33

384 21 2
                                    

Wani irin iska ya furzar tare da lumshe idonsa yana nazarin abubuwa da dama.... Jin maganan mum dinshi ne yasa ya bude ido tare da fadin mum har kin fito

Hjy fatima tace lafiya kuwa naga kaman ranka a bace

Murmushi ya kago tare da fadin lafiya kalau bacci nakeji sosai, sai yasa

Hjy fatima tace ya kamata kam aje ayi domin rashin bacci babban illar ne

Kamal yace saika bari in tuka motar kar kaje kayi gyangyadi ka fadar damu dariya su mum suka saki shi kam AS wata shegiyar harara ya watsa ma kamal domin haushinsa yake ji dan yaga yana son saka yarinyar can ta rainashi

Mum tace aiko haka za'ayi kamal kaika tuka mu

As baice komai ba sai tashi da yayi ya koma dayan gefen kamal ya zauna mazaunin driver mum kam itama shiga tayi inda ta zauna a bayan motar bayan tayi ma hjy Fatima sallama

Koda suka karasa gida AS gefensa yayi inda kamal ya bishi yana masa magana koda ya shiga kwanciya yayi ganin kamal nason damunsa yasa yace mai ya tashi ya tafi ya barshi ya kwanta, kamal yace in tafi ina? Ganin yayi banza dashi yasa kamal tashi ya fita inda ya nufi wajen bukkan dake gidan dan yafi kowa sanin halin AS in yana fushi baya ji baya gani

Hjy fatima ta kira abba da mama inda ta musu bayanin yanda aka tsara, akan afrah zata koma Gidan mijinta gobe

Abba yace hakan yayi amma sai dai ina son a basu hakuri su dan barta ta kara samun lafiya sannan babu abunda muka siya na kayan daki, su kara mana lokaci kafin nan inga abunda Allah zaiyi

Hjy fatima tace maganan kayan daki karka damu an wuce wajan, domin mahaifiyar yaron tace basa bukatar komai, dama ni nayi burin siya badan komaj ba sai dan nasan kai bazaka iya siya ba, hjy Binta dani muka yanke gwara ta koma gidan mijinta domin jibi zasu tafi Abuja tare tace acan zata fi samun kulawa sannan tace ba zata taba bari Afrah ta tare ba har sai ta tabbatar ta samu lafiya ina hakan yayi, sannan hakan zai kara bata daman sabawa da mijinta

Mama tace Allah yasa hakan shine alkhairi

Hjy fatima ta amsa da Ameen tare da kallon Abba tace inaso muyi wata magana dani dakai ta kalli mama tare da fadin zaki iya bamu waje kije inda Afrah take

Mama ta amsa da toh tare da tashi ta nufi dakin da Afrah din take dan dama tana da bukatar ganin yar tata, koda mama ta shiga a zaune ta ganta ita da zainab afrah na hawaye Zainab na bata baki akan tayi hakuri

Mama tace Afrah yaushe zaki bar wannan kukan yaushe zaki daina asaram hawayenki yaushe zaki hankali yaushe zaki nutsu yaushe tunaninki zai dawo jikinki? Mai yasa har yanzu kika kasa gane gaskiya mai yasa koda kin dauka magana lokaci kadan kike ajiyewa? Karasawa mama tayi kusa da ita ranta a bace take fadin Afrah aikin gama ya riga daya gama, kuma komai ta fanjama an daura auren kukanki bashi da wani amfani Dan haka gwara kima daina inhar kina jin magana ta kuma kina bukatar Farin ciki na toh ki tabbata kinyi hakuri kin zauna gidan mijinki inki kina son ganin fushi na toh ki bijire ma wannan auren.

In banda shashanci irin naki da sakaci ko ince hauka a gabanki iyayen Yaron da kike hauka a kansa suke nuna miki kiyayya haka ma Yaron ya nuna bai sanki ba. Bari inyi tuni kadan kun san ba'a fadama Afrah David yayi losing memory dinsa ba, mama tana fadin mata haka ne danta cireshi a ranta ta kuma tabbatar da cewa baya sonta yaudarar ta yake sai yasa mama fadin wannan maganan

Afrah kuka take sosai lokaci daya ta tashi tare da nufan mama ta rungumeta tana fadin Dan Allah mama karki fushi dani wlh na hakura da komai kaman yanda nayi miki alkawari zan zauna a dakin mijina duk wuya duk dadi bazan taba baki kunya ba, kiyi hakuri ki daina fushi dani domin kuwa fushinki ba alkhairi bane a rayuwata dan Allah kiyi hakuri mamana

GIDAN KASHE AHUحيث تعيش القصص. اكتشف الآن