57&58

538 53 4
                                    

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_

    _Jameelah jameey 🖋_

    *(Yar mutan kankia👸🏻)* 

  


*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''

57&58

"Allah ya taimakeki angama haɗa ruwan wankan yana jiran ki."

"Azima ki fiddo man kaya masu sauki dan kwaliya kawai zamu tafi sai gyaran jiki cikin gari kafin lokacin walimar yayi."

"Angama uwar marayu a fito lafiya, "Uhmmm."

Bayan Gimbiya Hakima ta shiga wanka Azima ta fido mata wani material wanda ya ansa sunan shi material, dan Azima ba daga baya ba wajen iya zaɓen kaya shiyasa Gimbiya Hakima take san duk inda zata ta tafi da Azima dan tana da kallar waye wa..

Sai da tayi kusan awa biyu sanann ta fito daga wanka, nan su duka ukku suka haɗu wajen shirya ta, bayan sun gama shirya ta ita da Azima suka ɗauki hanya sai salon dan Gimbiya Hakima ba daga baya ba wajen tsata ba..

Shiri akeyi naga ni na faɗa dan sai mutun yayi tunanin biki ake ko suna amman ba ko ɗaya kawai walimar gama karatun su Hakima Sarki Abdulhadi ya shirya dan ba ƙaramin san yaran nashi biyu yake ba dan su kawai Allah ya bashi kuma gashi Allah yasa yana da rabon ganin kammala karatunsu lafiya dole ya haɗa liyafar da ba'a taɓa yin kamarta ba a masarautar kano.

Niko nace ina da zaiyi masu aure ai abun mai faɗuwa sai dai.. Ba ruwa 🤭.


Shima Yarima Annas ba'a barshi a baya ba wajen shiri duk da ba wani aboki ga gareshi ba a cikin masarautar hakan bai hanashi yayi abunda ya ga ya dace ba, shida Hakim abokaine a makaranta suka haɗu lokacin shi yarima Hakim yana Phd ɗinshi shi kuma Yarima Annas yazo yin masters degree  nansu haɗu sai tasu tazo ɗaya duk da Hakim ya dan girmi Annas amman ba wani girma yayi mashi sosai ba kuma halin su yazo ɗaya shiyasa freindship ɗinsu yazo dai-dai.

Sai da Yarima Annas ya gaiyyaci Hakim yazo walimarsu amman Hakim yace yayi hakuri bai da lokaci comitement sunyi mashi yawa amman insha Allah ya samu time zai zo yayi mashi congrats ya gama karatu lafiya..

Bangaren sarki kuwa ya gaiyaci ko wani sarki da yake Nigeria suzo su taya shi murnar kammala karatunsu Hakima, su ma su Gimbiya Yakumbo ta gaiyyaci ko wace matar sarki da matan yan siyasa dan tayata murnar gama karatun su Hakima.

______________________________

*× ZARIA×*

"Hakim cikinku ku ukun nan ɗaya ya shirya insha Allah zamu masarautar kano , domin taya Sarki Abdulhadi murnar kanmalawar karatun yaronshi da ya dawo daga dubai."

"Ba sai na gaya maku ba waye Sarki Abdulhadi ba a wajena ba, don Sarki Abdulhadi Aminane na hannun dama tare mukayi karatu da shi masarautar su na zauna da nayi karatu B. U. K Kano, dan haka hallatar walimar ta zamai mana dole koda muna da uziri mu ajiyeshi gefe muje."


"Allah ya taimaki adalin Sarki Abdulmatalak, ai ba wanda ya dace da ya baka zaria inba Hamad ba tunda shine babba."

"Zulaha wa ya baki izinin magana ?, "Ina neman afuwa, "ni ban damu da babba ba kuma in ta girma zan bi ai da Hakim zan tafi kenan tunda kinsan ya girmi Hamad kowa ma ya sani cikin masarautar nan ban san tashin hankali Zulaha dan haka akiyaye."

"Cikin ku wa kuka fidda mu tafi tare."?

'Allah ya taimakeka, nidai na hakura cikinsu sai ka tafi da ɗaya."

"Ina ai ba zai yuyuba idan har za'a tafi da Hamad sai dai a tafi da Humad dan shima Humad ɗin ba wani girmanshi a kayi sosai ba da za'a ringa nuna mana banbanci."

"Kilishi kema ko? To tunda abun ya zama haka ku tashi ku ban waje ban zuwa da kowa baki ɗayansu daga ni sai waziri zamu tafi."

"Allah ya huci. "Ya isa haka ku tashi ku ban waje."

Haka suka fita ana hararar juna tsakanin Gimbiya Kilishi da Gimbiya Zulaha, ita dai Gimbiya Fulani Kubrah bata tanka ba nata ido duk abunda akace shi zatayi..


Bayan ta fiyarsu Sarki ya shirya ya sa aka kira mashi Hamad suka tafi tare ba dan yaso ba, amman ba yanda zaiyi dan shi da Hakim yaso zuwa amman haka Allah ya so.

Haka suka ɗauki hanyar kano, shi ko Hakim direct shashen shi ya wuce dan ya lura kwana biyu bai da aiki sai tunanin Hakima gashi ta tafi shi ko garinta bai sani ba, "maiye amfanin tunaninta!?? Wai mai ke damuna ni Hakim, ina no gaskiya ba haka bane ni Hakim zan so wannnan useless girl ɗin Allah ya tsari kakana da asara, kawai dai dan mun saba faɗa da ita shiyasa banjin daɗin gamawar da suka yi."

Haka Hakim ya kama yan surutanshi har ya samu ya ɗauro alwallar wal'ha ya fara sallolinshi yana neman tsarin ubangiji Allah dan ya lura maƙiyanshi ba kyaleshi suke ba, shiyasa ya miƙama Allah lamarinshi shida ƙannanshi da kuma mahaifiyarshi.


Bayan ya gama sallahrshi ya tafiyarshi school ya fara marking ɗin papers din su Hakima..


Ko da yazo wajen paper ɗin Hakima yayi mamaki sosai dan yanda yaga waje ɗaya ta faɗi shima wajen final answer ne ta rubuta ba dai -dai ba.

"Uhmmm! Gaskiya yarinyar nan tana da koƙari shiyasa wani time ɗin take bugerni."

Hakim ya faɗa yana ajiye paper ɗin Hakima wajen da yayi marking sai da yayi da yawa ba laifi sannan ya ɗauki hanyar Join domin yana bukatar refresh ɗin brain ɗin shi, saboda hayaniyar da su Gimbiya Zulaha su kayi ɗazun ba ƙaramin ciwon kai take sa shi ba.


Anya Hakim hayaniyar su Gimbiya Kilishi ta saka ciwon kai🤔, nidai babu ruwa na 🤭, Team Hakima ina jiran ansarku.




_A gaskiya masoyana bani da bakin da zani yi maku godiya sai dai nace Allah ya bar kauna masoyana❤️💃🏼_


'''Tabbas naga masoya, da wanda nasani da wanda ma ban sani ba, ina ganin ruwan comments da ma fatan alkhari da masoyana suke yi man duk suna isowa gareni dan haka ba abunda zance sai Allah ya barman ku my Fans much love❤️💯'''



*Yan wattapad kuma ba'a barku a baya ba, kuna nuna man iyakar kaunarku kuma inayin ku over and over kudia ku cigaba da comments and vote ni kuma na cigaba da surbudu mako da zafafan litaitafai da litafin na suna hanya very soon kudai cigaba da biyoni 💃🏼💃🏼💃🏼*

_Yan facebook ban san mai Zance ba aiku sai dai kwando godiya da miko zuwa ga duk wani masoyana da suke facebook inajin dadin ganin comments ɗin ku kuma😍_

_By Jameelah Jameey_✍🏻



#JameelarhSadiq
#Share
#Comments
#Vote
#Like
#please

GIMBIYA HAKIMAWhere stories live. Discover now