36&37

618 59 7
                                    

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_

    _Jameelah jameey 🖋_

   *(Yar mutan kankia👸🏻)*

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''

37&38


"Gimbiya Hakima Uwargijiyarmu barka da dawowa wanann masarauta mai albarka."

"Uhmmm! Ladi ina fatan kuna aiki yanda ya kamata."?

"Eh Uwargijiyarmu muna yi, muna farin cikin dawowarki uwar marayu."

"Zaki iya tafiya, ki gayama yan'uwanki da su tabarta da suna aiki akan lokaci."

"Angama ƴar'sarki jikar sarki, na barki lafiya, "Uhmm."

"Larai! Mu godema Allah wanan karatun yasa Gimbiya Hakima ta chanza baki ɗayanta."

"Aiko dai Larai, karki so kiga kallar farin cikin da nike, domin koni jiya da naje yi mata barka da dawowa fuskar sake ba kamar da ba."

"Alhmdulh! Hakan ma mungode, indai babu wanann zagin dake yi mana ai ba komai."

"Zaman lafiyarku da Gimbiya Hakima shine ku ringa yin aiki kan lokaci, dan ita Gimbiya Hakima batasan taga mutun bai san abunda yake ba."

"Hakane kuma Inna Lantana insha Allah zamu kiyaye duk abunda Gimbiya Hakima bata so, insha Allah zamu kiyaye."

"Allah yasa, ni na wuce wajen Gimbiya tana jirana, "a fito lafiya."

"Hutawarki lafiya ƴar'sarki matar sarki."

"Lantana na fahimci bakisan ki dunga ganina cikin gidan nan ko."?

"Allah ya huci zuciyarki, ai idan baki gidan nan muma ai barinshi zamuyi, dan kice gidan baki ɗaya zaman ki muke Allah ya taimakeki."

"To maiyasa kike ceman matar sarki."?

"Allah ya taimakeki, ai aure dole ne Gimbiya Hakima uwar marayu, muna fatan muga jininki a hannunmu."

"Hmmmm Naji yanzun dauko wannan tsarabar da mukayi ma bayin shashena ku raba kuba kowa kosan shi, sannnan ace ma su Ab'u yau su haɗa Liyafa mai kyau anjima zani ci abincin dare da kowace ma'aikaciyar shashen na ni Hakima a babban parlour na."

"Angama Gimbiya Hakima, Allah ya ƙara lafiya ya rabaki da murmushin mahassada."

"Yanzun kinji matsalarki, kedai baki gajiya da fadanci tashi ku fara aikin da na saku, ke kuma Azima shiga toilet ki haɗa man ruwan wanka."

"To Uwargijiyarmu, Allah ya ƙara girma."

Nan Azima ta shiga toilet ta fara haɗama Gimbiya Hakima ruwan wanka, su kuma su Bilkisu suka fara rabon tsarabar da Gimbiya Hakima tayi masu..

GIMBIYA HAKIMAWhere stories live. Discover now