28

1.1K 47 8
                                    

http://www.youtube.com/channel/UCXz_jPVZsMtLDEbT4tnNTrw?sub_confirmation=1

*Ku danna wannan shudin rubutun dake sama👆👆👆👆 domin samun wasu littafan dana rubuta, tare da magungunan karin ni'ima domin jin dadin zamantakewa*

*GIDAN KASHE AHU*

*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*

*Wattpad @maryam-obam*

*DEDICATED TO.....*
*HJY NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*

*WARNING WARNING 'YAN MATA PLZ KARKU KARANTA MIN NOVEL, ONLY MATAN AURE NA YARDA SU KARANTA*

*PAGE 28*

Iyayen Afrah sukai kanta, yayinda iyayen David din suma sukai kanshi nan Dr ya fara fada akan su fita su bashi waje domin a dubasu tare da fadin suna son kashe yaransu.....

Dad din David dinne ya katse Dr da fadin plz ka fadamin maike damun David, mai yasa yake kiran sunan yarinyar data dade da rasuwa??

Dr yace plz suje waje zai dubasu haka suka fita jiki a sanyaye babu kwari gaba dayansu suna cikin matsanancin tashin hankali.

Hjy fatima fadi take mun shiga uku duk yanda akayi aljanu sun taba yarinyar nan, inko ba haka ba taya zatayi soyayya da kafiri arne wanda ba musulmi ba, kai wlh da sake wannan zubda mutunci har ina?? Kallon mama tayi tare da fadin kin dai gani koh kin kuma ji da kunnenki abunda yarki take fadi, anya wannan yarku cema kuwa?? Koda yake wacce aka haifa ta hanyar........ Shuru tayi lokaci daya komai ta tuna kuma oho, kallon mahaifiyar AS tayi dake tsaye kana ganinta kasan akwai alamun bacin rai a tare da ita, da kuma mugun damuwa, matsawa kusa da ita tayi tana fadin kawata dan Allah kuyi hakuri akan abunda ya faru wlh......

Mahaifiyar AS ta dakatar da hjy fatima tare da fadin hjy fatima karki damu, bani da matsala kuma bani da iko akan ita yarinyar tsakanina da ita sai dai shawara a matsayina na mahaifiyarta kuma uwar mijinta, tabbas duk wani hukunci yana hannun AS tare da fara waige waige ko zata ganshi amma ina wayam baya wajen shida kamal nan hankalin mum ya tashi ta fara fadin ina ya shiga kuma, hjy fatima tace ba yanzu na ganshi a nan ba, mu duba shi, ai mum tuni tayi gaba tana waige waige amma ina baya wajan, dauko wayarta tayi dake jaka ta fara doka mai kira amma switch off, kaman ance ta daga kanta ta hango Kamal na tawowa aida sauri ta nufeshi tana fadin ina AS yace ya tafi gida

Mum tace gida kuma? Hope dai baya cikin damuwa koh? Kamal shuru yayi alaman ba'a magana, mum tace muje gidan, tare da kallon hjy fatima tace bari muje inga halin da yake ciki kafin zuwa anjima

Hjy fatima tace babu damuwa nan mum tayi gaba kamal ya tuka motar sukai gaba, can saiga mahaifin AS da shima yake wajan tun dazu tun sanda aka kawo su sai dai yaga wani daya sani an kawoshi asibitin shine yaje domin yaga halin da yake ciki, nan ya fara tambayar hjy fatima halin da Afrah din take ciki, tace da sauki tare da bashi labarin faduwar da tayi wanda yasa dr yace su fita domin su bashi daman duba su

Nan Dad yace Allah ya kara sauki tare da fadin kodai za'a fitar da ita ne? Ina AS da Mum dinshi??

Hjy Fatima cikin sanyin jiki tace sun tafi gida amma tace ba zata dadeba zata dawo

Dad yace ok, ya kamata inga Dr din ina tunanin mu kaita waje zaifi, dan ban tunanin nan zasu iya magance matsalar gaskiya ace abu tun dazu haba

Hjy Fatima tace wlh amma dai bari muga zuwa anjima yanda jikin zai kasance

Dad yace toh shikenan bari mu gani amma...... Karan wayarshi yasa bai karasa abunda yayi niyan fada ba yayi gefe domin ya amsa wayar daka duka alama wayan mai muhimmanci ne

Can ta gefe guda kam mahaifin David ne yake ta faman waya akan yanda za'a fitar da David waje, domin yaga sai yayi dagaske zai iya kwatan danshi daka hannun wannan mutanan da yake kallo abun kyama wato Afrah da kuma iyayenta, sai dai kuma ta gefe daya ita mahaifiyar David din abubuwa ne suka taru sukai mata yawa akai, musamman yanda kafin danta ya fadi taji yana maganganu kaman mai sambatu hakan yayi matukar bata mamaki hadi da bata tsoro babban burinta shine Dr ya fito ya fada musu maike damun dan nasu haka......

GIDAN KASHE AHUWhere stories live. Discover now