59&60

580 44 3
                                    

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_

    _Jameelah jameey 🖋_

    *(Yar mutan kankia👸🏻)* 

  


*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''

59&60

"Ranki ya daɗ'e, asa maki eyeshadow ne."?

"Azima kyalenni sosai kinga ya nayi idan ya dace a saman eyeshadow ɗin sai ta saman."

"To Allah ya taimakeki."

Masha Allah ba ƙaramin kyau Gimbiya Hakima tayi ba abunka da farar fata sai abun ya wuce masali, dan tsayawa na gaya maku irin kyaun da Hakima tayi ɓata lokacine dan haka Team Hakima wanan aikin naku ne sai ku gaya man kalar kyaun da Hakima tayi 😍.

"Allah ya taimakeki gskiya ko ba'asa eyeshadow ba kinyi kyau a haka, amman a sanya maki dan ƙara ma kwaliyar armashi."

"Uhmmm."

Abunda Gimbiya Hakima tace kenan, sannan mai make-up ta cigaba da aikin ta bayan ta gama yi mata kwaliya wata arniyar atamface black and red a Hakima tasa sanann aka murza mata ɗaurin dankwali mai kyau da aji bayan angama ɗaura dan-kwalin ta ɗaura alkaibarta bisa kayan sanann tasa takalimin viccin half-shop tasa sai ta sake fitowa Hakimarta yar'shekara 22,bayan sun gama shirya ta dubu ɗari hudu ta ba masu gyaran sannan suka wuto gida.

Bayan sun koma gida direct shashen Fulani ta wuce nan ta sake gyara idan ta ga ya dace ta gyara sannan ta wuce shashen Yarima Annas su Lantana na take mata baya.

Bayan ta isa bakin shashen shi aka yi mata iso ta shiga su kuma su Lantana suka tsaya bakin shashen suna gaisawa da sauran bayi yan uwansu.

"Yaya sannu da hutawa."

"Yauwa Hakima, masha Allah gaskiya ƙanwar nan tawa tayi kyau sai kace wanda zataje kasar kyau."

"Haba Yaya Annas karka fasa man kai fa, "Hakima ai gaskiya na faɗi amamn sirikin nawa zai hallaci wannan walimar ko."?

"Rufan asiri Yayana ina Hakima ina kula saurayi? Kaganni nan bani da wani saurayi kawai dai kwaliya akayi man saboda wannan walimar."

"Hakima kina aikin mai baki tsada miji ba? Bayan kin san Baffah aure zai yi maki tunda kin gama karatu."

"Yaya Annas am still young fa, duka duka yanzun nike da 22yrs ban isa na fara kula samari ba."

"Shut up Hakima, ke ɗince baki isa kula samari ba dan sakarci irin naki na banza."? 

"Yaya Annas, haba maiyasa ni ba'a sona cikin gidan nan inba ba'a sona ba taya za'a yiman aure inada wannan shekaru."?

"Hakima kisa ranki anyi maki auren dole angama, dan wallahi nasan Baffah aure zai yi maki kuma laifin kine, kinga ni da man nasan Baffah zai fidda man mata shiyasa ban kula ko wace yarinyaba, amman ke dai Baffah ya baki chain ke kika yi wasa damarki tashi mu tafi naga am fara taruwa."

GIMBIYA HAKIMAWhere stories live. Discover now