17

2.5K 100 5
                                    

http://www.youtube.com/channel/UCXz_jPVZsMtLDEbT4tnNTrw?sub_confirmation=1

*Ku danna wannan shudin rubutun dake sama👆👆👆👆 domin samun wasu littafan dana rubuta, tare da magungunan karin ni'ima domin jin dadin zamantakewa*

*GIDAN KASHE AHU*

*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*

*Wattpad @maryam-obam*

*DEDICATED TO.....*
*KHADIJA SULAIMAN JAGINDI*

*WARNING WARNING 'YAN MATA PLZ KARKU KARANTA MIN NOVEL, ONLY MATAN AURE NA YARDA SU KARANTA*

*PAGE 17*

Bude mortuary din akayi inda akaji motsi Nan aka fara bude gawarwakin inda akaga wani na motsi ai tuni aka nufi wajan inda aka ciroshi Nan aka fito dashi inda aka gane dogon Suma yayi aka dauka mutuwa ne, kai tsaye emergency aka nufa dashi inda mahaifiyar David na ganinshi ta saki Kara tare da fadin I know it I know it my son will not Die young, Aida wani irin sauri ta tashi Inda ta nufeshi tare da kankameshi inda nurses din suka cireta a jikinshi domin za'a kwantar dashi a Duba shi, Nan aka fara Duba David din da Bai San har yanzu a Ina yake ba.....

Dad dinshi shima ya tashi cikin jin dadin d'an nasu Bai mutu ba, haka Dr sukayi caaa akan David din, inda suka gano dazu yayi doguwar Suma ne, Basu kaida sun binciki jikinshi ba ganin mum dinshi ta Fadi yasa suka yanke ya mutu Duba da oxygen din da aka saka ya tsaya.......

David Kam Yana kwance amma daga duka alama har yanzu Bai San inda kanshi yake ba, Amma idonshi a bude yake Yana kallon kowa dake wajan, sai dai baya iya gano maike faruwa, inda likitocin sukai caaa kanshi domin gano bakin zaren da yanda za'a magance matsalan, cikin ikon Allah suka gano ya razana ne Wanda hakan yasa ya fita cikin hayyacinshi, Amma sunyi iya bakin kokarinsu domin su ga komai ya Zama normal inda aka hada mishi da alluran bacci

Iyayen David tunda suka ga dansu Bai mutu ba suka warke, domin dama ciwon zafin mutuwar Dan nasu ne yasa suka shiga cikin wannan halin Mai wuyar misaltuwa

Mahaifiyar David dince ta kalli Daya daga cikin Dr din tace ya jikin nashi Ina fatan komai nashi normal babu wani matsala? Cikin kuka take maganan

Inda Dr yace karta damu komai zai koma normal

Tace Dr do whatever nidai buri na shine ya tashi, I will pay you any amount that you want, but make sure ya tashi normal ba tare da wani matsala ba

Dr yace Karki damu, zai tashi and pray for him everything to be normal

Da sauri tace Amen I wish so, I will pray for him, tana maganan ne tana kakkad'a Kai alaman zata mishi Addu'a

David Kam Koda alluran baccin ya sakeshi still Yana Nan yanda yake, sai dai ya bude ido yaita kallon mutane baya magana baya cewa komai, hakan yayi matukar tasar ma iyayenshi da hankali sosai inda gaba D'aya suka tsorata da halin da d'an nasu ke ciki, sai dai Koda yaushe suna mishi Addu'a, sannan duk wani church dake fadin kasar Nan na najeriya suna mishi Addu'a domin mahaifin David din babban mutum ne a kasar gaba kadan za muji ko waye, indai Kuna bi sannu a hankali.......

Sai dai abunda yake daure ma iyayenshi Kai Bai wuce Mai David din yazo Yi a Zaria ba, shida yake kaduna, Kuma iya saninsu Koda wajan aiki zashi Yana fada musu, balle ace yazo har Zaria ba tare Daya sanar dasu ba, toh Mai yazo Yi a Zaria haka? Har wannan mummunan abun ya sameshi??



Taro ne Iya taro inda aka jera kujeru na alfarma a babban filin gidan hjy Fatima, ga masu zuba ma mutane abinci suna ta kaiwa da kawowa wajan kaima mutane abinci, gidan ya cika da mutane makil, Wanda duk zuri'ar su Afrah sun hallara, masu cin abinci nayi masu fira nayi, masu kaiwa da komowa nayi, gefe guda kawayen hjy Fatima ne zaune gaba D'aya Inka kallesu kasan mata ne Wanda naira ta zauna musu, ciki harda Hjy Binta wacce duk tafi kowa haskawa a wajan, fira suke cikin kwanciyan hankali tare da nishad'i

GIDAN KASHE AHUWhere stories live. Discover now