14&15 WANAN PAGE DIN BANSAN MAI ZANCE BA AKANSHI SAI KUN KARANTA KUYI COMMENT 😍

703 59 0
                                    

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''

https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa 
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_

    _Jameelah jameey 🖋_

    *(Yar mutan kankia👸🏻)* 

  


*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''

*@JameelarhSadiq Wattpad*

15&16

Shi kuma Yarima Hakim, tunda ya kori Gimbiya Hakima waje, sai kowa ya kara shiga taitayinshi a class din, dan sun lura da alama baya daukar nonsense, dan haka sai ko wace mace mai shirin shigarmai rayuwa sai gwiwoyin su suka yi sanyi, Amman duk da haka wasu daga cikin su suna kan bakarsu..

Yana mamakin rashin tarbiya da  rashin kunya da Wannan yarinyar da ya kora take da ita,  dan ga dunkan alamu yarinyar bata da kunya dan ya ga zahiri a cikin idanunta, "aiko bamu shiryawa da ita, dan ko wacece ita ba zan dauke nonsense ba" haka ya faɗi a zuciyarshi.. 

Haka Yarima Hakim yaita mamaki, sannnan ya cigaba da yi ma yan class darasi, bayan ya gama ya hada takardunshi ya fito yayi hanyar office din shi..

Tunda ya fito Gimbiya Hakima ke bin bayanshi a baya, bai lura da ita ba dan shi har ya manta da ya kori wata yau a class din shi..

Yana bude office din shi ya shiga ya zauna, yana zama ko suit din shi bai cire ba, saboda anfara yin zafi shiyasa yake san ya rage suits din jikinshi..

Sai kawai ya ji an bankado door din office din shi, dagowar da zaiyi sai ya ga yarinyar da ya kora a class tana nuna shi da yatsa tana cewa..

"Kai dan gidan uban waye cikin garin zaria da zaka koreni a class har kana ceman useless?".. 

Yarima Hakim tsayawa yayi kallon Gimbiya Hakima yana mamakin furincinta, wai shi Hakim take mana question na shi dan gidan uban waye, cikin zafin nama Hakim yace.

"Indan baki barman office ba sai kinyi danasin shigowarki office din na, ke bama danasin shigowarki office dina ba, sai kinyi danasanin haihuwarki duniya, wawiya marar tarbiya"..

"Kai harka isa kace man zanyi da na sani? To bari kaji ni Hakima ba wanda ya isa yace man zanyi da na sanin haihuwata duniya, balle Kai,ji baika dan Allah kamar wani almajiri, sannnan kaine baka da tarbiya ba dai ni ba"..

Kafin Hakim ya tashi yayi ma Gimbiya Hakima wani abu, har tayi ficewarta, dan daman a tsorace take dashi tana kallon idonshi da ta shigo office din shi taji tsoranshi ya kamata, kawai dakewa tayi ta mayarmai da ansa, dan bata iya daukar bakin ciki ita daya kwara suyi two two, daga office din Hakim wata lecture din ta wuce, Allah ya sota lecturer din bai Kai da shigowa ba, ta samu waje ta zauna taci kunu.

GIMBIYA HAKIMAWhere stories live. Discover now