13&14 HMMM! YAR'UWA KARKI SAKE A BAKI LABARI

689 52 0
                                    

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_

    _Jameelah jameey 🖋_

    *(Yar mutan kankia👸🏻)* 

  


*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''

13&14




Washe gari tun da asuba Inna Lantana ta tashi ta hadawa Gimbiya Hakima ruwan wanka..

"Allah yaja da tsawancin kwanan Gimbiya Hakima uwar marayu, ga ruwan wanka nan yana jiranki"..

"Ina Bilkisu take? "Ranki ya dad'e ai Bilkisu suna madafa suna nema maki abunda zaki karya kummallo kafin ki wuce bokon"..

"Maza kije kice mata, ta sallami Azima ta taho ta taya ki fiddo man kayan sawa, dan ita Azima tafi ku sanann kyau''...

"Angama yar'sarki, matar Sarki da yardar mai duka, "zaki tashi kije ki ban waje ko tsayawa zakiyi ki isheni da wannan maganganun naki, wanda basu da dadin sauraro?".. 


"Tuba nike uwargijiyata, "maza tashi ki ban waje kije ki kirata ko kun dawo"...

Nan Gimbiya Hakima ta shiga wanka da suna da eight, Lantana tayi mamakin yanda Gimbiya Hakima tayi mata yau, wai yau Gimbiya Hakima bata zageta ba da tace mata matar Sarki, bayan Gimbiya Hakima bata san ace mata haka tunda ita bata da niyar yin aure, tafi san ta zauna gida tana zuba mulkinta yanda ta gadama, Gimbiya Hakima kenan..

"Harma kun gama kenan? "Wallahi kin san halin Gimbiya Hakima, bata cin abu mai nauyi da safe shiyasa muka soya mata biredi sai dankali da Tea"..

"Sannun ku to, ke Azima taso muje fidda mata kayan sawa har ta shiga wanka"..

"Wai Inna Lantana kina nufin Gimbiya Hakima ce ta tashi tun karfe bakwai saura?".. 

"Nima nayi mamaki, dan tun ina gyara cikin dakin baccinta naga ashema idonta biyu, kawai dai tana wasa da waya sai da na gama hada mata ruwan wanka sannnan nayi mata magana"..

"Ku har mamaki kuke kenan? "...

"Ai abun mamaki ne Ba'ba Bilkisu,"to ku daina Mamaki ke Lantana kin manta yanda Gimbiya Hakima ke da san karatu? "Aah nasan tana da san karatu mana ban manta ba"..

"To Azima bari na gaya maki wani hali mai kyau na Gimbiya Hakima, "to Ba'ba Bilkisu ina sauraranki, Amman bari muje mu fiddo mata kayan sawa kafin ta fito"...

"To shikenan nima kafin ku gama na gama jera mata abinci, "to mun tafi, nan su Lantana suka tafi fiddo ma Gimbiya Hakima kaya, ita kuma Bilkisu ta jera mata abinci, bayan sun fiddo sanann suka dawo"...

GIMBIYA HAKIMAWhere stories live. Discover now