61&62

584 46 4
                                    

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_

    _Jameelah jameey 🖋_

    *(Yar mutan kankia👸🏻)* 

  


*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''


61&62



Bayan tafiyar Sarki Abdulmatalak, Sarki Abdulhadi ya haɗa Gimbiya Fulani da Gimbiya Yakumbo cikin daren nan yace yana san yayi magana da su.

Bayan sun zauna suna jiran jin maganar da Maigidan nasu zai yi su cikin daren nan, bayan bai taɓa yi masu kallar wannan neman na gaugawa ba.


"Yakumbo! Fulani."

"Allah ya taimakeka, Allah ya sa lafiya dai? Dan tunda nike dakai baka taɓa taramu cikin dare ba, koda zaka auri Fulani ba cikin dare kayi man maganar auren ta ba."

"Yakumbo lafiya lau, wanann abun a faɗi ne da zafin-zafinshi ba sai ya huce ba shiyasa na tare ku."

"To Alhmdulh yanzun hankalina ya kwanta, muna sauraranka Mijinmu."


"Da man maganar Hakima ce."

"Hakima kuma Maimartaba sarki Abdulhadi."?

"Eh Yakumbo Hakima Allah yayi na fidda ma Gimbiya Hakima miji."? 

"Miji? Hakima ka fidda ma Miji."?

"Eh miji, ya naga kamar hankalinki ya tashi wani abu? Ko tana da wanda take so."?

"Aa ko ɗaya, kawai ina mamakin Hakima da miji, naga duka duka yaushe ta gama karatun har kuma an fara maganar aure."

"Karki damu, daman ai nasha tambayarki nace Daughter ɗinki tanada wanda takw so kice babu, to ni Abdulhadi Abdulsalam na baka Yarima Hakim Abdulmatalak auren Gimbiya Hakima ko bayan raina ban yarda a ɗaura ma Hakima ko wa ba inba Hakim ba."

"Ai ba matsala naji dadi da Hakim ka ba auren Hakima, dan nasan Gimbiya Kubrah zata kula da Hakima sosai."


"To kunji abunda zan gaya maku, in Allah ya kaimu gobe ina san sake ganinku baki ɗaya harda su yaran, dan inasan gaya ma Hakima wannan albishir ɗin."

"To Allah ya kaimu goben lafiya."

Nan Gimbiya Fulani ta fito tana murna dan taji dadin haɗin da mijin nata zaiyi ma ɗiyar tata, nan ta bar Gimbiya Yakumbo dan ita take da kwana a turakar mai Maimartaba.

____________________________

*×ZARIA×*

Bayan Sarki Abdulmatalak ya huta yake tara duka iyalanshi taron gaugawa a babban parlournshi.

GIMBIYA HAKIMAWhere stories live. Discover now