73&74

587 43 1
                                    

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_

    _Jameelah jameey 🖋_

    *(Yar mutan kankia👸🏻)* 

  


*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''

73&74

Washe gari bayan su Gimbiya Zulaha sun gama shiryawa suka ɗauki hanyar Kano dan zuwa kai lefen Gimbiya Hakima da Yarima Hakim.

"Kilishi yau dai zamuga wannan Hakimar da Hakim ke yi ma rawar kai".

"Aiko dai yayi ya gama  dan shekara ɗaya zaiyi ita, ta zama ta Hamad baki ɗaya har abada kuma ta haifamana sarki".

"Hhhhhh! Kilishi kina sani farinciki wallahi shiyasa nike sonki, insha Allah zuri'ata ta dunga zama sarki kenan har abada Kilishi ".

Wani kallon banza Kilishi tayi tana aiyanawa cikin zuciyar ta itace zata kama ganin sarki a cikin zuri'atar , dan wannan komai da komai da Humad ya dace basu Hamad ba.

*Niko nace bawan Allah Humad shi baima san Gimbiya Kilishi na wanan wahalar ba dan bai damu da mulki ba🤣*

Haka dai suka kama yan maganganun su har suka iso masarautar Kano.

Baki sake su Gimbiya Kilishi dan sunga tarba ta girma, sunga idan akeyin abun girma da nuna arziki duk da Gimbiya Zulaha tasan masarautar Kano amman rabonta da masarautar Kano tunda da Sarki Abdulhadi zai auri Fulani  bata sake zuwa ba ita acewarta ba halinta ɗaya da Gimbiya Yakumbo ba shiyasa suka rabu.

Bayan angama ansar lefe suka wuce shashen Gimbiya Yakumbo, da yake a shashen Maimartaba Sarki Abdulhadi aka anshi lefen, zasuje suci abinci sannan su wuce gida.

"Sannunku da zuwa Gimbiya Zulaha, ashe rai kanga rai".?

"Gimbiya Yakumbo gashi kuwa, ya na samaiki keda ɗana Yarima Annas ".? 

"Lafiya lau kika samaimu, harda ma ɗiyarku Hakima ita da mahaifiyarta duk muna lafiya".

"Haka nike san ji, yau dai saura yan kwanaki akawo mana Amaryar mu, "eh daga gobe zamu fara aladar bikukuwan sarauta insha Allah ".

"Da kyau, ina ita Amaryar take bata zuwa ta gaidamu".?

''Aa fa Zulaha kin taɓa ganin ida Amarya ta fito ranar da ake kawo lefenta".?

"Ai nasa zaki kirata tazo mu gaisa ba wanda yaji ba wanda ya gani".

"Aa ni ba haka nike ba, kuma Hakima bata gidan ma baki ɗaya kuyi hakuri ta kusa dawowa masarautarku baki ɗaya ma".

"Shikenan muna maraba lale da zuwan ta Amarya Gimbiya Hakima ".

"Yauwa haka nike san ji daga gareku, kuci abincin mana, "to yanzun ko zamuci".

GIMBIYA HAKIMAWhere stories live. Discover now