14

2.9K 101 7
                                    

http://www.youtube.com/channel/UCXz_jPVZsMtLDEbT4tnNTrw?sub_confirmation=1

*Ku danna wannan shudin rubutun dake sama👆👆👆👆 domin samun wasu littafan dana rubuta, tare da magungunan karin ni'ima domin jin dadin zamantakewa*

*GIDAN KASHE AHU*

*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*

*Wattpad @maryam-obam*

*DEDICATED TO.....*
*MAIMUNA MATAR ABDULLAHI KAWATA TA AMANA*

*WARNING WARNING 'YAN MATA PLZ KARKU KARANTA MIN NOVEL, ONLY MATAN AURE NA YARDA SU KARANTA*

*PAGE 14*

Gaba daya hankalin mutane yayi Kan titi Wanda ke bayan motar David din Suma suka dinga taka burgi ganin abunda ya faru

Shi kam David Bai masan inda kanshi yake ba, sai jini dake faman zuba a jikinsa, Wanda motarshi ta bugi wata babban mota, da yawa daga mutanen wajan sun sadakar ya mutu ko waye a cikin motar, musamman yanda gaban motar har yanzu yake manne a jikin babban motar, kusan zan iya cewa Rabin motar ya shige cikin karkashin babban motar

Mutane Nan aka fiffito daga mota domin bada agaji, inda shima driver din babban motar ya fito, aka Fara kokarin janyo motar David din dake manne a jikin trailer din, dakyar aka samu aka janyo, inda wajan ya cika makil da mutane, kafin kace me har police sunzo, David kam gaba daya ba'a gabe fuskanshi domin jini ya Bata shi, kafanshi kam wajan cinyarshi wani karfe ya fasa mishi kafan sai jini ke zuba, gaba daya baya Koda numfashi, motar asibiti ce tazo inda aka daukeshi sukai Shika domin Nan ne kusa, inda wasu police suka bisu, yayinda wasu suka tsaya domin a duba aga ko za'aga wata alama a motarshi Wanda za'a gano ko waye, duk da motar tayi rugu rugu gaban ya lotse, cikin ikon Allah suka ga I'd card dinshi da Kuma wayarshi guda biyu Amma daya daga cikin wayar tayi fari alama screen din wayar ya lalace, sai karamar wayarshi suka Fara dubawa inda suka ga Ansa Dad suka doka ma number din Kira, ringing uku aka dauka tare da fadin David.......

Police din dake magana yace ba David bane, inda ya shaida ma mahaifin David abunda ya faru

Wani irin ihu ya saki tare da fadin Jesus, oh Jehovah, why tare da fadin am coming right now ya kashe wayar

Shiko David da ba'a San ko wani Hali yake ba, andai shigar dashi emergency domin a ceto rayuwarshi dake cikin tsaka Mai wuya......

AS ne cikin shiri daga duka alama zashi wani wajene, Kamal ne ya shigo falon Yana fadin Man ka shirya muje

AS yace yeah let's go na kosa in tafi wlh, I miss my mum alot

Dariya Kamal yayi Yana fadin ai yau zaka ganta tunda zaka wajanta, hakan dai suka fita inda sukai mota Kamal ke tuki suka Kama hanyar Abuja, gudu suke Suna fira jefi jefi har suka shiga cikin garin Abuja bayan sunyi tafiyan awa 2

Saida Kamal ya ajiye AS sannan ya wuce gida shima domin ya huta, AS direct part din mum dinshi ya nufa inda ya ganta zaune akan daya daga cikin maka makan kujerun falon tana kallo hannunta dauke da wayarta tana dannawa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali

Hugging dinta yayi ta baya tare da fadin my Love I really miss you......

Ai dariya ta saki tare da tashi tana fadin wow what a surprise? Mai yasa baka fadamin zaka zoba yau?

Yace haka kawai mum I just wanted to surprise you, Ina dad?

Tace Yana sama yanzu zai fito yayi lunch shi nake jira Nima......

Muryan mahaifin nashi yasa su duka kallonshi,  AS nufanshi yayi inda yayi Dan hugging dinshi tare da gaida mahaifin nashi cikin girmamawa Yana fadin Dad yau dai na kammala komai, duk wani Abu daya kaini garin Kaduna yau na Gama

GIDAN KASHE AHUWhere stories live. Discover now