35

347 19 2
                                    

Afrah ba ita ta tashi ba sai wajan karfe uku inda ta tashi tana mika hadi da salati inda taga zainab kwance itama tana bacci

Kai tsaye toilet ta nufa inda ta kuma yin wanka hadi dayin alwala tazo tayi sallah, gaba daya jinta take jikinta babu kwari gadai tanan ne dai kawai, a wajan da tayi sallah ta zauna ba komai take tunani ba sai yanda hjy fatima ta sauya lokaci daya, taba mahaifinta dukiyarshi ta gado hadi da sauke kiyayyar da take ma mahaifiyar ta, duk wanda hakan ya faru ne a dalilin wannan auren.... Iyayenta suna farin ciki da sauyawar da hjy Fatima tayi musu musamman ma mahaifiyar ta..... abu daya da zatayi ta dauwamar da farin cikin iyayenta shine ta zauna da mijin da aka aura mata lafiya..... dan cije kasan lips dinta tayi hadi da daga idanunta sama tare da fadin toh amma miye dalilin sauyawar hjy Fatima cikin sauki haka???

Anya ba wani abun take shiryawa ba?? Taba mahaifina gida saboda bata bukatar sirikanshi suzo suka inda muke kenan hakan na nufin tana jin kunyar suka inda dan uwanta yake kenan?? Kaita girgiza tare da fadin kai anya hakane kuwa? Toh inda hakane mai yasa ta bashi dukiyar gadonshi tabbas ta canza dinne dagaske.... Dan shuru tayi tana nazari tare da tuna maganan hjy Fatima din da take fadin cewa a sanadin wannan auren ne aka bata kwangilar da take burin ta samu saboda ta zama sirikar Alh muhd kura, kenan indai hakane zata iya komai taga na zauna a gidan aure na dan sauran bukatunta su biya ciki harda bama mahaifina kudinsa hadi da riba ninkin baninkin domin ya kara binta kaman yanda yake mata biyayya.... Toh amma koh bata bashi wannan kudin ba yana mata biyayya haka zalika baya bijire ma umarninta inta gindaya masa toh miye dalilin yin haka??? Kanta taji ya fara sara mata alaman ta rasa miye dalili kuma daga duka alama tunanin ya mata yawa, dan gajeran tsaki taja hadi da fadin koma mai nene I will find out in kuma na tabbatar da abunda nake zargi a ranar zan nuna mata wacece ni zan nuna mata niba mahaifina bace da take juya shi..... wani hawayen bakin ciki ne ya zubo mata wanda bana komai bane saina yanda aka aurar da ita ba tare da saninta ba ko kuma aji ra'ayinta ko tana so ko kuma bata so ba , aida sauri ta tashi tsaye ta fara sintiri a dakin wanda tasan duk wannan abun hadin hjy Fatima ne lokaci daya kuma taji wata sabuwar tsananta ya ziyarce ta hadi da fadin da fari nace na yafe miki amma a yanzu tsanarki dake raina tafi ta baya tabbas kinyi ma iyayena komai ne saboda wannan auren domin a maganarki kince kin dade da ganowa da aure aka haifeni toh kiyayyar miye kika cigaba da nunama iyayena, saida kika bayarda aurena burinki ya cika kika samu abunda kike so shine zaki watsa ma iyayena tsaba???

Hannunta ta buga a kanta hadi da fadin why mai yasa na bari tayi fooling dina ya kamata in fadama Mama wannan maganar fara tafiya tayi wanda tayi hanyar fita lokaci daya kuma ta tsaya hadi da kama kugunta tare da fadin no bani da wata hujja akan hakan inma inada hujja iyayena bazasu iya canza komai ba, hasalima sai dai in bata musu rai su dauka dan bana son Auren ne nake fadin haka kuma koda na fada aikin gama ya gama tunda an daura..... kuma mahaifina baya tsallake maganar hjy fatima wanda yake jinta kamar uwa.., Kalmar innalillahi wa inna ilaihira jiun ta furta hadi da fadin lallai kin cutar dani kin cutar da rayuwa ta duk saboda farin cikin ki, kin hanani samun wanda nake so nake burin rayuwa dashi tabbas kin cutar dani, Ido ta lumshe hawaye na zubar mata tare da fadin Mohd wato David mun shiga cikin wani irin mummunan kaddara daga ni har kai, duk irin rayuwar da muke burin yi ni dakai ya tafi a banza kenan?? Komai ya baci kenan,,,,,, kin maganan mama tayi tana fadin Afrah maike damunki? har yanzu bazaki cire wannan tunanin a ranki ba koh?

Afrah nufi mama tare da rungumeta tana fadin ko daya mama kawai ina kukan rabuwa daku ne, ina kukan yanda zan fara wata rayuwa ne wanda ban saba ba, na tabbata zanyi kewarku mamana sai kuma ta fashe da kuka mai sauti

Jikin mama yayi sanyi matuka hadi da tausayin yar tata, kun san irin soyayyar ya da uwa, mama shafa mata baya take tana fadin toh Afrah ya zakiyi haka dama rayuwar mace yake kuma aure shine Gatan duk wata mace babu iyayen da suke da burin yau ace yarsu batai aure ba, a hankali zaki saba yau muma ba gashi ba.... Afrah dai kuka takeyi wanda bana komai bane saina rabuwa da masoyinta abun kaunarta Muhd dinta..... mama itama cikin ranta tana tausayawa yar tata musamman da tasan bawai son auren take ba, tabbas auren wanda baka so abune mara dadi domin aure akanyi shine har abada, sai yasa ake son mutum ya auri wanda yake so shine kwanciyar hankalin kowa amma sai gashi ita yarta an daura mata wanda bata so, tabbas inda tana da iko toh da bata amince ba amma an nuna mata fin karfi sai dai addu'arta daya ce shine Allah yasa ma auren albarka ace gwara da akayi yasa kuma Afrah ta saki jiki ta zauna lafiya tare da fatan yar tata nan gaba kadan tayi farin ciki da auren tace gwara da akayi..... ajiyan zuciya mama ta sauke hadi da fadin ya isa haka Afrah kibar wannan kukan kinji maza muje ki shirya domin koda yaushe zasu iya zuwa domin daukarki inaso kiyi hakuri kisa Allah a duka lamuranki insha Allah zakiga komai yazo miki da sauki kinji...,,, Afrah kaita gyada hadi da fadin toh mama muryanta ciki ciki saboda kuka fuskanta duk ya tashi kun san mutum mai haske ba wuya

Dakinsu tayi ita da mama inda suka tarar da Zainab na Sallah dan haka kaya mama ta dauko mata tare da fadin maza kisa kinji

Afrah ta amsa da toh mama

Zainab ta idar da sallah tare da fadin shikenan Sis yanzu za'a tafi dake sai kuma ta saki kuka itama tare da rungume Afrah tana fadin wlh zanyi kewarki matuka ai Afrah kaman dama jira take zainab ta fara itama ta saki kukan mama dake tsaye ta fara fadin yau naga sha shanci toh miye abun kuka sai kace wacce zata bar kasar gaba daya, ke Zainab in banda shirme irin naki inma batai Auren ba aiba a nan take ba ita da take makaranta ma sai tazo jefi jefi ko in sunyi hutu

Zainab cikin kuka tace mama bazaki gane bane lokacin tana skul tana zuwa gida sanda taso amma yanzu shikenan sai kuma ta kara fashewa da wani kukan mama ganin haka yasa tace ai sai kuyi tayi tunda aiki ya ganku in kun gama kukan saiki taimaka mata ta shirya domin an kusa zuwa daukarta tana fadin haka tayi waje domin ta tabbata in ta cigaba da zama a dakin toh itama kukan zasu sakata maganin kar ayi kar afara domin inta fara rasa mai bama wani baki za'ayi

Saida sukai kukansu mai isarsu kafin Zainab tace sis ya kamata ki shirya kaman yanda mama tace, Afrah bata musa ba ta canza kaya tasa wani leshi mai kyau dinkin doguwar riga yayi mata kyau sosai duk da fuskan nata babu makeup tayi kyau sosai sai dai kallo daya zaka mata kasan cewa tana cikin damuwa sosai, fuskanta duk ta fada idonta ya kara girma, wani karamin gyale ta dauko tare da yafawa a saman kanta sannan ta kalli Zainab tare da fadin muje kasa

Kai tsaye fita sukayi inda yayi dai dai da shigowan su hjy Fatima, da Mum din AS dashi kanshi AS din da kamal, idon AS ne ya sauka akansu Afrah yau ne rana ta farko daya gano tana kama da Zainab sai dai ita Afrah tafi haske inda badan ya gane ita Afrah nada haske ba toh da tabbas bazai gane wacece Afrah dinba a cikinsu, duk ya gane kamannin nasu ne a kallon second biyar da yayi musu tare da kawar da kanshi inda yazo ya zauna a falon suna gaidawa da mama da Abba

Koda suka karaso idon Afrah nakan hjy Fatima wacce take ta mata dariya hadi da fadin sannu takwarata ya jikin naki? Ina fatan dai da sauki koh

Afrah dan cije kasan lips dinta tayi hadi da amsawa sannan ta kalli mum tare da gaidata ta kalli gefen su kamal tace sannunku da zuwa shima tayi hakan ne gudun kar iyayenta suji babu dadi bata gaida mijinta ba

Kamal ne ya amsa amma shikam As kaman bai san tayi magana a danko kallo bata isheshi ba balle ya iya amsawa ba

Afrah zama tayi kusa da mama a kasa inda ta daura kanta akan cinyar Mama, mama kam duk wani iri takeji duba da Afrah din itace yarta ta fari, kasa daurewa tayi inda ta kalli Afrah din hadi da fadin tashi kiban waje ki zauna a can......

Mum tace tashi kizo nan kinji Afrah

Bata musa ba ta tashi ta nufi mum din inda ta zauna kusa da ita hjy Binta ta janyota tare da fadin matso kusa yata jikin naki da sauki koh?

Afrah tace Alhmdlh amma cikin ranta fadi take ni daya nasan maike damuna dauriya kawai take amma inda ansan irin radadin da zuciyarta yake mata toh da tabbas dasun warware wannan kaddararran Auren kodan ta samu ta tsira da rayuwarta toh amma yata iya haka zatai hakuri har lokacinta yayi domin jinta take bazata iya kai koda shekara a raye ba gani take mutuwarta na kusa....

GIDAN KASHE AHUHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin