53&54

543 50 8
                                    

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_

    _Jameelah jameey 🖋_

    *(Yar mutan kankia👸🏻)* 

  


*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''


53&54




"Boka Turmurturs na kawo kukana wajenka ina san ka shareman hawayena."

"Ina san haka, Gimbiya Kilishi ai ke ta daban ce wata matsala ce kuma ta kunno kai kuma."?

"Turmurturs kwana biyu maimartaba baya kulani ba kamar da ba shine nace anya ba shiga tsakaninmu akayi dashi ba."?

"Tabbas Gimbiya Kubrah ta shiga tsakanin ki da mai gidanki, dan haka idan muka cigaba da yin wanka lafiya lau kin fi karfin duk wani makirci."?

"Ni Kubrah zata haɗa da maimartaba shikenan Turmurturs kabarta tayi lokacine nan da shekara biyu sai Kubrah ta zama baiwata."

"Au to dan aiki yana nan yanda ya kamata dan Turmurturs yace ankusa gamawa da Hakim harda Hamad ɗin da kikace a kashe maki."

"Yauwa ina godiya Turmurturs."

Nan Turmurturs yayi mata wanka da abunda suka saba duk sati sanann ta wuce gida hankalinta kwance..

Bayan ta dawo gida wanka kawai tayi ta kwanta cikin farin ciki, dan gani take Humad ya gama Mulkin zaria, dan bata ɗauki shekara biyu wani abu ba tunda har tayi hakurin shekaru tana bin bokaye amman ba biyan bukata sai yanzun ta Zulaha ta haɗata da Turmurturs tasan bukatar ta tabiya, haka dai har bacci ya kwasheta..

_____________________________

Bayan Gimbiya Hakima sun iso gida, gyara gidan akayi sannan ta shirya ta wuce school dan suna da lecture three dan haka hutawa kawai tayi sannan ta wuce school..

"Hakima kinga yanda kika koma kamar wata sarauniya matar Sarki."

"Kinji ki wallahi Maryam kin cika surutu har wani abu na ƙara kenan? Ke bance kin ƙara wani abu ba sai ke."?

"Ai ni ba abunda na ƙara, amman ke baki ganki ba masha Allah kamar yar India, anya Hakima bakida dangi a Indiyawa ko kuma larabawa."?

"Ke dai akeji Maryam, wani lecturer ne zan ɗaukemu 300lvel wai."?

"Prof Hakim da Dr Moha sai wasu ni ban riƙe sunansu ba dan vistors lecturers ne."

"Ok Allah ya bamu sa'a, "Amin ya Allah result ya fito naga kece over'roll ma, gaskiya Hakima kinyi koƙari sosai Allah yasa ki gama da First class ɗinki."

"Kedai Allah ya bamu sa'a baki ɗayanmu ,"Amin ya Allah ga Dr Moha nan, "na ganshi daga shi sai gida kenan."?

"Eh ai last week Prof Hakim yayi  attendance wai mune serious students tunda mun dawo kan lokaci, shine muka ce ai duk ku ba garin kuke ba shiyasa  amman ya nuna I don't care a kan reason din da aka bashi."

Mtsssss"matsalarshi nasan saboda dani yayi attendance dan yaga ban dawo ba kuma bani da damuwa da wannan."

"Aa Hakima kije ki bashi hakuri, dan naji yace shine a matsayin first C. A din shi kinga dole kije office ki bashi hakuri dan mutane sai zuwa suke kuma yana yi masu favor kinga ai kema sai kije daman kamar kece karshen dawowa."

"Ba zuwan ba, wallahi wulakancin shine bani ɗauka kin sani kawai na hakura mun haɗa a second c.a da exams kawai."

"To shikenan tunda kince haka kinga Dr ba shigowa yayi ba captain ya kira Allah ya sa ba fixing zai yi mana ba, "Amin."

Haka suka gama zamansu babu abunda suka yi suka koma gida, washe gari suka dawo suka yi lecture din Hakim..

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, dan tsakanin Hakima da Hakim abun nasu sai Allah dan ba kaunar junansu suke ba..

Karatu yayi nisa sosai dan 300lvel ba abun wasa bace shiyasa Hakima take karatu ba kama hannun yaro, duk da Hakim yace ya zama dole sai ta zo office dinshi dan ta bashi hakuri, kamar yanda duk wanda baiyi ma attendance suka zo har office  bashi hakuri, ita kuma tace bata zuwa sai wannan abun ya zama sillar caryover dinta..

Yau da wuri ta shirya ta wuce school saboda Dr Moha zai yi masu test shiyasa ta fito tun eight duk da sai ten zaiyi masu test din, tunda taje karatu take dan ta lura course din Dr shima ba laifi yana da wahala shiyasa ta dage mashi, sai wajen nine thirty Maryam ta shigo itama..

"Hakima tun yaushe kika zo?, "tun eight mana, sannu da zuwa late comer, "Yauwa dan Allah Hakima idan kika fito test din nan kije ki ba Yaya Hakim hakuri ai malaminki ne karki biye ma zuciya."

"Maryam ban daukar wulakancin Hakim shiyasa,  na gaji da abunda Hakim yake yi man na gaji am tired wallahi."

"To mai yayi saura keda kin kusa gama baki daya baki sake ganin shi tunda ba garinku daya ba, "to naji zan je kinga ga Dr nan yazo Allah ya bamu sa'a baki daya, "Amin."


Bayan Dr Moha ya shigo yayi masu test ba laifi dan sunyi mamaki saboda ba haka suka ran test din zata yi masu ba amman tayi dadi sosai , dan question yayi masu masu sauki sosai, bayan sun fito Maryam ta raka Hakima Office din Hakim amman bata shiga ba sai ta tsaya bakin office din..

Nocking tayi sannan ta shiga, bata damu da yace ta zauna ba ta samu wani sit ta zauna ta jiran ya gama waya dan ta lura waya yake mai mahinmanci shiyasa..


Bayan Hakim ya gama waya ya juyo ya kyaleta sanann yace, "what Wrong with you? Kin zo ki sani gaba sai kallo kike kamar tsohuwar maiya."

"Lafiyarce ta kawo haka, dakata Hakim komai kake karka kuma ceman Maiya, kuma inni maiyace nafi karfin na cinyeka kuma kasan office dinka kallo bai isheni balle har na cinyeka."

"Shut up, stupid girl, wai Hakima sai yaushe zakiyi hankali dan Allah dan Annabi?  ace mutun kamar ciwon ciki, ki kiyayeni Hakima, to wata tsiyar ta shigo dake."?


"Ni ba tsiya ta shigo dani office din ka ba, daman zuwa nayi akan attendance din da kayi first week din dawowa, nazo ka sa suna kamar yanda kasa na su tunda mu ba garinku muke ba shiyasa bamu shigo week din farko ba."

Tunda Hakima ta fara magana Hakim ke kallon dan karamin bakinta dan ba karamin burgeshi tayi sai yaji ina kartayi shiru ta cigaba da maganar, shidai bai san reason ba amman yana san yaga Hakima na magana ba tun yau ba, amman shi dai baya daukar raini duba da yanda take magana kamar tana bashi comment..

"Ta shi ki barman Office Hakima ba wani sanyaki da zanyi tunda na fahimci baki iya magani ba."

"Bangane ban iya magani Malam duk maganar nayi ita maicece?shikenan zan tafi Allah yana sane da Hakima."

Nan Hakima ta fita office din Hakim cikin fushi wai ita Hakim zaice ma bata Iya magana ba ga kuma yace mata maiya.





_By Jameelah Jameey ✍🏻_



#JameelarhSadiq
#Share
#Comment
#Vote
#Like
#Please

GIMBIYA HAKIMAWhere stories live. Discover now