26&27. Yau dai zanga mai Team Hakim zaku sake cewa 😍

602 50 8
                                    

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_

    _Jameelah jameey 🖋_

   *(Yar mutan kankia👸🏻)*

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''




27&28



Haka rayuwa ta cigaba da tafiya ba bu wata jutuwa a tsakanin Hakima da Hakim, dan baki dayansu sunyima juna tsana maitsanani wanda suna  iya kashe junansu idan suka biye ma zuciyoyinsu..

'''(Allah ya rabamu da akin da nasani Amin)
'''

Yau su Gimbiya Hakima zasu fara exams, dan haka tunda safe ta shiriya duk da ba eight garasu ba Amman tana san fita da wuri dan ta kara duba inda take confused din bai zauna ba sosai, shiyasa..

"Lantana! Kinsan bansan kuna bataman lokaci Amman gashi har bakwai ta wuce baku gama yin wani breakfast ba, dan haka ni na wuce kunci abunku"..

"Allah ya taimakeki, ko akawo maki a makarantar indan sun gama? kinsan abasan mutun ya fita bai karya kumullo ba".

"Aa Lantana karku damu ba sai kun wahalar da kankuba, zani samu abunda naci, kudai kusamu kaci ni na wuce kinyi man add'ua"..


"Ubangiji Allah ya baki nasarar wannan jarabawa uwargijiyarmu, "Amin Lantana nagode"..

Nan Gimbiya Hakima ta tafi tabar Lantana da mamakin da kusan kwana biyu suke ganin chanjin Halin Gimbiyar tasu..

"Saurin maikuke Bilkisu? "Harkin tambayimu saurin mai muke Lantana, bayan kinsan Gimbiya Hakima muke hadama abinci karya kumollo"..

"To ai ita uwarjiyarmu ta wuce boko yanzun-yanzun man"..

"Kai haba Dan Allah Inna Lantana da gaske kike? "Azima kintaba jin anyi wasa da sunan Gimbiya Hakima".?

"Aa gaskiya, Amman abun ne yana bani tsoro fa"..

"Tsoro! "

Su'duka biyu suka hada baki wajen yin maganar at wants, dan sun tsorata da suka ji Azima tace tana jin tsoro bama mamaki ba..

"Wani kalar tsoro Azima? "Eh Ba'ba Bilkisu tsoro, gudu nike karda musake jiki muna murna Gimbiya Hakima ta chanza Hali baki ɗay, tana gama jarabawa tadawo mana da halinta na farko"..

"Maiyasa kika ce haka".?

"Inna Lantana kin fini sanin halin Gimbiya Hakima nisa ba kusa ba, saboda tun tana yarinya kuke yi mata bauta,Amman ni daga baya nazo"...

"Dan haka ba Gimbiya Hakima kawai ba mutane da dama suna chanza hali saboda zasu fara jarabawa Dan Allah ya basu nasara, wani da bai sallah kan lokaci da zaran zaya fara jarabawa daga ladan sai shi a jam'in sallah, abubuwa da dama ma wanda dan Ina jin yaunwa da sai na tsaya na gaya maku shi". 

GIMBIYA HAKIMAWhere stories live. Discover now