39&40

566 49 9
                                    

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_

    _Jameelah jameey 🖋_

   *(Yar mutan kankia👸🏻)*

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''


39&40


"Kilishi ya kamata ki tashi mu tafi wajen Bokan nan tunda ƙafafu sun ɗaga."

"To Gimbiya yanzun daman nike shirin aiko maki Mariya naji ko kin shirya."?

"Amman kifara fita sanann na biyo bayanki duk da munyi ɓata kama amman mu kiyaye."

"To mu hadu ta baya, dan yau sai naji abunda yasa Hakim bai mutu ba har wata hudun yayi."

'''Niko nace da alamu Gimbiya Zulaha ta manta da Allah, dan naga kominta a boka ta miƙa shi ba ga Allah ba ☹️😡'''

"To shikenan! Nima yanzun zan biyo bayanki, "kidai yi sauri dan nasanki da nawa sosai."

Bayan fitar Gimbiya Zulaha, Gimbiya Kilishi ta fara magana kamar haka.

"Sakara ai ko bakice ba dole na biki wajen bokan nan naga idan yake nima na ringa zuwa dan da alamu aikinshi yana aiki."

"Dole naga bayan Hamad, ke kuma Zulaha zan barki kiga bakin ciki, kina kallo Humad zai mulka masarautar Zaria, kina ji kina gani zan zama uwar sarki, shashasha kawai marar wayau kin ɗauki yarda kin ɗauraman."

Haka Gimbiya Kilishi ta kama surutunta har ta gama shiryawa suka ɗauki hanyar zuwa wajen boka..

Wani ƙauyene cikin Zaria tafiya ce mai nisa amman ba sosai ba, dan wani dajin Allah suka kama ketawa suna shiga cikinshi ko tsoro basuji..

Dan a bakin tati aka ajiyesu saboda mota bata shiga cikin dajin, amman su Gimbiya Zulaha suka fidda tsoron komai suka kama zurma kai cikin wannnan gurmin dajin da bakajin kukan komai sai na tsubtsaye..

"Wai Gimbiya har yanzun bamu ida isowa ba?, "ai da nisa ƙadan ma mun kusa isowa, karki damu Kilishi wanann bokan aikinshi na kyau shiyasa bani aiko kowa nike zuwa da ƙafaffuna."

"Wai hakane kuma, kinsan ance zuwa da kai yafi aike, "yauwa kinga ga bukarshi can mun iso."

"A shigo da baya-baya bamu bukatar Sallama wajen nan, karku cire takalminmu."

Haka suka shiga da baya baya basu tsoran komai sudai burinsu bukatarsu ta biya shikenan..

"Gafara dai ubanmu, mai taimakonmu mai share hawayenmu."

Kallon su yake da jaijayen idanuwanshi wanda basuda banbanci da manja nan take ya kalli Kilishi take yaji yana sha'awar kusantarta, dan tunda yake bai taɓe ganin macen da dayi mashi ba kamar Kilishi..

GIMBIYA HAKIMAWhere stories live. Discover now