31

552 21 4
                                    

http://www.youtube.com/channel/UCXz_jPVZsMtLDEbT4tnNTrw?sub_confirmation=1

*Ku danna wannan shudin rubutun dake sama👆👆👆👆 domin samun wasu littafan dana rubuta, tare da magungunan karin ni'ima domin jin dadin zamantakewa*

*GIDAN KASHE AHU*

*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*

*Wattpad @maryam-obam*

*DEDICATED TO.....*
*HJY NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*

*WARNING WARNING 'YAN MATA PLZ KARKU KARANTA MIN NOVEL, ONLY MATAN AURE NA YARDA SU KARANTA*

*PAGE 31*

Zainab binta take da kallo ganin yanayinta ya fara canzawa dama gashi bawai ta warke bane kawai tasan karfin hali takeyi tayi saurin nufanta tare da kamota, ta rungumeta tana shafa mata baya tana fadin Afrah dan Allah kisa ma zuciyarki salama, ya kamata ki sani babu wanda ya isa ya canza kaddarar da Allah ya rubuta mishi, komai da kika ga munayi haka Allah ya tsara mana, kici jarabawar da Allah ya jarabceki da ita, kika sani in kika auri wanda kikeso ya mutu tunda Allah yasa bashi bane mijinki ba????

Afrah dan jan jikinta daka na zainab tayi tare da nufa gadon dakin ta zauna tare da jingina kanta akan saman gadon, ido ta lumshe tana hawaye wani irin radadi zuciyarta yake mata,babu abunda takeji sai tsantsar soyayyar David hadi da kewarsa, ita da kanta tana mamankin yanda har akayi ta fara sonshi haka, Idan akace zata so Namiji haka wlh zata karyata sai gashi tana gani yanzu lallai so masifa ne tasha jin labarin so tana karyatawa tana ganin duk karya ne babu wani so mai zafi haka, harma tana ganin idan mutum yana mutuwar son mutun har yana ganin rayuwa bazatai mishi ba sai dashi toh karya yake duk yaudarar zuciya ne, ashe ba haka abun yake ba, ashe dagaske ne so yakan zautar da mutum yaji baya ji baya gani lallai so bala'i ne babu abun da baya sawa.

Zainab itama tana hawaye ta matsa kusa da ita har zata tabata, ta fasa tare da tashi daga inda take ta barta domin ta lura a cikin halin da dake yanzu tana bukatar kadaici bazata so a takura mata ba dan haka tabar dakin gaba daya inda tayi falo anan taga su hjy fatima kowa idonshi na kanta hjy fatima tace tayi wanka??

Zainan tace eh, tace toh nuna ma inlow dinki dakin da take, zainab ta amsa da toh

AS tashi yayi yabi bayan zainab inda ta kaishi har kofar dakin sannan ta juya, bude kofar yayi shesshekar kukanta ne yayi mishi maraba da zuwa, ji yayi kaman ya juya domin harga Allah baya san karan kuka jin kukan nata yake kaman a kawon kunnensa, har zai koma komai ya tuna kuma Oho ya juya ya shiga cikin dakin kai tsaye inda take ya nufa tare da matsawa kusa da ita ya zauna ya daura hannunsa akan kafadanda tare da janyota jikinsa yana shafa mata gashin kanta........

Jin kamshin turaren daya bugi hancinta yasa ta bude idonta a hankali domin taga waye yake tabata, idonta ya sauka akan nashi wani irin zabura tayi kaman taga abun tsoro tare daja baya amma saboda jikinta babu kwari yasa ta kasa matsawa daga inda take, janyota yayi jinshi tare da hugging dinta sosai yana shafa mata baya tare da hura mata gashin kanta a hankali

Cikin siririyar muryanta da baya fita dakyau tace masa ka sakar mun jiki bana bukatar ganinka a nan plz

Murmushi yayi tare da fadin same hare nima bana bukatarki amma yana iya dole in zauna dake tunda haka iyayenmu suke bukata, inda badan su ba toh da bazan shigo inda kike ba

Tana manne a jikinsa har yanzu ta kara fadin toh ka rabu dani nima bana bukatar ka a inda nake mai yasa ka aureni mai yasa ka amince aka daura maka ni bayan kasan ni dakai babu soyayya a tsakanin mu tana maganan ne tana kuka

Cikin muryanshi irin na gadara da nuna isa yace karki damu nan gaba kadan zaki san dalilin da yasa na aureki zan fada miki, inaso ki sani ni mijinki ne yanzu dan haka ki cire kowa dake ranki ki rungume ni kaman kwai........

GIDAN KASHE AHUWhere stories live. Discover now