37

318 10 0
                                    

Ta gefen Afrah kam kuka take ta rusgawa sosai a toilet tare da takaicin ganinta da yayi haka, wani irin tsanarshi takeji yana kara shigarta hadi da ganin bakinsa a cikin idonta, a yanda takeji inda kisa ba komai bane toh da tabbas zata iya kasheshi ko dan ta huta ta kuma yaye ma kanta wannan kaddararren auren da aka lakaba mata shi eh lakaba mata shi mana tunda bata San dashi ba, bata kuma da labari sanda aka daura sai dai ji kawai tayi an daura wani kwalla na takaici ne ya kara zubar mata, lokaci daya tunanin muhd dinta ya fado mata tare da tunanin ko yana ina yanzu oho? Wani irin rayuwa yakeyi yanzu?? Lokaci daya ta kawar da tunanin tare da tashi dakyar domin tun fitan AS taji rufewar kofarta ta fita inda ta kwanta akan gadon dakin jikinta na faman mata zazzabi ta kududdune a cikin blanket

Mum jin shuru bata fito ba yasa tace bari ta leka ko sun tafi ne, duk da tana tunanin bazasu tafi bata mata sallama ba, kai tsaye dakin Afrah din ta nufa inda ta ganta a kwance ta kudundune da sauri ta nufeta tana fadin Afrah lafiya kuwa....... Bata kai ga karasa maganan ba ta taba goshinta tace fever, sannu let me call a doctor family dr dinsu Mum ta kira bai wani dadeba yazo ya duba Afrah tare da fadin zai aiko mata da magani sannan ya tafi

Mum ce ta zauna da ita har aka kawo maganin ta taimaka mata tasha sannan dauko mata kaya tasa domin babu komai a jikinta sai towel, Afrah tana Bala'in jin nauyin Mum tare da kaunarta tana son Mum sosai domin tana mata kallon kaman Mama duk irin kulawar da mahaifiya zata ma yarta ta cikinta toh shi Mum take ma Afrah

Haka ta gefen Mum tana jin Afrah tamkar As tana masifar son Afrah tun farkon ganinta da Afrah a lokacin saukan Zainab gidan hjy Fatima taji son Afrah har cikin ronta tun daga lokacin take burin danta ya auri yarinyar domin ta kwanta mata a rai sai gashi Allah ya cika mata burinta sai dai duk da wannan burin nata bai hana tasan cewa Afrah hakuri takeyi kawai amma bawai tana son Dan nata bane, sai dai a kullum ta kanyi addu'a akan Allah ya karkato da hankalinta kan mijinta ta, domin ita bata ta AS dan nashi mai sauki ne zata tursasashi yayi abu koda kuwa bai so ba, amma ita kam Afrah ba komai bane zata iya sata tayi dole ba....... Motsin da Afrah tayi ne yasa mum fadin sannu jikin da sauki kuwa

Afrah cikin rawar murya tace eh da sauki Alhmdlh

Mum tace toh masha Allah mai zan kawo miki kici???

Afrah tace na koshi bana jin yunwa

Mum tace kinci abinci ne

Afrah tace eh naci

Mum tace ok tare da fadin toh ki samu ki kwanta ki huta bari inje in sallami Dad dinku in dawo

Afrah tace toh sannan mum ta fita

Mum bayan ta fita direct dakin AS tayi inda ta sameshi kwance kanshi na kallon saman dakin daga duka alama tunani yakeyi mum harta karasa inda yake bai san da mutum ba saida ta taba shi tayi firgit tare da kallon mum ya sauke ajiyan zuciya hadi da fadin Mum tare da tashi yana zama

Mum tace wai lafiya kuwa? Tunanin mai kakeyi haka ne???

Dan kago murmushi yayi tare da fadin ba tunani nakeyi ba

Mum tace Allah ya kyauta saika tashi kaje kaga matarka domin bata jin dadi dr yazo ya dubata an bata magani na barta ita daya kaje ka ganta

Ya amsa da okey amma badan yaso ba ya tashi suka fita shida mum tare inda ya nufi dakin Afrah din yana shiga abunda ya faru ya fara dawo mai yayi wajan 7mnt a tsaye yana kallonta idonta a lumshe yake ta kudundune jikinta tana dan rawan sanyi jikinsa a dan sanyaye ya karasa inda take tare da daura hannunsa akan goshinta yaji da zafi a hankali ya furta oh my God..,,,,, dai dai lokacin ta bude idonta wanda ya sauka akan nashi idon aida sauri tayi kokarin tashi amma kafin ta tashi ya taimaka ya kamota tare da dagota ya zaunar da ita duk da tana kokarin jan jikinta daga nashi amma ta kasa saboda jikinta babu kwari

GIDAN KASHE AHUWhere stories live. Discover now