47&48

627 53 6
                                    

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_

    _Jameelah jameey 🖋_

   *(Yar mutan kankia👸🏻)*

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''

47&48

"Hakima sannu kinsha karatu kinga yanda kika koma."? 

"Momy ba dole ba wallahi karatun naija ba sauki shiyasa naso Baffah ya fidda ni turkey amman yaki yarda."

"Daughter ai zuwanki Zaria kin chanza sosai ba kamar da ba, tunda gashi yanzun bayinki suna samun sausauci."

"Uhmmm! Ni daman ko da Momy ba abunda nike yi masu kawai dai kuke ganin Ina matsa masu."

"To Daughter ki kara sabo dasu kinj."?

"Eh naji Momy, "Daughter yanzun har zaki shiga 300 level amman banji kin fara kula samari ba, komai yasa."?

"Haba Momy ai ni yarinya ce fa duka duka yanzun  nike da shekara sha tara fa, ni gaskiya ban isa aure ba."

"Aiko kice kika isa aure, ki fara kula samari in ba haka ba Maimartaba ya fidda maki da kanshi kinsan dai kina gama karatun nan aure zaiyi maki."

"Momy jibaini fa yarinya dani Baffah yayi man aure tun yanzun ina laifin na gama masters din sannan."

"Daughter waya gaya maki gidan sarauta ana karatu."?

"Momy amman.. "Da kata Hakima."

Yakumbo ta tsada Hakima cikin fushi dan ta lura Hakima batada ra'ayin kula samari kuma tana tsoran karda maimartaba yayi mata auren dole...

"Daughter gidan sarauta ba'a karatu sai dai mulki yanzun ne da zamani ya shigo mu masu sarauta muka dauki boko muka sama kanmu Amman mu da mulki aka sanmu."

"Kuma Ina laifin da ya barki kikayi degree, ki fidda master a zuciyarki kisa aure, Daughter ki fara kula samari kafin dare yayi maki shawarata kenan a matsayina na Wanda ta daukeki diya."

"To insha Allah Momy zan duba, ni zan wuce Momy na barki lafiya."

"To Daughter, kin gaida Fulani KO? "Aa yanzun zan wuce wajenta daman daga wajen Baffah na biyo wajenki sanann wajenta, "OK Daughter."

Haka Hakima ta dauke shashen Fulani tana tunani maganar da Yakumbo tayi mata ba kamar wannan maganar, "Daughter ki fara kula samari kafin dare yayi maki."

Haka Hakima ta Kama maimata wanann maganar har ta iso shashen Fulani, nan akayi mata iso ta shiga..

"Fulani ina wuni, "Lafiya Hakima ya karatun."?

"Lafiyalau Alhmdulh, "to Allah ya bada sa'a, "Amin ya Allah..."

"Na sa maiki Lafiya."?

"Lafiya lau, in kina bukata ki shirya gobe zamu adamawa bikin Yarima Bishir."?

GIMBIYA HAKIMAWhere stories live. Discover now