44

300 10 2
                                    

wani irin runguma yayi ma Dr din cikin Jin dadi tare da fadin Allah na godema

Bayan ya saki Dr din Dr din ya fara mishi bayani kaman haka damuwa yayi Mata yawa kuma ba'a son nace Mai ciki tana shiga damuwa, jininta ya hau sosai ya kamata duk wani abu da zai Sata damuwa a bar yin shi gaba daya.

As mamaki abun ya bashi toh maike damunta da zata Sama kanta damuwa haka? Tambayan Dr din yayi zai Iya zuwa yaje ya ganta

Yace eh, Kai tsaye Dakin Da take yayi inda ya ganta a kwance idonta biyu Amma tana hawaye, ido ya kura Mata na wani lokaci sannan ya karasa gareta tare da kamo hannunta yana yana shafawa yace Afrah yau kin sani cikin farin ciki Mara misaltuwa Allah na gode ma, zan zama Daddy very soon

Wani kallo tamai cikin rashin fahimtar maganansa, Mai yake nufi da zai zama baba, kodai ya fara..... Katse Mata tunani yayi da fadin yau ina cikin farin ciki najin wannan kyakyawan labarin na samun cikin ki

Aida sauri ta Mike tare da fadin what? Ciki? Wani irin ciki? Yace Afrah na haiyuwa mana

Shuru tayi tana tunani yayin da zuciyarta ya fara Mata wani Kala, Kenan Rabon wannan cikin yasa sukai aure, ita a yanda take Jin kanta yanzu ba zata ce tana murna ba haka kuma ba zata ce tana bakin ciki ba, A ranar suka koma gida inda As yake Bata duk wata kulawa Nadia Jin shuru kwana biyu Bata zo skul ba yasa ta kirata inda ta Fada Mata Bata Jin dadi ne, nan Nadia ta bukaci address din Afrah inda ta tura Mata batai awa daya ba tazo Koda tazo ta iske As inda Nadia suka gaisa

Afrah tace mishi yar skul dinsu ce, nan ya basu waje domin su samu su tattauna, Amma kafin ya fita saida ya roki Nadia Akan ta kulan Mai da Afrah sosai inda tayi dariya tace karya samu damuwa

Bayan fitan As ne Nadia ta kalli Afrah tace wanene wannan? Naga yanda yake baki kulawa, Afrah tabe baki tayi sannan tace mijina ne..... Nadia tace what tare da tashi tana kallon Afrah din

Afrah ta kamo hannunta tare da fadin miye na razana, Nadia tace Afrah kina nufin ke matar aure ce ko kuma kina nufin shine Wanda zaki aura

Afrah tayi Dan murmushin takaici sannan tace inada aure a yanzu haka ma ina dauke da ciki a jikina

Nadia tace Afrah inhar kina da aure tabbas ke babbar Mai aikata sabon Alah ce, kina nufin kina da aure kina mu'amala da wasu maza tabbas nayi nadaman saninki a rayuwa, Nadia kokarin barin Dakin tayi Afrah ta riko Mata hannu tare da fadin karki zama mutum Mara adalci Nadia karki zama mutum mai saurin yanke hukunci ba tare da kin jira kin samu kyakyawan hujja ba, Nadia ki tsaya kiji dalili na nasan inada laifi inada aure naje ina nanikar wani namijin Daba maharrami na ba.....

Nadia tun da muka hadu na daukeki tamkar yar uwata ta jini, inaso ki zauna domin In baki labarin Kai na.....

Bata Musa ba inda ta zauna nan Afrah ta fara Bata labari Bata boye Mata komai ba na rayuwarta harta fyaden da akai Mata bin mazan data fara Har haduwansu da David irin abubuwan da yayi Mata duk ta fadama Nadia

Nadia idonta babu abunda yake fita sai hawaye daga ita Har Afrah an Rasa Mai rarrashin wani, duka kuka sukeyi lokaci daya Nadia ta rungume Afrah tare da fadin lallai Afrah Kinga rayuwa duk Wanda yaji labarinki dole ya tausaya miki, ki yafe ni nayi miki mummunan fassara da farko, Sai Dai duk da naji labarinki ba shine zaisa inki fada miki kuskurenki ba, sakan Afrah tayi daga rungumar da tayi Mata, inda ta fuskanci Afrah da kyau tace Afrah abubuwan da kika aikata duka zan iya cewa Harda rashin wadattacen ilimin addini, inda kina da ilimin addini ba zaki aikata abunda kikayi ba, duk saboda anyi miki fyade, uwa uba a cikin labarinki kince iyayenki na miki kokari ke baki taba ji a cikin ranki kin cutar dasu ba

Cikin kuka Afrah tace tabbas na yarda Harda rashin ilimin addini, da kuma son zuciya, tare da Rudin kawaye, wlh Nadia nayi matukar yin nadama Akan abunda na aikata a kullum ina yin Dana sani, Wanda hausawa ke cewa keya ce, sai yasa a yanzu nake son in dage wajan bama addini na muhimmanci domin in Kara kusanci da uban giji na.

GIDAN KASHE AHUWhere stories live. Discover now