26

2K 96 32
                                    

http://www.youtube.com/channel/UCXz_jPVZsMtLDEbT4tnNTrw?sub_confirmation=1

*Ku danna wannan shudin rubutun dake sama👆👆👆👆 domin samun wasu littafan dana rubuta, tare da magungunan karin ni'ima domin jin dadin zamantakewa*

*GIDAN KASHE AHU*

*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*

*Wattpad @maryam-obam*

*DEDICATED TO.....*
*HJY NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*

*WARNING WARNING 'YAN MATA PLZ KARKU KARANTA MIN NOVEL, ONLY MATAN AURE NA YARDA SU KARANTA*

*PAGE 26*


Mutane makil ne suka taru ko ince dubban mutane ne suka taru domin daura auren Abubakar Sadiq da Fatima Afrah inda cikin bata lokaci aka daura aure inda dubban jama'a suka shaida wannan daurin auren sai dai muyi ma Amarya da ango fatan sa'a da kuma zaman lafiya, toh sai dai da duka alamu daga iyayen amaryan har angon da ban tunanin yana da number din amaryar balle yasan ko tana wani hali shidai burinshi ya aureta ya rama abunda ta mishi shikenan ya cika burinsa, toh inji hausawa suka ce karshen tika tik kuma komin nisan dare gari zai waye gashi dai an daura aure koya zata kaya shin amaryan tana ma raye ko ta tafi duniyar da in an tafi babu dawowa bari mu leka muga maike faruwa amma sai munga ta gefen ango domin ganin wani hali yake ciki

AS tunda aka daura auren ya tsinci kanshi shiba farin ciki ba haka kuma ba bakin ciki ba, sai dai abu d'aya da ya dameshi shine inda ya tsinci jikinshi cikin kasala gaba daya babu wani kwari a tare dashi, ga mutane nata gaisawa dashi tare da mishi fatan alkhairi ganin inya ci gaba da zama mutane zasu iya kaishi bango ya kasa juriyar da yake kokarin yi yasa ya tashi inda ya kalli kamal tare da fadin plz kazo mu samu mubar nan bana jin dadi gaba daya

Nan kamal ya tashi suka fice inda suka gudu babu wanda yasan sun tafi, ko sauran abokanshi kamal ne ya kirasu a waya inda ya shaida musu cewa su hade gidan Iyayen AS din inda aka shirya musu lafiyyayar walima

Koda suka isa gida direct As part dinshi ya nufa domin ya kwanta ya huta, gaba daya ya rasa maike damunshi ya rasa maiya kawo mishi wannan kasalan..... Kamal ne ya katse mishi tunani da fadin wai lafiya kake kuwa??.

As cikin magananshi ta isa ya ce maika gani???

Kamal ya ce naga tun da muka tawo baka ce komai ba kuma naga is like kaman jikinka yayi wani iri

AS yayi ajiyan zuciya tare da fadin nothing just kawai ina jin bacci ne that why

Kamal yace ok toh yanzu Inka kwanta ya zamuyi da mutane??

Cikin murya irin ta gajiya yace I don't know, kasan yanda za kayi dasu and plz ban san damuwa, I need to be alone plz

Kamal yace ok tare da fita ya barshi inda yake ta tarban abokansu, in aka tambayi ango sai yace kanshi ke ciwo yasha magani yana bacci, da yaga kaman mutane basa gamsuwa da hakan saiya fara fada musu Dr ne yace yana bukatar hutu gashi an bashi magani mai sa bacci da allura shine yake bacci haka dai akaci aka sha aka watse har aka gama watsewa ango bai fito ba, saida kowa ya tafi kamal ya koma part din AS din a zatonshi zai ganshi yana ta sharar bacci amma sai ya ganshi ido biyu babu alaman bacci a tare dashi, sai idonshi da yayi dan ja ja haka, zama yayi akan kujeran dakin tare da fadin mutanen sun tafi saika sake, wlh As kana da matsala wani zubin na rasa mai yasa basa son zama cikin jama'a bayan kasan mutane rahma ne

AS yaja dan gajeran tsaki tare da Fadin plz malam indai surutu mara amfani zakayi toh ga kofa zaka iya fita dan at this moment bana bukatar dogon magana

Kamal yace Allah ya kyauta toh yanzu ya maganan dauko Amarya??

AS yace I don't know nasan mum zataji da wannan so you don't have to worry about it

GIDAN KASHE AHUOnde histórias criam vida. Descubra agora