9

4.5K 141 5
                                    

http://www.youtube.com/channel/UCXz_jPVZsMtLDEbT4tnNTrw?sub_confirmation=1

*Ku danna wannan shudin rubutun dake sama👆👆👆👆 domin samun wasu littafan dana rubuta, tare da magungunan karin ni'ima domin jin dadin zamantakewa*

*GIDAN KASHE AHU*

*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*

*Wattpad @maryam-obam*

*DEDICATED TO.....*
*AYSHA A BAGUDU*

*WARNING WARNING 'YAN MATA PLZ KARKU KARANTA MIN NOVEL, ONLY MATAN AURE NA YARDA SU KARANTA*

*PAGE 9*

Da Sauri ya saketa yana kallonta a firgice tare da fadin maiya faru sweetheart? Mai Nene? Hannun ne? Tell me, duka a tare ya jefo mata tambayar data kasa amsa mai sai nishi da take saki sama sama, shi kam idonshi Na kanta ya kafeta dashi yana kallonta cikin damuwa tare da tausayawa, lokaci daya ya janyota jikinsa tare da rungumota a hankali yana shafa mata baya yana fadin am so sorry my baby.....

Dan Jan jikinta daga nashi tayi tare da kallonshi tana cije lips cikin wani irin yanayi Wanda hakan da takeyi yana kara ruruwar wutar sha'awar David a kanta, sosai yake jinta har cikin ranshi da zuciyarshi, lallai ya tabbatar ma kanshi yana son Afrah so kuma Wanda bazai so ace sun rabu ba domin a kanta ya fara jin abubuwa da dama akan mace, idonshi na kanta yace ko muje hospital ne??

Kaita girgiza Mai tare da fadin a'a naji ya rage zafin

Cikin tausayawa yake mata sannu, tare da fadin Nan da kwanaki kadan Zaki koma kiga Dr din daya daura Miki hannun kaman yanda yace right

Kaita daga Mai Alaman eh

Hannunta dayan ya rike Yana danja mata yan yatsun hannunta gaba daya jikinta taji ya mutu domin wani irin mugun sha'awarshi takeji sosai, Amma ta kudurta a ranta bazata Bari wani Abu ya Kuma shiga tsakaninsu ba, tana kokarin ta cireshi a cikin rayuwarta gaba daya, duka a yanzu wannan abun ya Fado Mata, domin zuciyarta na kera mata cewar wannan fah Bai kamata dake ba Afrah domin ba addinku daya ba, gwara Koda iskancin zakiyi kiyi da Wanda kuke addini daya ba Wanda addini yasha Bam Bam Ba....... Matse hannunta da yayi yasa ta dago da sauri inda idonta ya sauka a cikin kwayar idon David din inda suketa kallon juna cikin Ido, a kalla sunyi wajan minti uku Suna kallon juna kowa da abunda yake gani cikin idon Dan uwan nashi, tabbas abubuwa da dama masu sark'e zuciya yana ta kaiwa da kawowa a cikin zukatansu.... Shine ya hura Mata iska inda tayi firgit wani irin tsadaddan murmushi ya sakar Mata Wanda gaba daya taji jikinta ya mutu sosai

A hankali yasa hannunshi akan lips dinta inda ya Fara shafa mata da yatsa daya tare da Dan daddana lips din nata

Tsigar jikinta taji Yana tashi sosai, tabbas indai taci gaba da zama dashi a Nan komai zai iya faruwa ya kamata ta tafi ta barshi In..... Katse mata tunani yayi daya Kira sunanta da Afrah

Dago da kanta tayi ta kalleshi magana ya Fara kaman Mai Rada Yana fadin Zaki aureni???....

Bata San lokacin data kwashe da dariya ba, domin kalman Zaki aureni ba karamin Bata dariya yayi ba, tabbas David yasha wani Abu itace zata auri Arne Wanda ba musulmi ba? Lallai Aiko addini Bai haramta hakan ba, toh ita Bata tunanin zata iya auren Arne tabdi...... 

Tunda ta Fara dariya idonshi ke kanta gaba daya wani irin sonta da muguwar sha'awarta yake Kara shiganshi sosai, hannunta dayan ya kamo Mara ciwon Wanda yasa ta nutsu ta daina dariyan inda ya Fara magana kaman haka.

Afrah am serious dagaske Ina son muyi aure ba wasa nake Miki ba, ki bani dama, I will make you happy I promise indai na Aureki

Afrah idonta na kanshi tana sauraranshi harya Gama inda ta Fara magana kaman haka David kana tunanin tsakaninmu akwai aure ne?

GIDAN KASHE AHUWhere stories live. Discover now