29

1.6K 66 17
                                    

http://www.youtube.com/channel/UCXz_jPVZsMtLDEbT4tnNTrw?sub_confirmation=1

*Ku danna wannan shudin rubutun dake sama👆👆👆👆 domin samun wasu littafan dana rubuta, tare da magungunan karin ni'ima domin jin dadin zamantakewa*

*GIDAN KASHE AHU*

*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*

*Wattpad @maryam-obam*

*DEDICATED TO.....*
*HJY NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*

*WARNING WARNING 'YAN MATA PLZ KARKU KARANTA MIN NOVEL, ONLY MATAN AURE NA YARDA SU KARANTA*

*PAGE 29*



Hango mum yayi tana tawowa ta mirror motar wannan yasa ya tada motar tare da fara kago murmurshi har mum ta iso inda motar take ta bude ta shiga

Bayan mum ta shiga ya kalleta tare da fadin mum you always look so young kullum kara kyau kike my love

Mum tayi murmushi hadi da shafa mishi kai tace muje dan Allah muga wani hali yarinyar nan take ciki, amma kafin muje ya kamata muje mu siya musu abinci

Yace yes gaskiya kam, dan ban tunanin ma akwai wanda yaci abinci a cikinsu, Mum tayi ajiyan zuciya tare da fadin ai abunne sai a hankali akwai tashin hankali kaima ka samu kaci abincin kuwa??

Yace No mum bana jin yunwa kwata kwata

Kallo mai kama da alaman tambaya mum take mishi alaman mai hakan ke nufi, bayan ta gama kare mai kallo tace taya mutum zai zauna baici abinci ba yace baya jin yunwa ta ina kaga an taba yin haka??

Murmushi yayi tare da fadin mum am serious bana jin yunwa kuma lafiya na kalau, kawai damuwar ciwon Afrah ne yake damuna ku....... Dan shuru yayi tare da kara gudun motar ba tare daya karasa abunda yayi niyan fadaba ko kuma furta wani kalma har suka isa wajen Saida abinci yayi parking yace mum let go

Fita mum tayi inda suka sai musu abinci, bayan sun fito ne mum ta shiga wani supermarket dake kusa da wajen ta siya musu kayan tea da sauran abubuwan da tasan zasu bukata, sannan ta fito suka kama hanyar asibitin

Koda suka karasa asibitin inda aka kai su Afrah nan suka nufa inda suka iske su hjy fatima harda Dad mahaifin AS dana Afrah da mahaifiyarta da Zainab da idonta yayi jajawur dan kuka

Mum tace sannunku yamai jikin ina fatan ta farfado??

Hjy Fatima tace wlh har yanzu Dr baice komai ba, gadai munan ne dai

Shuru mum tayi hadi da ajiyan zuciya kana daga bisani tace Allah ya kyauta tare da kallan AS tace kwaso ledojin mota mana, har yayi taku biyu zuwa uku ya tsaya tare da kallon Zainab dake zaune ta zabga tagumi yace Sis cum and help me.

Tashi tayi jiki a sanyaye tabi bayansa har bakin kofar motarshi inda ya danna motar hadi da budewa yace cum on zoki dauka

Matsawa tayi ta diba wasu can ya hango kamal na tawowa yace yauwa kaima zoka dauki wanda zaka iya

Kamal kallonshi yayi sannan ya dauki wasu ledojin shima kana ya kuma kallon AS din yace Man hope dai kana lafiya?

AS ya tamke fuska hadi da cewa inda bana lafiya zaka ganni a tsaye a gabanka, hadi da jan gajeran tsaki yayi gaba, ganin haka kamal yabi bayanshi har inda su mum suke duka suka zuba kayan abincin inda AS da kanshi yaba Mum din Afrah abinci tare da fadin Mama ga abinci kici......

Amsa tayi hadi da mishi godiya tare da addu'a, haka dai duk suka ci abinci duk da bawai suna cikin nutsuwa bane amma yanayinsu kadai zai nuna maka cin abincin kawai suke

Dare ya farayi inda Dad din AS yace bari dai inga wannan Dr din sun bar mutane shuru tare da kallon AS yace muje nan suka bishi harda kamal inda aka nuna musu inda Dr din yake a nan suka iske Dad din David da mum dinshi a bakin kofar Dr din daga duka alamu suna son ganin Dr dinne suma, dan haka Dad jira ya farayi inda can saiga wani ya fito daga office din Dr din ganin haka yasa AS yin nocking aka amsa da "Yes come in"

GIDAN KASHE AHUNơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ