48 8
                                    

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                          

loadιng...........✍🏻

*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*

© 2019

  Wannan shafin na masoya Namijin kishine dake Watsapp ako'ina suke... 😍

22

Kusan zamu iya  cewa Adam yafi farin ciki da wannan cikin akan na farko, har Addu'a yake Allah kar yasa yayi wani abu da zai kawo musu cikas akan wannan cikin, yana k'okarin danne abubuwa dayawa  koda zai ga Khairi da wasu Cousin dinshi ko nata yana d'an dannewa, don tabbas haushine baya fasa ji koya yaga tana fara'a da wani namiji. D'aura d'ankwalinta take akan dogwar rigar cotton material dake jikinta sannan ta d'auko veil d'inta ta d'ora akai, ta juya ta kalleshi tace "Nashirya" inda idonsa k'yam akan kugunta daya k'ara fad'i yayi shiru kaman baiji me tace ba, sai da tak'ara nanatawa ya kalleta yace " Gaskiya inaga yau bazaki aikin nan ba" cike da mamaki  tace " hahh amma dai wasa kake yi ko?" don ita takawo irin  zolayar nan ne na mata da miji, d'aure fuskarsa yayi yace "Yace ko kusa da gaske nake,  wallahi banso naga k'afarki ta taka k'ofar gidan nan" ya tashi tsaye ya juya zai bar d'akin, take taji ranta ya b'aci har hawaye ya fara suntiri afuskarta " Don Allah karka min haka mana, kaga last month fa nayi fashi akan bikin Khadija, yanzu kuma wane excuse zan bayar, kadad'e da sanin inason kiyaye halak d'ina" a zafafe ya juyo yace " Nidai nace yau bazaki fita ba matuk'ar nine mijinki kuma na isa dake" yanzu  kam ta tabbatar da gaske yake ba da wasa ba don haka ta zauna akan gado, ranta na suya ita takan rasa gane kan Adam lafiya lou zaka ganshi yanzu amma in ya birkice sai ka rantse abu aka mashi.

Tafiya yake yana sak'e- sak'e aransa " Dama ni sam aikin nan baya gabana, bazata gane bane tunda dana yarda bawai ina nufin zan kyale bane, dolene naita hanata har takai ai mata query, hmm dani  suke zancen" sosai yake  jin d'adi yau tunda yasan ya  hanata fita, don haka ana tashi daga office gidan Sabeer ya fara zuwa suka d'an taba hirar sannan ya nufi nasa gidan, koda yaje an fara  kiran sallah don haka ya fara shiga masallaci sannan ya dawo, yayi tunanin zaiga tana fushi amma sai ta tarbeshi as in komai normal, ta gabatar mishi da abinci yana ci yana bin ta da kallo cikin bumpshort da armless top, ta jima bata tsuke mishi kamar hakaba don haka ya gigice sai da yayi romancing d'inta kafin Isha'i..

DUTSE

A lalace wajan masu magani uku su Jamila sukaje kowanne da nasa salon tsarin amma shiru kake ji, kwana biyu saboda  tasaka  damuwar aranta har rama tayi, yanzu haka tana zaune akan kujera suna maida zance da Samira tana k'ara nuna mata dole ta bazama neman haihuwa koda sanin Ahmad ko babu, don shi baida matsala dole taga yana calming d'inta da sunan k'addara, ta rafka tagumi tana tunani daga baya tace "Samira bari na tashi naje naga magriba na neman yi, sai kinji ni awaya zamuje,  kacako jibi k'ila asake wani" sukayi sallama sannan ta nufi gida, bata fi minti uku da shiga gida ba ya shigo cike da gajiya da tsananin yunwa, baiyi mamakin ganin dining wayan ba abinciba, don tun lastweek ta fara dawo da d'abi'arta dama ance mai hali baya  fasawa, haka kurum yaji ransa ya b'aci don yunwar bak'aramin kamu ta  masaba, tunda ya amsa sannu da zuwan da tamashi taga ba annuri fuskarshi kallonta yayi ad'aure yace "Kafin na dawo daga masallaci ki samamin abinda zanci" bin k'eyarshi tayi da harara tare da jan siririn tsaki, ta nufi kitchen ta d'ora ruwa sharp sharp ta dafa indomie wanda sai da takusa gamawa ta zuba 2 spoons na miya aciki, sannan taje ta d'auko juice afridge da cup ta ajiye masa, ita already taci abincinta gidan Samira sai k'ila dare  ta samu wani abun taci before ta kwanta. Koda yadawo ya tarar da indomie baiyi mamaki ba, loma biyu yayi ya ajiyeta, ya d'au key din motarsa  ya fita zuwa bakin titi ya sayo nama da gurasa ya dawo gidan, sai da yayi nak sannan ya shiga d'akinsa a inda ya zauna taga wani ledan daban da bai tab'a ba, tasan nata ne ko kunya bata jiba ta d'auka ta adana shi akitchen sai 9 zata nemeshi.

NAMIJIN KISHIWhere stories live. Discover now