32&33 TURKASHI AGAIN NI BA ZANCE KOMAI BA

575 51 8
                                    

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_

    _Jameelah jameey 🖋_

   *(Yar mutan kankia👸🏻)*

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''



33&34



"Hakim lafiya naga duk ka wani zama silent maike damunka."?

"Hmmm! Aliyu kai dai bari wallahi yau nayi ma Hakima abunda banji dadi ba ko da sau daya ne."

"Mai kuma ya sake haɗaku da ita."? 

"Kawai dai kasan abunda tayi man a join, to shine nima na rama amman at the end banji dadin abunda nayi mata ba wallahi totaly."

"Wata sabuwa inji yan-caca, mai kuma kayi mata."?

"Kawai dai ta tambaye ni zata fita na hanata daman already na fahimceta fitsari xatayi, wallahi banyi tunanin fitsarin ya matseta sosai ba kawai naga yarinya na fitsari a tsaye, baka ji yanda nike ji ba kamar mai."

"Ayya! Maganar gaskiya Hakim baka kyauta ba, ai koda zaka rama abunda Hakima tayi maka bai kamata kayi mata haka ba."

"Ko baka san ba'asan mata na tara fitsari ba? Balle ita ta tambaye ka ka hanata gaskiya  baka kyauta ba."

"Uhmmm! Naje nayi ita bata ga abunda tayi man ba, dan haka ni nama kyauta, na lura kifi son Hakima a kaina komai akayi nine banda gaskiya."

"Yes of course! Nidai naga kai ka wurga mata ɓawon ayaba, maimakon ka bata hakuri sai MULKI DA SARAUTA suka hanaka dan gani kake ka fi karfin da zaka bata hakuri, ita kuma taga bata iya kyaleka har ta rama."

"To na Hakima naji sai akayi ƙaƙa? Dan haka ba ruwanka faɗana da Hakima kasa ido kayi kyalo shine naga OK."?

"Ni kuma bani yin shiru mudin nagani sai nayi magana, kawai ina ganin gaskiya a hana ni magana gaskiya sai nayi."

"To parrot! Ai sai kai tai tayi, tunda bakasan kaga bakinka yana shiru ni tashi ka ban waje zani gaida Fulani."

"Ai bakai ɗaya keda Fulanin ba, dan haka tashi mu tafi daga nan naga Sahibata."

"Baka da kunya a gabana? Kayi addu'a Allah yasa Maimartaba indan ya tashi badasu ya sa sunanka."

"Amin ya Allah, Nifa Hakim duk wanda aka bani inaso dan ai duk kamarsu ɗaya dan har yanzun bani gane Maryama balle Sadiya."

"Hakane kake wahalar banza baka ganesu kenan? "Wallahi ko"to Allah ya kyauta niko dai ba gaya maka zanyi ba."

"Naji tashi mu tafi, Nan gaba dole na ganesu insha Allah tunda ɗaya zata zama halak malak ɗina."

GIMBIYA HAKIMAWhere stories live. Discover now