28&29

603 44 3
                                    

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_

    _Jameelah jameey 🖋_

   *(Yar mutan kankia👸🏻)*

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''

29&30

"Oyoyo! Oyoyo!! Oyoyo!!! Daughter sannu da dawowa"...

"Yauwa Momy, wallahi Momy duk nayi missing dinku, "ai muma munyi missing dinki Daughter, "Amman shine ko ziyara baku kawo man ba".?

"Ai Maimartaba yace karda aje, a barki kiyi karatu sosai, yanzun tashi kice abinci sai kije ku gaisa da Fulani".

"Uhmmm! Mai aka dafa man? "Sinasir mana shi nayi maki da kai na ma, "Yauwa thnk you Momy". 

Nan Gimbiya Hakima taci Sinasir din sosai sannan ta nufi shashen Fulani....

"Fulani sannu da hutawa, "Yauwa Hakima ya karatun? "Alhmdulh, "Allah ya baki sa'a, "Amin ya Allah".

"Kinje kin gaisa da Maimartaba ko? "A'a sai gobe zani, na dai aika am maman ison ganinshi".

"To Allah yayi maki albarka, "Amin ya Allah, ni zan wuce, "To Hakima dan Allah kiyi hakuri da wannan bayin Allah da suke a karkashinki"..

"To insha Allah zanyi iyakar kokarina Fulani, na barki lafiya"..

Bayan Hakima ta koma shashen ta, waya tayi da Maryam sun jima suna wayarsu sannan sukayi sallama..

"Bilkisu, "Allah ya taimaki Gimbiya Hakima gani gabanki ina jiran umirninki"..

"Ki dauko takalma nan akaima Barau ya gogeman su, dan inasan gobe naje gidan marayu"..

"Angama ranki yadad'e yanzun zani cika umirninki "..

"Uhmmm, abunda Gimbiya Hakima tace Kenan , sannan tace, "kice ma Azima ta ansoman ɗinkina gidan waziri, Lantana kuma ta gogeman kayan baki dayan su"..

''To angama yar'sarki jikar'sarki, "bayan nan ki gayama masu aiki nan shashen gobe da safe bayan kungama aiki ina san ganinku baki daya"...

"Insha Allah uwargijiyarmu na barki lafiya "...

Nan Bilkisu ta tafi ta gayama Barau sakon Gimbiya Hakima..

"Malan Barau sannu da hutu, "Yauwa Bilkisu yan zauzau ansha zauzau, "Aiko dai Malan Barau ya muka samaiku? "Alhmdulh "..

"Ai mu tunda kuka tafi , muka fara ƙiba da kumari, dan rabon da aima wani bawa a masarautarnan hukunci ko yatsa tun tafiyarku ba'a nuna mana ba, daman Gimbiya Hakima itace marar tausayin da mutunci, to kuma tayi mana nisa"...

"Muma ai tunda muka tafi muke jindadinmu, da man kune kuke jamana, tunda bakusan halin Gimbiya Hakima ba shiyasa kuke bata mata rai"..

''Ai baku ganeba Bilkisu Amman.. "Da kata dan Allah, haba ya isa haka Malan Barau , ko baka san baki shi ke yanka wuya ba? Yanzun idan wani yazo wucewa ya jika kana ai banta Gimbiya Hakima kaga kashiga uku kenan, harda ma ni, dan haka ga wanann takalman nan na Gimbiya Hakima ka gogesu kafin gobe"...

GIMBIYA HAKIMAWhere stories live. Discover now