09&10 Hausawa sunce gani ya kori ji, so sister karki sake a baki labari

732 59 0
                                    

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''

https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=what
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_

    _Jameelah jameey 🖋_

    *(Yar mutan kankia👸🏻)* 

   '''
A GASKIYA BA NI DA BAKIN DA ZANI YI MAKU GODIYA SAI DAI NACE ALLAH YA BAR KAUNA MASOYINA DOMIN COMMENT DINKU YANA SANI FARINCIKI SOSAI DA SOSAI 💃🏼💃🏼💃🏼❤️❤️''' 
*Ga mai bukatar shiga group 08160508316 yayi ma wanna number magana banda kira pls*

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''

11&12



Washe gari bayan Yarima Hakim ya tashi daga bacci yayi wanka sannan ya yayi addu'ar fita, ya fita sannan ya wuce shashen Fulani..

"Fulani ina kwana, "lafiya Lau Hakim ka tashi lafiya? "Lafiya lau Alhmdulh"..

"Fulani ni zan wuce office,"to Hakim, Allah ya tsare ya baka sa'a, "Amin Fulani"..

"Hakim ka biya shashen Gimbiya Zulaha da Gimbiya Kilishi  ka gaishesu kaji?"..

"Fulani kin san matan nan ba son mu suke ba, mai zanje nayi wajen su"..

"Kaje ku gaisa Hakim ai kafi su har gun Allah,dan haka ka wuce ku gaisa"..

"To shikenan ni na wuce dan yau inada lectures, "to Allah ya baku sa'a"..

Nan Yarima Hakim ya fara shiga shashen Gimbiya Zulaha, nan yasa akayi mashi iso sannan ya shigo..

"Antashi lafiya? Lafiya, wani abu ka shigo man waje tunda safe? Dan nema"..

Dan Gimbiya Zulaha Tayi mamakin ganin Yarima Hakim, ai ita ta tashi da niyar ganin gawar Hakim, to wai shi Hakim wani kalar mutun ne wannan, mutun yaci guba amman ya tashi lafiya lau kamar kowa, tana cikin maganar zuci taji yace...

"Kwantar da hankalinki matar sarki, kema kin san bin umarni ya kawo ni wajenki, ba dan haka ba ba abunda zani yi a wajenki"..

Gimbiya Zulaha taji zafin maganar da Yarima Hakim yayi mata, amman sai ta daure bata nuna mashi komai ba tace.

"Ai daman ana san yaro mai biyaiya ga iyaye kayi kokari sosai  Hakim"..

Haka Yarima Hakim da Gimbiya Zulaha suka kama gaya ma juna magana a fakaice sannan ya taso ya wuce Shashen Gimbiya Kilishi..

"Antashi lafiya Aunty? "Lafiya lau Hakim, ana nan anata kokari ko?". 

"Alhmdulh Aunty ni zan wuce na barki lafiya,"to shikenan..

Haka ya fita yana mamakin halin Gimbiya Kilishi, ita bata nuna ma mutun tana jin haushin shi ba kamar Gimbiya Zulaha ba da bata iya boye kishinta ba, bayan tare suke duk wani tungu acikin gidan..

GIMBIYA HAKIMAWhere stories live. Discover now