PAGE ONE $TWO ROYAL

4.2K 166 4
                                    

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
           *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

      _STORY AND WRITING BY_

         _Jameelah Jameey_

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_____________________________

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''

'''SISTER JAMEEY DAN ALLAH KI FARA YIMANA POSTING THIS MONDAY AM BEG YOU SISTER JAMEEY WALLAHI GIMBIYA HAKIMA KO BA'A FADA BA ZAIYI DADI SOSAI DAN ALLAH KIYI HAKURI KI FARA POSTING THIS MONDAY DAN NEXT WEEK YAYI NISA SOSAI MUNA NEMAN WANNAN ALFARMAR😰'''

_Ko dan wanna baiwar Allah zanyi posting yau Monday, Amman ban dai cewa komai 😉😙_

Page 01&02

"Ranki ya daɗ'e Gimbiya  Hakima, Fulani tayi aike, tace tana son magana dake,"..

"Lantana aje ace mata yau bani san yin magana da kowa"....

"Maryamu, yau Gimbiya Hakima tace bata son yin magana da kowa"..

"wai Allah kice yau an tabo jaraba a cikin gidan nan? "Aiko dai"...

"Lantana! Lantana!! Lantana!! "..

"Na bani Maryamu, Gimbiya na kirana, ni yau na shiga ukku, yau buguna ne Kawai baza tayi ba"...

"Allah ya kara maki lafiya,  rainki yadaɗ'e  uwar marayu uwargijiyata, ina neman sausaci rain Gimbiya ya dade"...

"Lantana, mai kika tsaya yi waje ina ta kiranki kin gyaleni?"..

"Ina neman a fuwarki ya uwargijiyata'..

"Yi man shiru ba wanann na tambaye ki ba, "nace uban me kika tsaya yi a waje?"...

"Eh naje nakai sakonki ne, "wani sako? "Na baki san yin magana da kowa yau".

"Shine kika yi ma mutane wannan uwar tsayuwar, ke Bilkisu"...

"Naam Allah ya ja da rain uwar marayu Allah yaja da tsawancin kwana Gambiya Hakima"..

"wuce maza ki kiran man Sarkin bulala, yanzun nan"..

"Ton Allah ya taimakeki"

Nan Bilkisu ta tafi kiran sarkin bulala cikin rawar jiki tana tausayin Lantana dan bata san wani kallar hukunci Gimbiya Hakima zata yi ma Lantana ba..

"Dan Allah Gimbiya ki man rai, ki duba tsufa na, kiyi hakuri, kuskurene nayi ina neman afuwa"..

Tas! Tas!! Tas!!!

Gimbiya Hakima ta wanke Lantana da Mari tana cewa..

"Yi man shiru tsohuwar banza, tsohuwar wofi, ke har wani  tsufa ne dake da za'a kalla aji tausayinki, to ni *GIMBIYA HAKIMA,* bani tausan Yaro balle tsoho"..

Suna cikin wannan yanayi sai ga Sarkin bulala yazo..

"Ran Gimbiya ya dade, gani na ansa kiranki, yake uwar Marayun masarautar  kano"...

GIMBIYA HAKIMAWhere stories live. Discover now